MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

“Hajiya ai Abba ne ya bukaci hakan amma nidai bani nace asa rana kadan hakaba”

“To ai babu aibu hakanma,ni dama kullum fatana inga kayi auren nan zaman ka kai daya babu aure baya min dadi yana damuna wallahi…..ga kayan nan bari yaran nan suzo su bude maka kagani”

“Toh hajiya…”

Tashi tayi tafita zuwa kitchen da kanta ta harhado masa abinci ta kawo masa,tuwon accha miyar busasshiyar kubewa sai dafaffen zogale wanda aka kwadantashi da kuli kuli,dafaffen kwai,tumatur, cucumber da sauran kayan lambu,sai bottle water da kunun aya da zobo,

“Hajiya duk wannan abincin ni daya..”

“Ehh ai gara kaci dan yanzu Allah kadai yasan rabonka da abinci Khalil,shiyasa nake murna da zakayi auren nan domin nasan idan kasamu mai nutsuwa zata kula da abincin ka”

Filet din zogalen da ta kwadanta masa yaja gabansa yafara ci,mazauna gidan sai shigowa akeyi ana gaisheshi kamar yadda aka saba duk ranar da yazo,

Sosai yaci zogalen da yawa ya sha zobo kadan domin shi yana son irin wadannan kayan marmarin kamar kwadon yakuwa,kwadon rama, kwadon zogale da sauransu,

Su mufida ne suka zo suka bubbude masa kayan wanda shi bama wani gani yayi sosai ba kawai dai dan kar hajiya tace bai gani bane,yana jin ankira salla yatashi yafita masallaci dama neman hanyar tashi yake domin yagaji da kallon kayan gashi sunki karewa,

Yana fitowa suka hadu da Zaid wanda shima shigowar shi gidan kenan,musabaha sukayi Zaid ya gaisheshi sannan suka shiga masallaci tare,

Lokacin da yakoma ciki bayan yafito daga salla sallama yayiwa hajiya akan zaije asibiti yaduba sirikin Abban London wanda ke can kwance a asibitin kudi baida lafiya kuma ta can zai wuce Abuja, kudi ya ajiye mata mai yawan gaske saboda hidindimun da ba arasa ba musamman ma yanzu da biki yake dososu.

Jama’a cankam a kofar gida yagani lokacin da yafito dama duk ranar da yazo hakace take faruwa shiyasa saida yayi rabon kudi sannan yawuce suka nufi asibitin standard dake nan cikin garin gombe,acan dinma duk da asibitin kudine sai masu hali ke zuwa saida yabi yayi rabon kudi sannan yabar asibitin,shi haka rayuwarsa take Allah bani inbayar ne da yasamu zai rabar,matasa kuwa suna morewa duk ranar da suka samu ganinsa shiyasa a gombe da mai matasa ake kiransa.

K’arfe 1 na dare yashiga gidansa acikin Abuja,gidan shiru kamar koda yaushe,ji yayi cikinsa yana yimasa wani irin ciwo amma haka ya lallaba yayi wanka yasanya farar jallabiya yafita zuwa dakin Aryan,yana kwance ga tulin tady nan akan gadon kamar hauka Kuma manya manya,kwashe tady din yayi ya matsar masa dashi gefe sannan yayi masa addu’a yafita,

Acikin daren yakira Dr Al’amin saboda dagaske cikinsa ciwo yake yi bada wasa ba kuma yakasa gane musabbabin faruwar hakan……….鉁嶏笍

_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:07 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*

  _(Home of expert & perfect writers)_

*D’AND’ANO…..*

*MIJIN MATACCIYA…..*馃挒馃挒

    *_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

*Wattpad-ummishatu*

   *11*

      ***Zuwan Dr Al’amin yasashi fitowa daga cikin bedroom dinshi zuwa falo inda yake zaune yana jiransa,

Fitowarsa ta sa Dr Al’amin mikewa tsaye dan girmamawa,kan daya daga kujerun dake kawace afalon yasamu guda daya ya zauna,

“Dr ciwon ciki ke damuna tun bayan dawowata gida…”

“Ayya Allah yabada lafiya yallabai amma yau me da me kaci?”

“Da safe tea kadai nasha sai dazu da naje gombe shine naci zogale da tuwo dan kadan….”

“To ai ranka yadade ga inda matsalar take nan,dan abubuwan da kaci dinne suka dan ruda maka cikin naka gashi dama bai saba ba”

“Wallahi duk ya takura min gashi bacci nake son inyi”

“Babu damuwa Allah yakara lafiya bari yanzu inbaka magungunan da zaka sha insha Allah zaka samu bacci…”

Lumshe idanuwanshi yayi ya dan kishingida jikin kujerar yana sauraren Dr Al’amin, sai da yagama hada mishi magungunan sannan yatafi,

Cikin bedroom yakoma bayan tafiyar Dr yayi shirin bacci ta hanyar saka gajeren wando na bacci sannan ya dauko robar ruwa guda daya daga cikin bedside fridge dinshi,zama yayi yasha maganin da Dr yabashisannan ya kwanta yana lumshe idanuwanshi cike da bege da kuma tunanin Ramlat, Allah sarki Ramlat Allah dai yasa tana gidan aljannah,shi kam yasan shima har yakoma ga mahaliccinsa bazai iya mantawa da Ramlat ba kullum da tunanin ta yake kwana yake tashi.

***

 Duk da tana cikin damuwa sai dai yau bacin ranta ya ragu da damuwar ta amma fa duk da haka dai sai ahankali yanayin nata,

Karfe 8 nasafe ta kammala shirinta tsaf na komawa Abuja sai kuma satin biki sannan zata dawo,

Dakin Abba taje tayi masa sallama nan yasake dan yimata nasiha sannan yasaka mata albarka ta taso tafito, sallama tayi dasu mamaye yaya shamsu ya rakata tashiga napep zuwa tasha inda zata shiga mota,

Tun tana cikin napep din sukayi waya da mujahid kan cewa zasu hadu a tasha inda zata shiga mota,tana zuwa shima babu jimawa sai gashi ya karaso cikin motarshi,

Karasawa tayi wurinshi ta bude gaban motar ta shiga tana dan harararshi,take away din dake ajiye seat din baya ya dauko ya mika mata saboda dama yasan bata ci abinci ba,

“Good morning my love,gashi kici….”

Dan makale kafada tayi sannan ta kawar da kanta saida ya dan yimata magiya sannan ta yarda ta karba koda ta buda dankali da kwai tagani nan tafara ci mujahid na sake kwantar mata da hankali yana cemata insha Allah akwai matakin da zai dauka yana nan yana shirinsa a boye ita kanta zata sha mamaki, wadannan kalaman nasa ne suka sake sakawa zuciyarta nutsuwa har taci abincin da yakawo mata da yawa dan kadan ta rage yabata ruwa tasha,5k yabata wai tayi kudin mota amma dakyar ta karba daga nan ya rakata mota sukayi sallama dan tuni motarsu ta cika.

Agajiye lis ta isa dan karamin d’akinta dake quarters din malamai,salla kawai tayi ta dafa noodles ta kwanta domin ta huta wanda ba ita ta tashi ba sai la’asar lis wannan dinma wayarsu hajara ce ta tada ita bayan ta dauka suke cemata wai zaman wuri dayane ya ishesu yau suna son su kawo mata ziyara,

Tashi tayi tai wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atamfa sannan ta dora musu abinci kafin su karaso,

Tana shirin sauke sphagettee jalop din da ta dafa mai dauke da kifin gwangwani su hajara suka karaso,sunyi murnar ganin juna sosai saboda rabonsu da haduwa tun ranar clearance na wancan watan dan wannan watanma basu haduba saboda ba rana daya sukayi ba,

Har magriba suna tare amma sam bata sanar dasu cewa za ayi mata aureba. Sha’anin gabanta kawai takeyi dan koda anty salaha ma ta kirata akan maganar gyaran da sauran abubuwan gyara da ake yiwa amarya cewa tayi bata so,anty salaha kuwa tace to ko bata so ita zata yimata inyaso ta zubar,

“Ai kuwa wallahi zan zubar,inma anyi auren kenan” tafada cikin kunkuni,anty salaha na jinta amma dai bata yi magana ba kawai sai ta kashe wayarta,

Agefe guda kuma mujahid naci gaba da bata tabbaccin sai maganar aurenta da minister ta rushe,sai yahana wannan auren indai yana raye to baza ayishi ba sai dai afasa da minister shi ayi dashi wadannan kalaman nasa ne ke sakawa zuciyarta cikakkiyar nutsuwa da farin ciki shiyasa take abinta gaba gadi,kallon kowa take yanda gida suka dauki abin da muhimmanci gashi komai akayi sai yaya shamsu ko anty sun kira sun fada mata dan ko dazu saida anty ta kirata wai za akawo lefenta gobe gasu agida sai aikin nama suke yi amma snacks sun bada kwangila sun biya ayi musu,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button