MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

Baki ta tabe aranta tace sayi sa gama aure dai ba yinsa za ayiba kamar yadda mujahid ya saba sanar da ita kuma wani sharri na Shaidan ayanzu kusan kullum sai sunyi waya da mujahid fiye da sau biyar sabanin da wanda ada idan ya kirata ma ganin nacinsa take yi amma yanzu ko bai kirata ba ita tana kiransa saboda wani sonshi ne kullum ke kara shigarta.

Kamar yadda anty salaha ke sanar da ita ankawo kaya kuma anyi bajinta anyi rawar gani kowa yaga wannan kayan yasan babu karya ankashe masu gidan rana dan har da kudin dinki dubu dari, kuma gashi biki ya matso dan haka yakamata ta dawo gida tazo ayi abinda yadace,

Kuka ta fara yi ta kira mujahid tana fada masa abinda ke faruwa nan yace mata babu komai tayi yanda suka ce din hakan bazai basu matsala ba, hutu taje ta rubuta har na tsawon sati uku domin bikin saura sati daya da kwanaki biyu,

Kamar wacce idan ta tafi ta tafi kenan haka ta harhada kan kayanta tsaf washe gari ta nufi kano.

Bayan ta koma gida aboye suke haduwa da mujahid suna yin hira yana sake kwantar mata da hankali,tun ranar da ta koma kuma anty salaha tafara kawo mata kayan gyara irin na amare amma bata sha sai dai ta faki ido ta zubar,gaba daya gidan shirin biki akeyi ganga ganga bugu da kari ansake gyare gidansu tsaf yasha fenti yasha gyara na musamman.

***

  Duk shirye shiryen da can gida gombe ke faman yi shi kuwa mai gayya mai aiki wato ango yana nan Abuja yana harkokinsa domin ayyuka sun sakoshi gaba bashi can bashi nan kullum cikin yawon ayyuka yake bashi da kwakkwaran lokacin kansa kullum da garin da zaije banda yawon taruka da bude ayyuka da yake halarta,

A gaggauce yake fitowa daga tamfatsetsen dakinshi hannunshi rike da agogon azurfa na Rolex yasha skye blue din shadda mai tsada da kyau,

Yana tafe yana kokarin daura agogon sukayi kicibus da Aryan wanda ke sanye cikin kayan shan iska kasancewar weekend ne babu school,

Rungumeshi ya ida yi sannan ya daga kai yana kallonshi,

“Papa…… Zan bika wurin mommy”

Murmushi yayi ya daga shi sama ya rikeshi yana kissing din face dinshi,

“Good morning my lovely son…., Waye yace maka wurin mommy zanje? Zanje lokoja ne fa,ba gombe zanje ba”

Makale kafada Aryan yayi ya sake rikeshi kamar zaiyi kuka,

“Zan bika Daddy,ni ka kaini wurin mommy,hajiya tace ankusa kawota nan”

Kan dining ya nufa dasu yana murmushi wallahi shi har mantawa yakeyi da wani batun auren nan saboda sam bashine agabansa ba shi sabgogin gabansa ma sun isheshi domin yawa garesu wanda idan har ba mai cikakkiyar lafiya kamarsa ba to mutum bazai iyaba shi dinma da yake da lafiyar ya aka kare stress da zama babu cin abinci kusan koda yaushe cikin kara masa drip ake shiyasa amafi yawan lokuta yafi danganta wannan mukamin nasa da wahala,

Zama yayi saman kujera ya dora Aryan akan glass table din yana kallon shi,

“Aryan kabari inje lokoja indawo zanzo indaukeka muje gombe din but yanzu ka zauna gida kaga anjima kadan lesson teacher dinka zaizo…”

Bata fuska Aryan yayi yasoma murtsuka ido,

Dakyar yasamu ya lallasheshi yakaishi wurin umma barira sannan yafita ta kofar baya.

A lissafinsa ma shi baza ayi bikin nan yana k’asar ba domin zai tafi kasar Spain shida yan wasan kwallon kwando inda za aje akara wasan kuma yana son ya halarta domin yana da muhimmin abinda zai gabatar acan,sai dai yana shakkar sanar da hajiya duk da harka ce ta aiki watakila tayi fada tace dan me zai tafi bayan gashi bikinsa za ayi, addu’ar sa dai Allah yasa kar tayi fadan.

Aranar saida yaje gombe kuma basu tafi da wuriba dan ko lokojan da yaje bai dawo ba sai karfe biyar na yamma,suna zuwa Abuja suka dauki Aryan suka wuce,

Koda sukaje gombe tuni yaga shirye shirye sunyi nisa domin ita hajiya da gaske ta dauki lamarin bada wasa ba shiyasa yayi ta fargabar sanar da ita tafiyar da zaiyi daga karshe dai yaja bakinsa yayi shiru ya zabi yasanar da ita daga baya ta waya,

Sai bayan karfe tara sannan suka baro gombe lokacin tuni Aryan yajima da yin bacci ajikinsa, PA dake gaban mota yayiwa magana,

“Gobe in Allah yakaimu zan aikeka kano,hajiya tace aje akaiwa yarinyar nan kudin menene wai ita da friends dinta….”

“To yallabai Allah yakaimu”

Shiru yayi bai kara cewa komai ba sai tunani fal da yasoma zagaye ilahirin kwanyarsa.

***

 Amarya Hanan kam tana cike da damuwa duk da mujahid kullum na sake bata kwarin gwiwar cewa aurenta ba tabbatacce bane dan haka ta kwantar da hankalinta tajira taga abinda zai faru,

Duk da idan taji yafadi haka takan ji ranta yayi sanyi amma hakan baya hanata shiga damuwa da jin faduwar gaba mai tsanani akoda yaushe,

Yau tunda sassafe taji abba na barwa mamaye sallahun wai ta fada mata zatayi bako,ranta bakikkkirin ta wuni tana jiran taga wannan bakon da zaizo tunda tasan dai bai wuce tsohon banzan nan wato angon.

Wurin misalin karfe 2 na rana nura PA yazo,ranta ahade kamar kullum taje bayan sun gaisa yazaro envelope yabata yana cewa,

“Ranki yadade gashi inji yallabai saboda yan hidindimun da zakuyi keda kawayenki, sannan yace idan kuna bukatar wani abu sai ki sanar dashi”

Karba tayi fuska ahade tace,

“Bama bukatar komai kawai dai kafada masa inada bukatar yaje asibiti yayi gwajin cutar HIV,sai yabada result din akawo min….”

Jin abinda tace yabawa nura PA mamaki amma baice komai ba kuma gaskiya bazai iya fadin wannan sakon nata ba dan yayi masa mutukar nauyi,tayaya zaije yafadawa uban gidansa haka? Dan russunawa yayi sannan yace,

“Ai ina ganin ranki yadade gara dai kawai ki fada masa da kanki ko ta waya ne saboda ni din ba lallai nasamu ganinsa ba”

“Ok to ni zan fada masa”

Daga haka tajuya takoma cikin gida tana kunkuni,kudi ne cikin envelope din da yabata har kimanin dubu dari yan dubu dubu sabbi fil ita tama yi mamakin ta yadda akayi kudin yashiga cikin envelope din,

Aranar anty salaha tasa aka fara yimata gyaran jiki wanda Hanan bawai ason ranta bane amma ko ba komai dai za agyara mata fatarta duk da auren bamai yuyuwa bane. Mujahid ke kaita gidan gyaran jikin sannan ya daukota yadawo da ita gida,tayi tayi dashi akan ya sanar da ita plan dinshi amma yaki kullum sai dai yace mata kawai ta zuba ido zata sha kallo,

K’unshi da saloon ma da kin yi tayi sai da mujahid ya lallabata shine ma yakaita kuma yajira ta har ta gama sannan yadawo da ita gida lokacin bikin yarage saura kwana biyu. 

Kamar yadda nura PA yace mata ta fada da kanta da kan nata kuwa ta fada dan sako ta turawa gogan tana rubutawa tana tsaki aranta tana cewa,

“Ance shekararsa wurin 9 babu mace wai tunda matarsa ta mutu,to waye yasan abinda yake aikatawa tunda da kudinsa gashi a Abuja yake zaune babu dangin iya bare na baba, watakila ma a hotel yake yin gaba daya weekend dinshi,kai may be ma bazai rasa karuwar da ya ajiye ba za ma ta iya yuyuwa baturiya ce”

Ita kadai taketa wadannan maganganun har ta tura masa text din sannan ta ajiye wayar ta tashi tafita tsakar gida inda take jiyo hayaniyar su anty salaha wadanda keta aiki.

***

 Kamar yadda ya shirya sai ana igobe zai tafi k’asar Spain sannan ya sanarwa da hajiya ai kuwa tafara fada tana cewa to kuma auren nasa fa? Taya zasu yarda su bashi aure adaura babu ango? 

“Hajiya “yar abokina ce fa yarinyar,kuma wallahi wannan tafiyar dole sai dani za ayita shiyasa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button