MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

Jin abinda yace yasa hajiya sakin ajiyar zuciya sannan cikin mamaki ta furta,
“Yarku mu’azzam? ‘yarku fa? To ai shikenan”
“Yawwa hajjaju adai yimin addu’a da fatan alkhairin da aka saba”
Addu’a tai tayi masa sannan sukayi sallama,katse wayar yayi yana murmushi acikin ransa kuma yana cewa,
“Ga inda nasarata take, addu’ar hajiya itace take zame min jagora adukkan nasarorin da nake samu cikin rayuwata”
Yana kokarin tashi daga office kuma sakon marar kunyar nan yashigo kamar yadda yake kiranta domin tuni ya rada mata wannan sunan acewarsa bata da kunya ko kadan,dubawa yayi aransa yana cewa yau kuma dame tazo?
_Ina bukatar HIV test result dinka before adaura aure._
Tsaki yaja yamike daga kan kujerarshi yana danna kararrawar dake kan teburinshi alamar yana kiran masinjanshi sannan cikin sanyin murya yana fadin,
“Wannan yarinyar baki da hankali,you are very stupid”
Saida yabar office sannan yatura mata da reply _’Ok’_ shine kadai abinda yatura mata saboda baida lokacinta shi idanma bata saniba to da asuba zai bar k’asar baida lokacin zuwa yayi wani HIV test sai dai kar subashi auren,
Toma wai yarinyar nan me take nufine da sai yayi HIV test? Ko suna tsammanin shi mazinaci ne? Mtswwww tsaki yaja daga nan bai kara bi ta kanta ba har yabar kasar.
Ayau itace ranar da za adaura auren Ibrahim Sulaiman Ibrahim da Sa’adatu mustapha mai jama’a daurin auren da yatara manya manyan yan siyasa da masu rikeda manya manyan mukamai na k’asar Nigeria,
Amarya acike take famm sakamakon wayar mujahid da taketa kira bata samuba duk da kusan kwana sukayi suna waya daren jiya tana ta bashi labarin wulakancin da minister yayi mata wai tace yayi HIV test yaki yayi yace mata kawai ok,ita wallahi bata sonshi ita mujahid take so kuma kowa haushinta yakeji ana cewa ga arziki Allah yakawo mata har gida amma ta runtse ido,arziki na binta tana gudu.
K’arfe 11 na rana ake son adaura auren da tuni ma andaura ana jiran waliyyin ango yakaraso ne wato Alhaji Idris kanwa tsohon gwamnan jihar gombe,dama Abban London tuni yajima da karasowa shida tawagarsa,
Zuwan waliyyin ango yayi daidai da isowar mujahid wanda yacaba ado tamkar shine angon tare da zugar abokansa dake take masa baya……….鉁嶏笍
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*MIJIN MATACCIYA…..*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*
*WATTPAD-UMMISHATU*
_Alhamdulillah wannan shine karshen Dandanon da zan baku (free pages) duk mai bukatar karanta cigaban labarin sai yaturo da 200 ta account din 3112877210 Aisha Ibrahim first bank,sai atura shaidar biya ta wannan number 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta wannan number din,dan neman karin bayani sai a tuntubi marubuciyar kai tsaye ta wannan number din 07044644433._
*13*
***Kwana tayi tana kuka sam bacci baiga idonta ba, abubuwa biyu ke sakata kuka abinda mujahid yayi mata da kuma abinda minister yafada mata dagaske dai raino zataje tayi masa na yaro,kaico,kaiconta inama iyayenta sun san manufar wannan auren nata,inama sun san abinda ke lullube da wallahi tasan ko za ayi kuli kulin kubra dasu bazasu yarda ayi wannan aurenba amma da yake wasu mutanen Allah yahore musu baiwar iya tsara mugunta da cuta shine aka rufi kura da fatar akuya aka yiwa iyayenta ungulu da kan zabo su sunata murna yarsu ta auri babban mutum basu san nan kuwa a matsayin yar raino ta fito ba,ai kuwa minister zaisha mamaki domin zata saka kafafunta duka biyu tayi kolin kolin fatali da wadannan sharrud’an nasa inyaso idan yaji haushi ya korata gida.
Da bacin rai da bakin ciki ta wayi gari wanda ko diss bata samu bacci ba,wanka tayi bayan tayi salla wanda su anty salaha ne suka tilastata bayan sun shigo cikin dakin,humrah masu sanyin kamshi da jan hankali suka shasshafa mata sannan tasaka kaya wadanda suma suka sha turare na daukar hankali,
Doguwar riga zuwa gwiwa tasaka da zaninta duka na atamfa orange and blue colour bayan sun gama shiryata tasaka su sarka da dan kunne akayi knocking a kofa aka shigo yanmata ne guda uku wato mufida da Sarah da Zarah kowaccensu dauke da madaidaitan warmers masu kyau iri daya,kasa kasa take kallon yanmatan wadanda daga gani kasan jin dadi da hutu sun jima da samun muhallin zama a jukkunansu,
Kayan breakfast ne suka kawo musu sannan suka gaggaishesu sai kallonta suke suna dan magana kasa kasa shiyasa taji duk sun isheta domin ta tsani kallo,kamar sun san abinda ke cikin ranta suka tashi suka fita.
Abincin karyawa ne na gani a na fada domin farfesun koda ne da soyayyar agada sai wainar kwai fal sannan ga wainar shinkafa itama da zuma ga kuma kayan tea da ruwan zafi agefe abinci dai kaca kaca gashi nan sai wanda ka zaba ita kam ruwan tea din kadai ta iya sha sai da anty salaha suka bude mata wuta sannan tasamu ta danci farfesun kuma suka tilasta mata saida tasha romon tass,sake gyara mata jikinta sukayi suka nada mata lafaya suka fita zuwa dakin hajiya Zaitun,
Ita ma taci ado Sosai cikin wani leshi, kama Hanan tayi ta rungume tana dan shafa bayanta ahankali take yimata magana,
“Barka da zuwa cikinmu Sa’adatu,lale marhabun dake,kinyi dace da miji mai biyayya ga iyayensa bawai dan nina haifeshi ba a’a sai dan kawai halinsa ne,ko kai ka haifi mutum halinsa shi zaka fada,ki zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya duk abinda yayi miki wanda ba daidai ba ki sanar dani,tsawon shekaru kusan bakwai kenan rabonshi da mace tunda matarsa ta mutu wurin haihuwar yaronsa shikenan bai kara aure ba nayi nayi amma baiyi ba sai yanzu bagatatan yazo min da maganar ki kuma gashi da yake Allah ya kulla anyi, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka…..” Wadannan sune kalaman mahaifiyar sa wanda harda kwalla take yi lokacin da take fada mata domin duk da fuskarta arufe take amma tana fuskantar komai kuma tana jin lokacin da matar Yakumbo ke cewa,
“Haba hajiya kema kukan zakiyi Khalil din da ba shine auta ba…….”
Sun dan jima awurin hajiya sannan akace sufita domin tafiya Abuja,kamar jiya yauma zaid ke jan motar da take ciki tun daga garin gombe har Abuja wanda tafiyar awanni kadance ta kaisu,tana jin anyi parking gabanta ya tsinke ya fadi,
Da addu’a abakinta ta taka tashiga da k’afar dama wadda iyaye keta nanata mata wadanda ke tare da ita, Masha Allah, Masha Allah,shine abinda kunnuwanta keta jiye mata lokacin da suka shiga gidan gashi babu laifi tafiya taki karewa abisa dukkan alamu gidan da zurfi dan harda su hawa bene taji anyi daga bisani aka danyi yar tafiya taji anbude wani daki sun shiga wanda sanyi da kamshi ya cikashi kai gaba daya cikin gidanma sanyi da kamshi ne acikinsa dan tunda suka shigo taji yana shigarta,abakin wani luntsumemen gado taji an zaunar da ita kan wata hadaddiyar katifa mai sifrin tamkar kahau irin gadon nan na da irin na karfen nan wanda zakaji yana tsalle dakai,
Har lokacin bata bude fuskarta ba tana jin lokacin da su anty badi’a suka shigo anty badi’a tazo kusa da ita ta zauna cikin rada take cemata,