MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

“Wallahi yarinya kin more da gida, aljannar duniya,kinga gidanki kuwa Hanan? Wallahi girman wajen nan ya isa mata hudu su zauna basu takura ba, Allah yasa rabonki ne yasa gidan zamanki ne har abada, Allah yasa mutuwa ce kadai zata raba….. Ai tun dazu muna kasa muna ta santin wannan aljannar duniyar, Masha Allah wallahi gidanki ko a London iyakaci kenan sannan gaki ga Villa….”
Ai Hanan ji tayi kamar ta dora hannu aka saboda takaicin wadannan addu’o’in na anty badi’a danme zata rinka yimata addu’ar kare rayuwarta a wannan gidan da yafi kurkuku tsanani agareta babu kunya bare tsoron Allah aranta ta rinka cewa, “Ba amin ba”
Tana tukunkune atakure har saida dakin yarage daga ita sai su anty salaha sannan ta bude fuskarta,tamkar amafarki tajita lokacin da tayi ido hudu da dakin da ake kira da mallakinta bata san lokacin da ta furta,
“Masha Allah”
Ba kadan ba taga dakin yayi bala’in haduwa gashi tangamemen gaske duk kayan ciki dark purple ne masu dan sirki sirkin haske ko ina sai sheki yake magana ta gaskiya bata taba cin karo da furnitures makamantan wadannan ba wurin kyau da haduwa, sunkuyar da kanta tayi saboda bata son su gane dakin take kallo tabari har sai sun tafi sai ta bude idonta ta kashe kwarkwatar idonta dakyau gida kamar akasar turai?.
Saida suka ci abinci sukayi sallar azahar sannan yan kawo amarya aka fara haramar tafiya nanfa Hanan tace bata san zance ba domin zama tayi ta rinka rusar kuka ahaka suka tafi suka barta, kwanciya tayi saman gadonta tana cigaba da kukanta cike da kunar rai har tayi tagaji tunda babu mai rarrashinta dan abisa dukkan alamu ma ita kadai ce agidan sai ko ma’aikata domin bata ji motsin ko kare ba duk da cewa ma gidan yana da girma da fadi ko da ace akwai wani ciki ba lallai kasani ba indai bawai yashigo side din da kake bane,ita kam ko tantama batayi tasan ita kadaice cikin wannan katon gidan domin dazu lokacin da suna kan hanya tana ji zaid yana waya da wani wanda bata san ko wanene ba yana cewa wai su umma barira da Aryan na tsohon gida ita amarya yanzu sabon gida za akaita amma suma su umma barira din nanda anjima ko gobe za akawo su sabon gida basu karasa parking din kayan su bane. Saida tayi kukanta ta gaji dan kanta sannan ta tashi da niyyar yin alwala domin la’asar ta kusa zaman dirshan tayi tana bin d’akinta da kallo wanda ya amsa sunan aljannar duniya, mai karatu Hanan bata san ta inda yadace tafara kwatanta muku haduwar da d’akin baccinta yayi ba domin komai yajine ba karya komai yadace da muhallin da aka ajiyeshi tun daga kan labulayenta gadonta wardrobe dinta,da komai dake cikin dakin sannan daga can dan gaba kadan da gadonta wasu hadaddun kujeru ne guda uku suma dark purple an dan yi circle dasu an ajiye glass table a center sai wurin yabada ma’ana tamkar dai aturai sannan ga wurin sallarta nan an tanada ga katuwar tv ta bango da dan karamin fridge kawai dai komai yaji ne fa,sauka tayi ahankali da niyyar zuwa toilet nan ta tsaya yin wani kallon domin shi kansa bathroom din nata da glasses aka zagaye shi marassa duhu sai dai ba lallai ne ka iya hango mutum ba idan yana ciki amma ta yuyu zaka iya ganoshi tsaff,kamar mai shirin daukar kwai haka takama kofar bathroom din ta tura ahankali tashiga,bandaki kamar wani filin shakatawa? Ta fadi hakan aranta domin shima an kawatashi an shiryashi sannan anzuba daula acikinsa kamar ba wurin wanka da fitsari ba,irin haduwar da bathroom dinnan yayi fadarshi bata bakine yahadu fiye da duk yanda zaka kissimashi cikin ranka,ita dai gidansu ba hamshakan masu kudi bane shiyasa sai da tabi komai asannu gudun kada tayi barna domin wasu abubuwan ma yaune tafara ganinsu haka dai ta lallaba tayi alwalar tafito tazo ta bude wardrobe ta ciro hijabi daga cikin jakunkunanta wanda su anty salaha suka saka mata cikin wardrobe dinta dazu.
Rasa wacce irin addu’ar da zatayi tayi saboda ita dai bata son zaman gidan nan ko kadan bare tayi addu’ar Allah ya tabbatar da ita agidan,daga karshe dai sai kawai ta roki Allah da ya zaba mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta,
Saman gado taje ta hau ta kwanta domin bata san abinda zatayi ba ayanzu juyi kawai tashiga yi tana ta tunanin rayuwa wai yau itace acikin wannan gidan wanda ko acikin mafarkin ta bata taba mafarko gida makamancinsa ba a tarihin rayuwarta,duk da gidan ya cancanci akirashi da aljannar duniya ita kam bata yiwa kanta fatan tabbata acikinsa, nasihar Abban ta ce ta fado mata inda yake cewa,
“Hanan ki yiwa mijinki biyayya kibishi sau da k’afa ban yadda kiyi ko musu dashi ba sannan ban amince miki kiyi koda yaji ba bare ki nemi saki a hannunshi,kada naji kuma kada nagani,duk ranar da kika zo gidan nan da sunan yaji to ba zamu kwashe dakyau ba,mijinki shine aljannarki domin tana karkashin kafarsa ne dan haka kiyi masa biyayya iya iyawarki daidai gwargwadon yanda zaki iya….. Allah yayi miki albarka”
Wasu tagwayen hawaye ne suka zubo mata sakamakon tuno wannan nasihar ta abbanta da tayi,to wai ita yanzu ta ina yadace tafara ne? Wanne irin zama zatayi a wannan gida? Wanne irin zama zatayi da abokin mahaifinta? Wacce irin rayuwa zatayi da dansa da sauran jama’ar da ke rayuwa cikin wannan gida? Menene makomar rayuwarta? Wadanne irin kalubale ke jiran rayuwarta saboda auren babban mutum da tayi shin zai dauke mata dukkanin bukatunta ko kuwa zai yi watsi da lammuranta? Wadannan tambayoyin sune keta circulating acikin kwakwalwarta wanda ta gagara bawa kanta amsa…………………鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:07 AM – Ummi Tandama: 漏锔? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
_(Home of expert & perfect writers)_
*D’AND’ANO……*
*MIJIN MATACCIYA…..*馃挒馃挒
*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*
*WATTPAD-UMMISHATU*
*12*
***Wata zazzakar guda ta jiyo babu k’akk’autawa wata mata wacce Allah yabaiwa baiwar hanci ta dage sai rangada ta take yi kamar anyi mata bishara da kujerar hajji ko ta umarah kafin daga bisani tafara jiyo maroka suna faman yin kirari,tsam ta dakata daga kokarin saka sarkar da take yi awuyanta,
“Ayyiriyiriyiriiiiiiiiiiiii……. Aure ya kullu,amarya Sa’adatu rai yakaiki….. Allah yasa gidan zamanki ne….. Ayyiririiiiiiiii” Matar da keta faman rangada guda agufi agufi tafada tana sake bude makogaro wurin rero wata gudar, sake saurarawa tayi dakyau har tana mika kunne domin jiyo abinda marokan nan ke fadi,
” _Sa’adatu sa’ar mata, Sa’adatu mai sa’a babu shakka kin tako sa’a da auren baya goya marayu dan mulki kuma jinin sarauta, yagaji arziki da sarauta dan na gada ba dan na koya ba, wato Alhaji Ibrahim Khalil ga kudi ga mulki… Ina amarya Sa’adatu,kifito kibani kyautar mota da kujerar hajji amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida…._”
Ai bata iya karasa jin karshen kirarin da marokan nan ke zuba mata ba jikinta yahau rawa wanda har kyakkyawar sarkar hannunta na neman sulmiyewa,anty badi’a yar gidan yayar mamaye itace tayi gaggawar riketa sannan ta rike sarkar tasoma kokarin saka mata,
Ita anty badi’a duk azatonta rudewar Hanan akan an daura auren ne bata san ita jin sunan wanda aka daura auren dashine ya rudata ba saboda taji ana ambaton wani daban sabanin mujahid. Hawaye ne suka shiga wanke mata fuska babu k’akk’autawa kamar anballe bakin fanfo,