MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

Ai wani sanyi Hanan taji jin zasu fita su barta ita kadai,

“To ba matsala muje,amarya ga wayarki may be zaku dan taba hirar dare da ango kar mu tauye muku hakki….” Anty badi’a ce tayi wannan maganar sannan ta fito mata da wayarta ta mika mata,sake tukunkune fuska tayi saboda bata son anty saudat dake tsaye bakin kofa taganta.

Tattarawa sukayi gaba daya suka fita suka barta nan ta duba wayarta jikinta har wani tsuma yake saboda yanda take hanzarin taba wayar,miss called sama da guda 15 tagani sai massages guda biyar bata bi ta kan massages din da miss called din ba tafara kiran layin mujahid amma duka akashe,ji tayi kamar ta fashe da kuka amma babu hali sakamakon wani dunkulen abu mai kamada curin karago da yazo ya tsaya mata a kirji ya tokare mata makoshi,

Miss calls din tabi ta duba kusan fin rabi kiransa ne sai na sauran abokan arziki wanda bata tsaya bi ta kansu ba, massages takoma dubawa nan taga sakon bank guda daya anturo mata alawee sai sakon minister shima guda daya sauran kuwa duk sakon mujahid ne,

Na mujahid din tabi tafara karantawa daya bayan daya gaba daya jikinta sai yayi mata sanyi tamkar bata da sauran laka ajikinta wai ashe duk abubuwan da mujahid yajima yana fada mata gaba daya zirata yayi akwali yarufe wai dama wallahi baida niyyar yin wani abu dan yahana aurenta da minister kawai yayi hakane dan ya kwantar mata da hankali amma kamar yadda yafada mata abaya shi mai taimaka mata ne dari bisa dari tayiwa iyayenta biyayya bazai taba goyon bayanta wurin bujirewa umarnin iyayenta ba saboda soyayyar gaskiya yake yimata kuma har gobe yana sonta,ayau dashi aka daura auren ta domin ya halarta kuma yayi musu addu’a ita da mijinta Allah yabasu zaman lafiya dan Allah tayiwa mijinta biyayya fiyeda yadda taso yiwa shi mujahid din sannan ta sani ko gobe aurenta ya mutu wanda baya yimata fatan haka ashirye yake da ya aureta yakaita gidansa domin yana sonta har gaban abada,

Wadannan kalaman nasa sune suka kashe mata duk wata kafar laka dake jikinta sannan kuma suka tsayar da tunaninta cak na dan wani lokaci tabbas abunda mujahid yayi abune da yadace ta yaba masa kuma taji dadi amma kasancewar akwai Shaidan sai taji samm hakan bai burgeta ba ita wani haushi ne ma ya turnuketa dan me mujahid zai yaudare ta yamayar da ita karamar yarinya wacce bata san ciwon kanta ba? Wallahi da tun farko tasan wannan tuggun yake hada mata da tuni ta samarwa kanta mafita amma dan mugunta bai sanar da itaba sai a kurarren lokaci, lokacin da bata da matakin dauka,

Sakon minister ta bude tana jin kwalla na ciko mata ido wanda sai lokacin hawayen suka samu zarafin fitowa,

_Kamar yadda na fada miki zan kafa miki dokoki akan yarona,nafarko ba a dukan min yaro,ba a zaginsa,ba a yimasa tsawa sannan duk abinda yake so abashi,kuma ki sani ko harararshi kikayi zai sanar dani._

Ganin abinda yaturo mata yasata wurgi da wayar can karshen gado amma dai Allah yaso bata kai ga faduwa kasa ba,fashewa tayi da kuka aranta tana cewa wannan shine inuwa zafi rana kuma k’una……..鉁嶏笍

_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:07 AM – Ummi Tandama: *Littafin mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

  *14*

        ***Tun bayan tafiyarshi k’asar Spain ya tsinci kanshi cikin yanayi na rashin lokaci duk da a bangare daya yayi tafiyar ne dan ya kebance kanshi wuri daya kwakwalwarshi da gangar jikinsa su samu hutu koda babu yawa amma baiyi katari da samun hakanba har sai bayan yan wasu kwanaki da zuwanshi k’asar.

Ranar da aka daura aurensu da Hanan Khalid ne yafara yimasa albishir ta hanyar turo masa da sakon karta kwana ta wayarshi,

Lokacin yana kwance adaki mai lamba 9 cikin babban hotel din da ya sauka wato luxury 5 Stars hotel wanda ke cikin tsakiyar birnin na spain wato birnin Madrid,yana ganin sakon sai yaji hankalinsa ya dugunzuma mutuwar Ramlat ta dawo masa sabuwa kamar yanzu ne akayi ta,

Samun kansa yayi da zubar da hawaye kamar wani karamin yaro kankani,mutuwa mai yankan kauna,mutuwa yanke buri,bai taba kawowa Ramlat mutuwa ba a lokacin da ta mutu amma wai sai mutuwar kawai yaji,a wannan lokacin saida rayuwar da suka gabatar tare ta dawo masa tun daga ranar da yafara ganinta har izuwa ranar da aka daura musu aure da irin tsaftacacciyar rayuwar da sukayi tare har izuwa samun juna biyunta da kuma mutuwarta duk saida suka dawo cikin kwakwalwarshi a wannan lokacin,wai yau gashi shine aka sake daura masa aure da wata saboda rashin Ramlat da ace Allah yabarshi da Ramlat dinsa ai shida kara aure har abada saboda ita kadai ta isheshi rayuwar duniya dai wadda ba matabbaciya ba. A zamansu da Ramlat yasha fada mata cewa bazaiyi mata kishiya ba ita kadai ta isheshi a lokacin sai tayi murmushi tace wannan fa tatsoniya ce kawai yake yimata ba komai ba,idan kuma Khalid na nan sai yarinka tsokanarta yana cewa ai karya Khalil din yake yi bayan shi yake ma rakashi zance ta shirya kwana kwanannan zasu kawo mata amarya,

A takaice dai ranar wuni yayi acikin daki wani lokacin yayi kuka wani lokacin kuma yayi murmushi tamkar wanda ya zauce ko yasamu tabi,amma ta wani bangaren yana jin sanyi acikin ransa idan yatuna da ya cikawa Aryan burinsa dan irin farin cikin da zaiyi sai Allah. Bai samu fita ba sai bayan da yayi sallar magriba bayan yayi wanka, kananan kaya yasaka jeans da t shirt dukkansu bakake sannan ya dora jar jacket asama bayan yasa bakin takalmi sau ciki,amafi yawan lokuta irin wannan shigar yake yi aduk lokacin da yabar gida Nigeria, kananan kaya yake sakawa sai yakoma Nigeria ne yake saka manyan kaya kuma shima bai fiya amfani da babbar riga ba a’a sai dai doguwar riga da wando da hula su yafi ta’ammali dasu,

Wayarshi ya dauka yafita bayan yasaka hular dake jikin jacket dinshi yarufe kansa,saida yabar harabar hotel din domin dan mike kafarsa sannan yakira Aryan yasan dai lokacin ba afi la’asar ba a Nigeria tunda akwai dan banbancin lokaci,

Zama yayi kan wani bridge sannan ya kalli screen din wayar domin video call yakira,ganin Aryan yayi da hijabin umma barira ajikinsa yana kan cinyarta dare dare,

“Papa Uncle…… Daddy”

“Aryan,shine ka haye min kan cinyar gyatuma saika karasa mata kafafun ko? Oya tashi maza dagata”

Kafada ya makale yana dariya,

“No Papa…..uhm uhm”

“Bar ja’iri dai ai sai na kaishi an aske masa wannan sumar tashi dake kansa” umma barira ta fada cikin tsokanar Aryan ai kuwa sai yafara kuka yana cewa baza ayi masa aski ba dan tunda aka haifeshi ba ataba yimasa aski ba tun bayan na suna har yau dinnan sai dai ataje sumar wani lokacin kuma akaishi saloon a dan gyara masa ita shikenan saboda shi kansa baban shima ba askin yake yiba sai dai gyaran fuska amma shima kansa haka yake,

“To ya isa kyale umma babu mai yiwa abbana aski….. Daina kuka”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button