MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 11 to 20

“Papa momy tazo ko? Zamuje wurinta nida umma balila”

Dariya umma barira tayi ta d’aukeshi cancak ta dora saman kujera tawuce gaban gado ta zauna tana cewa, 

“Daina bata min suna dan nema..”

“Momy tazo tana sabon gida,are you happy?”

“Yes Daddy,ka siyo mata kaya mai kyau”

Kamar yadda ya tsammata sai da yagaji da surutun Aryan dan har saida yaji yamanta damuwar da ya wuni acikinta, Aryan na debe masa kewa Sosai aduk ranar da yasamu kansa cikin damuwa da zarar ya kasance da yaron sai yaji hankalinsa ya kwanta ko dan irin son da yake yiwa yaronne oho.

***

 Zaman kadaici,shiru da rashin sanin abinyi takamaimai shine ya taru ya dabaibaye Hanan wacce ke kwance cikin daki lamo ita kadai batare da abokin hira ba har magriba tayi tana kwance saman gado bata ma san magribar tayi ba saida ta kunna wayarta wacce ke kashe da niyyar kiran yaya shamsu taji ko Allah yasa sun isa gida sai lokacin taga ashe har lokacin salla yayi,yaya shamsu takira bugu uku ya dauka,

“Yaya shamsu kun karasa gida ne?”

“Ehh”

Shine kadai abinda yafada yakashe wayarshi saboda baya son tayi masa kuka yasan yanzun nan zata fara koke koken nata,

Itama tasan dalilin da yasa yakatse wayar kenan duk da haka saida taji hawaye sun zubo mata tamkar ruwan zafi saboda duminsu,kiran mujahid tayi amma har lokacin wayarshi akashe take,lallabawa tayi ta tashi tashiga bathroom tayi alwala tafito tayi salla nan ta zauna awurin bata tashiba har lokacin sallar ishah yayi,mikewa tayi ta gabatar da sallarta sannan ta tashi takoma saman gado,gaba daya tagaji da kwanciyar ma amma kuma babu yanda zatayi babu yanda ta iya,sake tashi tayi ta canja kayan jikinta izuwa na bacci riga da wando lainon c green rigar mai botira ce da gajeren hannu shi kuma wandon dogo ne, kwanciya tayi duk ranta tsoro fall amma tasan insha Allah babu abinda zai sameta saboda katon gida irin wannan akwai security duk da dai Allah ne mai karewa ita abinma mamaki yake bata wai itace daren farkonta ya kasance ahaka,lallai Allah shine mai tsara rayuwa amma ko amafarki bata taba tunanin wai daren farkonta zaizo ta wannan sigar ba. Tajima tana juye juye amma kasancewar akwai ramukon bacci da yawa akanta bata san lokacin da bacci ya dauketa ba wato shiyasa bacci yakeda dadi domin akwai wani sirri acikinsa duk damuwarka ko ciwo ko bacin rai kana mantasu a lokacin da kayi bacci baka tuna komai har sai ka farka,

Hakance tafaru gareta itama domin tunda tayi bacci tasamu nutsuwa tayi baccinta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali wanda ba ita ta tashi ba sai bayan asuba wannan dinma tasowar hadirine yatasheta saboda iska,salati tayi tai maza tashiga bandaki tayi alwala tafito lokacin tuni anfara ruwa misalin karfe 6 da kwata na safe,

Sai bayan da tayi salla sannan tashiga wanka tafito,make up kit dinta ta bude ta dan shafa lotion tasaka powder sai kwalli shikenan ta saka kayanta shadda brown colour da sarka da dan kunne ta dan fesa turare sama sama sannan ta bude kofa tafita domin wata lafiyayyar yunwa take ji duk hanjin cikinta sun sarke da juna,tamkar sakaliya yau haka ta zama sakamakon ganin haduwar da falonta yayi yasha purple colour din furnitures hatta wallpaper din dake bangon falon purple colour ne amma mai dan haske sannan ga wata tangamemiyar plasma ajiye wacce ke barazanar cinye bangon da take,agaskiya gidan yayi kyau ya hadu kuma ya tsaru sannan ankashe miliyoyin kudi wurin shiryashi, ita kanta cikin falon nata wurin bedrooms hudu ne aciki banda kitchen da store da dining area haka dayan part dinma dake opposite da nata,daga tsakiya kuma akwai wani dan corridor mai dauke da wasu hadaddun kujeru kai daga ganin wurin kasan anyi ne domin shakatawa dan ga flowers nan masu kamshi shuke agefe cikin tukwanen kasa wacce aka yiwa fenti da golden gashi yadda aka you roofing din wurin dabanbanci da sauran domin wannan anyishi ne da wani style mai ban sha’awa sosai ya burgeta dan daga nan inda kake ma kana iya hango cikin unguwar ta glasses din dake zagaye da wurin kana iya hango kyau da tsari irin na unguwar wacce ke dauke da manya manyan gidaje kerarru ga korayen ciyayi da shuke shuke da suka yiwa unguwar kawanya, gaba kadan kuma wata kyakkyawar kofa ce katuwa mai dauke da security code ajiki amma ita arufe take balle taga abinda ke ciki dan haka tajuya ta nufo kasa, babban falon dake kasa shima yana dauke da kitchen da store da dining room sannan ga guest room, atakaice dai gidan yakai part 4 waje waje ko ina kuma a tsare wani wurinma bata san dashi ba. Babu kowa cikin falon sai sanyi da kamshi dake ta faman tashi ta ko ina, kan dining ta duba abinci ne reras cikin warmers mai kyau kala kala wanda ita abinma har yaso bata tsoro to ina za akai wannan abincin sai kace wanda mutane goma zasu ci bayan bata ji motsin kowa ba? Lallai masu kudi suna shagalinsu a duniyar nan ta Allah,

Zama tayi ta debi dankali da kwai sai farfesun kayan cikin saniya dan su kadai zata iya ci,tana ci tana sake karewa falon kallo wanda yake kamar baza amutu ba dan tsabar haduwa tab irin wannan gidan idan mutum ba mai cikakken imani bane ai sai yamanta da mutuwa domin zai shagaltar dashi shi kansa dining area din abun kallo ne kujerunshi na karfe ne milk colour sai wani show glass mai fadi da girma glass da glass anzuba kwanukan cin abinci duk na tangaran plates, spoons, cups da sauran kayan amfani irinsu dinner set. Bayan tagama ci ta mike ta dauraye hannunta da bakinta awurin wanke hannu wanda aka tanada a dining area din dan hadda sabulun wanke hannu ajiye awurin nan ta matsa ruwa yafito ta wanke hannunta sannan ta leka cikin kitchen din wanda ke tafare da kayan amfani na wuta dan gaba daya electric ne kayan ciki gashi kuma babba dashi ba karami ba kayan ciki kuwa yaci ayiwa yanmata biyar aure dashi cikin wadata kuma,mayar da kofar tayi ta rufe takoma sama tana mai sake jinjina wannan gida acikin ranta,da ace wanda ta aura take so ko yaro ba tsoho ba ai zata fantama ta wataya to amma ina k’addara tariga fata.

Rasa abinda zatayi tai daga karshe tasaka wayarta a charge tabi lafiyar kujera ta hakimce tana sake bin falon nata da kallo to kenan ma har kayan dakin shi minister dinne yayi amma dai zata iya yuyuwa shima abbanta yayi mata,to aure ne babu shiri dududu ko wata daya fa ba ayiba da maganar akayi aure shiyasa komai babu shiri,

Dan sakin ranta tayi sakamakon kiranta da mutane keta faman yi awaya suna yimata Allah yasanya alkhairi wasu kuma suna yimata korafin kin sanar dasu bikin nata da batai ba ita dai bata cewa komai sai dai tayi shiru ko ance Allah yabada zaman lafiya bata cewa amin, su Khadija kuwa wadanda sukayi zaman camp tare sunce insha Allah zata gansu tunda dai tana Abuja.

Wuni guda ta kwashe tana shan baccinta salla kawai ke tada ita,bayan tayi sallar la’asar ta yi wanka ta sake shiryawa cikin atamfa exclusive irin na cikin lefenta,dinkin riga da zani ne pieces simple daurin dan kwali tayi sannan ta shafa turare,tun safe rabonta da abinci shiyasa ta nufi downstairs domin cin abinci ai kuwa gashi nan jere an ajiye wurin kala biyar,shinkafa fara da plantain sauce,sai amala da miyar yauki,ga gasasshen kifi wanda yaji vegetables washa washa ga jalop cous cous,sai farfesun kaza da wasu ganyayyaki wadanda bata gane Wadanne bane,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button