MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:08 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*23*

    ***Juyi tayi ta dauki karamin pillow guda daya ta rungume acikin zuciyarta tana hango kyakkyawar fuskarshi, murmushi ta saki ita kadai kamar wata tababbiya saboda tuno rashin son hayaniyar shi da tayi ga masifar jan ajin tsiya kamar wata mace wanda hakan ba karamin kyau da kwarji yake kara masa ba,wai meke shirin faruwa da itane?  Ta tambayi kanta bayan ta tashi zaune,

“He’s cute…..” Tafada ahankali bayan ta koma ta kwanta tasake rungume pillow,

“Ban taba ganin namiji dan gayu handsome kamar shi ba”  ta sake fada afili tana sakin murmushi,gaskiya Khalil yahadu yahadu irin haduwar da tafi gaban kwatance domin sai wanda idanuwansa yagane masa kawai,juye juye tayita faman yi takasa bacci sai Khalil da take ta faman gani a idon zuci dakyar tasamu bacci ya lallabo ya saceta.

Shima Khalil anasa b’angaren bayan yagama nafilfilinsa lokacin da ya kwanta kasa bacci yayi kawai tunanin abinda yesmin tayi masa yake yi wato ta zabi ta kashe masa d’ansa saboda bata samu abinda take so ba daga gareshi,ita sabon Allah take son ya yarda suyi ta yi shikuma hakanne bazai taba iya aikatawa ba,sau da dama tana zuwa office dinsa amma baya saurararta,gashi dai babbar mace ce amma kuma sam bata da nutsuwa dan babu halin mata na kirki atare da ita gashi abanza tana neman illata masa yaro wallahi ba dan Abban Hanan yabashi baki yace yarabu da itaba da sai sunyi shari’a da ita,bacin rai bai barshi ya runtsa ba sai tsakiyar dare.

  Washe gari Hanan da farin ciki ta tashi cikin nishadi tayi wankanta ta shirya cikin riga da skirt na English wears sannan ta saka dan madaidaicin pink din hijabi ta fita lokacin umma na kwance adakin Aryan dama tare suke kwana sai da Hanan ta shiga sannan umma tafita,daga Aryan Hanan tayi wanda zata yiwa brush nan taga abunda yayi masifar tsorata ta har ta nufi kofa da gudu dan kiran umma ko hajiya amma tana bude kofar sukayi gware da Khalil wanda ke kokarin shigowa cikin dakin ganinta da yayi kamar a razane yasashi riketa kamar yanda ta rikeshi,

“Menene…?” Itace tambayar da yayi mata,cikin razani ta nuna masa Aryan jikinta na rawa,

“Wani abune a karkashin Aryan”

Sakinta yayi ya nufi Aryan, shima saida abin yaso tsoratashi domin wata sab’a ce daga jikin Aryan din tafita doguwa sambel kamar muciji bakikkkirin da ita,karasa cire masa sabar yayi yafita aransa yana tunanin wato duk wanda yayiwa Aryan wannan abun da niyyar kasheshi watakila yayi kuma sai Allah bai lamunce masa ba,

Ita kam duk tsoro ya isheta sai sannu take yiwa Aryan,bayan tagama yimasa brush ta zubo masa kindirmo cikin cup ta hada masa da maganin da Abba yace ta rinka hadawa da nono tana bashi da sassafe kafin yaci komai saida ya shanye sannan tafita ta nufi kan dining domin hadawa su Abba breakfast tana tafe tana murmushi sakamakon tuno abinda yafaru dazu da tayi, rikon da mutumin nan yayi mata ya tsaya mata arai,hannunsa masu masifar taushi da laushi kamar auduga. Ita kadai take ta sakin murmushi har tasamu ta gama jera musu breakfast din saman babban faranti,

Sama ta hau ta nufi sashen Khalil,kamar jiya suna zaune shida Abba sai hira suke sha fuskokinsu dauke da fara’a,

Tsugunnawa tayi ta fara gaida Abba sannan ta gaishe da Khalil wanda hankalinsa ke kan wayarshi yana turawa secretary dinshi na office sako,

Dan shiru tayi tana sauraren tattaunawarsu da Abba wadda bata shafeta ba su ta shafa domin bata ma gane kan zancen nasu ba, da gefen ido take satar kallon Khalil wanda ke sanye cikin farin yadi mai laushi wato tissue amma kai daga gani kasan naira tayi kuka domin yanayin yadin ma daban yake,

“Uwata tashi maza kema kije ki karya sai ki dawo muyi sallama saboda tafiya zanyi…”

Idanuwanta narai narai ta mike tafita daga khalil har Abba binta sukayi da kallo bakar body hug ce ajikinta sai purple din skirt wacce ta baje daga kasa,

Tana fita wurinsu umma ta wuce wadanda ke dakin Aryan can takai musu kayan karyawar suka ci domin hajiya ita ba ruwanta duk da cewa tana dan kunyar Hanan din,

Suna zaune su umma nata hira ita kuma ta na shirya Aryan wanda tayiwa wanka kuma dayake yau jikin nasa da sauki da kansa ya taka har zuwa cikin bathroom,

Wayar landline dake ajiye gefen gadon Aryan ce tafara rurin neman agaji, Hanan ce ta dauka tana mamakin to ko waye kuma, shiru tayi batace komai ba caan taji muryar Khalil,

“Zo abbanki na kiranki…..”

“Tohm ina zuwa..”

Baice komai ba yakatse wayar, hanzartawa tayi ta karasa shirya Aryan sannan ta fita,

Zaune ta samesu shida abbanta saman kujera suna yin magana amma zuwanta yasa suka bar maganar abba ya fuskanceta yana murmushi,

“Uwata ni zanje inkoma sai ayita hakuri da rayuwa kinji…., Ayita hakuri da duk halin da aka samu kai domin rayuwar gaba dayanta hakuri ce kuma kici gaba da yiwa mijinki biyayya banda sabawa umarninsa,kamar yanda na fada miki abaya ban yarda ki saba masa ba mutukar idan umarnin nasa ba shari’a ya sabawa ba….”

Tuni har kwalla ta ciko idanuwan Hanan tun bayan da Abba yasoma yimata wadannan nasihohin,

“Toh Abba insha Allah zanbi umarninka kuma zan kiyaye su….”

“To Allah yayi miki albarka, Allah yabaki zuri’a kema wadanda zasu yimiki ni zanje inkoma….”. Juyawa yayi ga Khalil wanda ke zaune ya tallafe kumatunsa da hannunshi guda daya dayan kuma yana lallatsa wayarshi ba komai kuma yake yiba sai game irin games din da Aryan ke yi idan ya karbi wayarshi,ahaka sai kace ba yajin abinda suke fada amma kuma yana sauraronsu sarai,

“To kai moddibo ni zanje inkoma fa,bako zaiyi halinsa”

Kashe wayar yayi sannan ya kalli Abban Hanan wanda ke kokarin mikewa tsaye,

“Ba zaka sake kwana ba,ai mu bamu gaji dakai ba tukunna”

“Duk da haka gara naje na karasa ai idan nace zan zauna har sai lokacin da zaku gaji dani to ai magana ta baci moddibo”

“To muje kaga Aryan sai mu wuce….”

Hanan na jinsu kuma tunda taga abba yamike tafara sharar hawaye kamar wata karamar yarinya,cikin bedroom dinsa yawuce shi kuma Abba yayi hanyar fita,tana nan zaune tana hawaye sai gashi yafito rike da hularshi a hannunshi,ganinta tsaye tana kuka kuma bata fita ba yazo zai wuce,

“Ko zaki bishi ne?” Shine abinda taji yace kuma bai jira amsarta ba yayi waje abunshi.

Itama bin bayanshi tayi abunka da dogo kamin ta fito har yayi mata nisa,a dakin Aryan ta iskesu Abba nayiwa Aryan wasa ya kama hannunsa yana yimusu sallama ita kam har lokacin kuka take yi,akan idonta Abba yayi musu sallama yatafi,yanzu inbanda aure mai zai rabata da abbanta amma gashi yazo yatafi yabarta,

Tunda Khalil yafita bata kara samun damar ganinsa ba domin duk da yana cikin gidan amma baya ganuwa saboda bakin da yaketa faman yi agida,su kansu cikin gidan kullum cikin baki suke yan dubiya dayawa Hanan ba saninsu tayi ba sai su umma ne da hajiya ke yimata bayanin ko su waye,yan makarantar su Aryan ma sunzo sun dubashi daga students har malaman nasu duka. Yau ma haka suka tashi da bakin daga wadannan sun tafi wasu zasu zo, Abba Khalid ne yau kuma yazo da iyalansa da matarsa Muneerat da yaransa guda biyu Nawwar da Nainah,yau kam Hanan taga su Nawwar din da Aryan kullum ke maganar su kuma take ganinsu a hoto tare dashi,suma yaran kyawawa ne kamar ba yaran hausawa ba koda yake maman nasu kamar irin shuwah shuwah dinnan take sai dai bata da sakin jiki da saurin sabo dan ko magana kayi mata sai dai tayi murmushi ita dai Hanan haka ta sauketa tana ta nan nan dasu shi kuwa Aryan ganinsu Nawwar ai tuni yasake warewa dan har yajasu dakin kayan wasanshi suna can suna fama. Bayan sallar la’asar sun gama lunch kenan ita da Muneerat  adakinta ta kwaso kayan zata kai kasa tahango Khalid da Khalil awurinsu Aryan wadanda suka fito da kekunan Aryan suna yi acikin falon, Khalid na fadin,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button