MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

“A’a lallai sauki yasamu,marar lafiyar nake gani akan keke?”

“Ai nafada maka da kunyi zamanku yasamu lafiya fa…” Khalil yabashi amsa,

“A’a sai munzo mun ganshi ai mun jima bamu ganshi ba dama…”

Hanan karasawa wurinsu tayi ita yanzu ne ma taga Khalil amma yau koda wasa bata ganshi ba inbanda yanzu, kamar kullum yana sanye da farar shadda shi kam da alama yana son fararen kaya koda yake farin abu dama na masu tsafta ne dan kazami bai isa ya saba yanzun nan sai aganeshi,dan dukawa tayi ta gaida Khalid wanda ya riko hannun Aryan yana tambayar shi yajiki,dan juyowa yayi yana amsa gaisuwar tata,

“Lafiya lau madam,ya hakurin zama da wannan sarkin yawon?ki rinka bashi query idan yaki zama agida…” Khalid yafada cikin barkwanci,ita dai shiru tayi ta dan saci kallon Kahlil wanda kamar bai san ma abinda suke fada ba yana tsaye ya dauki Nainah yana tambayar ta wai zatazo hutu suyi wasa da Aryan?

“Ya kuma jikin Aryan? Naga ma ai yasamu sauki to Allah yakara masa lafiya”

Sai lokacin ta amsa da “Jiki ai yayi sauki,amin ya Allah,mun gode madallah”

Juyawa tayi ta koma sama wurin Muneerat duk da ba wata hira zasuyi ba babu jimawa saiga su Aryan sunzo suna kiranta wai tazo inji Abba zasu tafi kar suyi dare ahanya,rasa abinda zata bawa Muneerat tayi sai kawai ta diddibar mata irin humra dinta ta aure acikin kwalabe madaidaita,

A babban falon kasa ta iskesu suna yin sallama dasu hajiya sannan ga kayan dubiya nan anata shigowa dasu wanda Khalid din yakawo kwalayen kayan ciye ciye daban daban da katan katan din lemuka jibgi guda,hannu Khalil yasa a aljihu yaciro rafar kudi yan dubu dubu guda biyu ya mikawa su Nawwar wai susha sweet shima Khalid din duk uban wannan kayan da yakawo sai da yabaiwa Aryan kudi wai yasai alawa bayan gata nan yakawo kaya guda, sallama suka yimusu suka tafi kuma tare suka fita da Khalil din……..鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:09 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*24*

       ***Tun bayan tafiyar su Khalid Hanan bata kara saka Khalil a idonta ba sai washe gari wannan dinma yana kokarin fita ne yashiga wurinsu hajiya ya gaida su daga nan yawuce office wai yana da meeting din gaggawa da shugabnnin wata k’ungiyar matasa, Hanan na dakin zaune itada Aryan suna cin plantain yashigo wanda tun kafin ya karaso kamshinsa na no 1 yariga shi zuwa,

“Mutumin nan dan gayu ne na ajin karshe” 

Hanan tafada acikin zuciyarta domin yayi kyau ba karya cikin farin lallausan yadin dake sanye ajikinsa harda hula amma babu babbar riga ajikinsa,zama yayi suka gaisa dasu hajiya sannan ya mikawa Aryan hannu suka gaisa yana amsa gaisuwar Hanan wacce ke gaisheshi kuma dama gaisuwar bata wuce guda biyu daga ina wuni lafiya shikenan,

Bai jima ba adakin yafita,itama hajiya tun aranar tafara Shirin tafiya domin jikin Aryan yayi sauki sosai kuma sannu ahankali duk farinsa da kamanninsa sun fara dawowa har wata yar kiba yafara yi saboda zaman wuri daya sannan ga kulawa da yake samu daga Hanan dasu umma har kumatu yafara yi,

A kowacce rana Hanan cikin tunanin Khalil take ita kanta tana mamakin yanda tafara damuwa dashi har haka bayan shikuma ba ta ita yakeba domin babu ruwanshi da ita ko maganar shi atakaice take sau da dama idan yana gida suna tare dasu umma sai dai su,su umman suyi ta hirarsu shikuma yayi shiru yana jinsu sai ta kama yake saka baki.

***

  Shawarar muhibba sumayya ta dauka duk da tana son mujahid amma haka ta daure tafara shareshi,ko sun hadu a kitchen ko falo ko compound din gidan yi take yi kamar bata sanshi ba ko bata ganshi ba sai takai makura sannan suke gaisawa gaba daya tayi watsi dashi duk da wani lokacin har kuka takeyi saboda irin yanayin da ta samu kanta na son maso wani.

Shi kuma abun duniya ne yataru ya dameshi sakamakon daina ganin text din Hanan da yayi,to ko lafiya? Kodai mijinta yaga irin sakonnin da take turo masa kullum ya kwace wayar tata?

Wadannan tambayoyin kullum su yake yiwa kansa gashi yasaba da ganin massage din nata shiyasa yakasa samun nutsuwa yana jin kamar wani abune marar dadi ya gifta ko kuma ya faru da ita,kullum cikin duba wayarsa yake waiko zaiga sakonta idan kuwa yaji k’arar shigowar text jikinsa har rawa yake yi atunaninshi ko itace sai ya duba sai yaga sabanin haka nanfa abun yayita damunsa daga karshe ya yanke shawarar kiranta duk da yasan hakan haramun ne amma haka yarufe ido ya kirata,har wayar tayi ta katse bata dauka ba nan yasake kira nan dinma no answer saida yakira sau biyar sannan ya hakura ya hada Kai da gwiwa ya rafka uban tagumi.

***

  Bayan Sati Biyu

Jikin Aryan yayi kyau kusanma za a iya cewa yagama warkewa gaba daya dan har ana maganar zai fara zuwa makaranta domin ana gab da fara exams,ganin yasamu lafiya yasa hajiya komawa gombe itama dama shi Zaid yajima da komawa tun lokacin da Aryan din yafara samun lafiya,ai Hanan ji tayi kamar kada hajiya ta tafi saboda tana mutukar jin dadin zama da ita babu tsangwama babu sa Ido da takurawa irin na wasu surukan,ita abubuwa da yawa ma hajiyan ke matsanta mata akai dan ko abinci ta rinka cewa taje ta zauna taci abinci tabar hidima dasu haka ita kam bazata fadi kiyayyar uwar mijiba duk da zaman nasu baiyi nisaba. Tunda hajiya ta tafi kuma yarage sai su kadai da umma shima Khalil ba ganinsa akeyi ba domin ankoma gidan jiya dan harma yasake fallawa yakoma Florence wato k’asar italy dan dama bawai yagama abinda yaje yi bane lalurar Aryan ce ta dawo dashi amma koda yaushe yanzun ma suna makale awaya,

Ita kam Hanan tana cikin wani hali domin ta samu kanta dumu dumu da tunanin Khalil wanda ke neman tarwatsa kwakwalwarta kullum ita kenan cikin tunani tarasa meke damunta gashi shi bama ya nan kuma koda ace yana nan dinma ba ganinsa take samun yiba sosai sai antaki sa’a,ranar da mujahid yafara kiranta tana gani taki dauka saboda kamar yadda yataba fada mata akan tayiwa iyayenta biyayya ta zauna da mijinta lafiya to ayanzu ta daura aniyar yin hakan idan kuwa hakane to babu bukatar sufara kiran juna awaya yanzu.

Lokuta da dama tana jin Aryan na yin waya da Khalil amma bata tunanin ya t’aba koda tambayar ta amma fa kullum kuma koda yaushe zaka samesu suna video call da d’ansa,ranar da su Aryan suka fara exams ranar yadawo da daddare yasauka a Abuja su PA sukaje suka daukoshi,tana son taje tayi masa sannu da zuwa domin idonta biyu yadawo amma bata son yin abinda ajinta zai zube a idonshi, shiyasa itama ta shareshi kamar yanda shima ya shareta. Washe gari da sassafe suna yin breakfast zasu tafi school sai gashi ya sauko sanye da kananan kaya kuma da alama dasu yayi bacci riga ce jersey fara sol da dogon wando shima fari mai sulbi sunkuyar da kanta tayi aranta tana tunanin wai Wadanne kayane suka fi karbar wannan bawan Allahn? Duk wadanda yasa kyau suke yimasa daga manyan har kananan,bata farga ba taji maganarshi akusa dasu yana yiwa Aryan magana da harshen turanci wai ko bai san yadawo bane yaga bai ganshi yaje bedroom dinshi ba da safe,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button