MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Makalkaleshi Aryan yayi yana murna dagashi yayi cancak daga kan kujerar da yake zaune akai ya rungumeshi yana kissing dinshi,
“Uncle ka siyo min abunda nace kasiyo min?”
“Nasiyo maka Abba na,ai dole insiyo maka,kaje school ka dawo zaka ganshi”
“Thank you Papa…”
“You are always welcome lovely son”
Saida tajira suka gama sannan ta gaidashi,kamar kullum adan ciki ciki ya amsa sannan yawuce yafita daga falon yayi waje,ita kanta tsarin rayuwarshi na burgeta saboda baida girman kai irin na wasu masu kudin sannan bai dauki rayuwarsa da zafiba dan ko yanzu da yafita takalmin roba slippers ne akafarshi amma fa yayi kyau yafito sosai ko dan jiya yadawo daga waje ne oho amma yayi kyau,
Suna fita suka shiga mota kasancewar daga bakin kofa ake ajiye musu motar shima Khalil din haka ne anan ake ajiye masa motarshi yana fitowa sai dai yashiga,daga cikin mota ta hangoshi caan nesa da su da mutane sun yanyameshi ko su wanene oho,kwalla taji ta ciko mata ido tayi saurin gogewa dan kada Aryan yagani.
Bayan dawowarsu daga makaranta tana kwance adakinta tana duba scrip din yara tagaji ta ajiyesu gefe ta kwanta tana hutawa Aryan yashigo da gudu hannunshi rike da wata kyakkyawar yar karamar laptop irin wacce ake siyawa students, ash colour ce mai mutukar kyau ashe dama shine sakon da Aryan ke tambayar Khalil da safe,karba tayi tana fadin,
“Woww…. Yaron babanshi yasamu sabuwar laptop,inye,to maza tafi library kaci gaba da karatu sai anjima sai kafito ka huta kayi game na 15 minutes”
Da gudu yafita ita kuma tashi zaune tayi ta bude laptop din tana dubawa babu komai aciki sai games kala kala da cartoons sai kuma pictures, pictures din tafara bi daya bayan daya tana gani duka na Aryan da Khalil ne tun yana rarrafe gasu nan yayiyyi musu selfie,shagala tayi da kallon hotunan domin mafi yawa daga ciki tare suke kuma sunyi shiga iri daya wato dai atakaice anko yake yi musu dan ko kananan kaya ne yasa sai taga shima Aryan din irinsu yasaka masa, tajima akan wani hotonsu duk sunsha bakaken suit da blue din t shirt aciki sun daura necktie rike da hannun juna awani katafaren wurin shakatawa wanda bata san kowacce k’asa ce ba amma duk fuskokinsu cike da fara’a dan har hakoran Aryan sun bayyana wanda ya daga kansa yana kallon uban, kowannensu idanuwanshi sanye da bakin gilashi wanda yasake kara musu kyau,
“Fatabarakallahu ahsanul kaliqin…..” Tafada tana sake zooming din hoton,tana zuwa kan na gaba taga ashe na baya ba wani kyau yayiba akan na yanzu domin shi na yanzu bakaken wanduna suka saka da jar t shirt sunsa p cap suna zaune akan wata gada cikin babban birnin k’asar ingila dan gashi nan akasan hoton anrubuta London Vive,haka tayita rudewa tana kasa banbance wacce shiga ce tafi yimusu kyau domin wani shigar manyan kaya sukayi iri daya har hula wani kuma jallabiya ma suka saka iri daya da yar karamar hularta amma yawanci a saudiyya ne suka yi wadannan shigar,
“Aryan dan gata”
Ta furta hakan acan kasan makoshinta sakamakon ganin pic din birthday dinshi na cika shekara biyar da tayi,shima ankon sukayi da uban kowa yasha bakin jeans da maroon din riga suna bawa juna cake abaki duk suna yin dariya……………..鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:09 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*25*
***Har Aryan yadawo bata samu zarafin gama kallon wannan pictures dinba wadanda ke shirin zautar da ita hakika sai yaune ta sake tabbatarwa da kanta cewa Khalil dan kwalisa ne kuma cikakken dan gayu sannan idan har ba fada maka akayiba wallahi baza ka taba cewa Aryan danshi ne na cikinsa ba duk da suna mutukar kama da Aryan din amma fuskar Khalil babu girma atare da ita yarinta ce fal kwance akai,
Jin Aryan yafada kanta yasata ajiye laptop din tana dubanshi,
“Wai har kayi me cutie?”
“Mommy har nagama karatun”
Kanshi ta shafa sannan tace,
“A’a cutie baka gama ba ka dai fito break ko?”
Kai ya daga mata yana kaiwa babban dan yatsanshi baki hannun ta buge saboda yanzu dabi’ar da ya ke neman koya kenan shan hannu tun bayan rashin lafiyarsa amma da ba haka yake ba,
“Cutie ba na hanaka shan hannu ba? Ka daina kaji yaron kirki…”
Kai ya daga mata yana jan hannunta,tashi tayi tabishi suka sauka k’asa ta kofar baya suka bi suka fita sune har garden gashi garin da alamar hadari kuma yagama haduwa,
Acan ruwan ya iskesu,da gudu suka shigo ciki ita kam cikin ruwan ta shiga ta hanyar shiga cikin wani dan karamin fili dake tsakanin part din Khalil da nata,filine fetal an shuka flowers kala kala awurin amma babu kasa gaba daya rufe yake da interlock an kawatashi yadda yakamata,
Sosai take jin dadin ruwan yanda yake sauka ajikinta, Aryan ne shima yashigo yana ta tsalle acikin ruwan yana jikasu,
Shigowar shi kenan cikin sashensa yashiga bedroom dinshi yasoma rage kayan jikinsa farar t shirt da bakin dogon wando yasaka yana son shiga yayi wanka kamar ance ya kalli window yanufi gaban windown yana shirin rufewa, Hanan ya hango a kasa ita da Aryan cikin ruwa suna ta wasan banza atoh wasan banza mana tunda wasan ruwa suke yi, wannan yarinyar bata da hankali yanzu da taja masa yaro takaishi cikin ruwa idan mura ta kamashi ko zazzabi fa?
Da sauri yabar wurin window din yafita daga dakin ya sauka zuwa kasa a hanzarce,
Sam Hanan bata san cewa yadawo gidan ba saboda lokacin dawowarshi baiyi ba dan sai dare kuma darenma bawai na kusa ba,
“Aryan….. what are you doing there?”
Dukkansu juyawa sukayi wurin da suka jiyo maganar shi,shi dinma tsaye yayi yana kallonsu cike da takaici dan gaba daya sun jike jagaf,kunya da tsoro taji sun rufeta lokaci guda,shi kam kama kunnen Aryan yayi guda daya yana yimasa fada,
“Idan nasake ganin kayi wasan ruwa nida kaine…” Juyawa yayi ga Hanan,
“Nan gaba idan zakiyi wasan ruwanki kiyi ke daya karki sake kai min yaro cikin ruwa…”
Daga haka yahaura sama yana cewa Aryan yaje umma ta sauya masa kayan jikinsa,jan hannunsa Hanan tayi suka je dakinsa ta sauya masa kaya bayan ta goggoge masa jikinsa,kayan sanyi ta saka masa sannan itama tawuce d’akinta taje ta cire nata kayan ta sauya wasu,tun daga wannan lokacin bata sake ganinshi ba shima haka,duk abin duniya ya taru ya isheta yayi mata yawa,haka dai taci gaba da daurewa tana yin al’amuranta amma can kasan ranta akwai damuwa atattare da ita. Kusan kullum sai sun gaisa da yan gidansu musamman ma mamaye haka itama anty salaha jifa jifa suna gaisaw musamman ma ta chat. A kwana atashi har su Aryan sun gama exams dinsu kuma ranar Friday ake sa ran yin hutu, kasancewar hutun azumi za ayi Khalil yana da burin kaisu gombe sai suyi azumi da salla acan shikam duk Ramadan umarah suke tafiya shida Aryan sai ankusa salla suke dawowa wani time dinma sai bayan sallar sannan suke dawowa,
Ranar Friday akayi hutu bayan anrabawa yara results dinsu,tun a makaranta Hanan taga result din Aryan kuma tayi farin ciki sosai domin ya dauki first position kamar yanda yasaba, Khalil kuwa da yagani farin doki yabada aka siyo masa domin Aryan na masifar son doki tun yana dan mitsitsi. Tunda akayi hutu kuma sai zaman gida babu wurin zuwa duk zaman nan yabi ya ishi Hanan,kullum kai kenan agida babu fita sai hira da umma da koyar da Aryan dan dama tun bayan warkewarsa take koya masa littafin (hisnul ad’fal) wato littafi mai dauke da addu’o’in yara wadanda zasu rinka yi dan samun kariya,