MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Sati daya da yin hutun taga text din Khalil wai ta shirya zasu tafi gombe kuma acan zasu yi azumi,wani dadi taji ya lullube ta domin tasan zaman gombe zaifi na Abuja dadi saboda can akwai mutane ba kamar nan ba,duk wani abu wanda tasan zata bukata ta dauki abinta haka shima Aryan ta shirya masa nasa kayan,ranar asabar da daddare bayan Khalil yadawo daga office suka dauki hanyar gombe, Aryan ne agaba sai shida ita abaya ita kuma umma motarta daban,tunda Hanan ta shiga cikin motar tayi shiru ta kasa ko kwakkwaran motsi amma fa motar ta tafi da ita domin sanyin AC kadai ke shigarta gashi hatta kujerar motar wani azababben laushi gareta wannan motar ita dai aganinta bata da maraba da jirgin sama kawai dan dai shi asama yake ne ita kuma a kasa,tv taga ya kunna wacce ke cikin motar,daga shi har ita babu mai cewa koda uffan sai dai yana ta amsa wayoyi lokaci zuwa lokaci,wani abu da yasake burgeta shine duk inda sukaje check point ba a tsayar dasu da sunzo zasu wuce shiyasa tafiyar tasu tayi sauri gaskiya masu kudi suna cikin ni’ima domin suna fantamawa son ransu ashe shiyasa Khalil bai jin wahalar tafiya kullum yana bisa hanya,
Suna shiga garin gombe duk da cewa dare ne amma mutane sai faman daga musu hannu suke gashi dai na waje ba ganin na ciki yake ba tun daga nan Hanan tasan jama’ar garin na sonsa kuma suna yinsa domin masu babura rakasu suka yi har kofar gida,ita kam ta bude ido tana ganin yanda garin yake domin wannan shine ganinta na farko dan lokacin da aka kawota tana amarya babu abinda ta samu damar gani shiyasa yau take ta baza idanuwa tana kallo. Suna shiga cikin gidan securities suka fito suka bubbude musu kofa ita abinma kusan mamaki yake bata wai yau itace cikin wannan daular ana girmamata kamar wata matar governor,kai tsaye cikin gidan suka shiga tare da umma da Aryan,
Duk yanmatan gidan suna tare da hajiya ana sauraren zuwansu ganin Aryan dake gaba yasa yanmatan rige rigen zuwa daukarshi shi kuma sai ya gudu ya haye kan cinyar hajiya yana boye fuskarshi cikin jikinta,
“Ja’iri ashe dai baka manta dokaka da kasar da suka taba yiba,sarkin wayo” Inji hajiya,
Kowa dake wurin dariya yayi,a kasa Hanan ta zauna tana gaida hajiya,duk da hajiyan tace ta koma kan kujera ta zauna amma taki anan taci gaba da zama zuwa can aka fara shigo musu da kayayyakin su wanda suka zo dashi, ita kuwa Hanan tuni ancika mata gabanta da kayan cima iri iri hajiya tana ta cewa taci abinci taje ta huta, abincin suka ci ita da Aryan sannan suka wuce dakin dake ciki wanda ko lokacin da tana amarya anan aka sauketa,wanka tayiwa Aryan tayi masa shirin bacci ya kwanta sannan itama taje tayi tazo ta kwanta ta san idan ba wani iko na Allah ba sai Khalil yashigo dakin nan komai dare yaga Aryan saboda tun da sukazo basu kara sakashi a idanuwansu ba yana can tare da baki tunda baya rabuwa dasu. Kamar Hanan ta sani kuwa domin tun bayan zuwansu Khalil salla kawai yasamu yayi daga nan yaketa ganawa da baki bai samu kansa ba sai karfe dayan dare saura yan mintuna gashi cikinsa inbanda yunwa babu abinda yake ji,kuma dadin dadawa ma kofa gaisawa da hajiya basuyi ba,
Tunda yaji part din hajiya shiru yasan kowa yayi bacci agidan amma yana shiga ita ya sameta ido biyu tana zaman jiran zuwanshi yaci abinci kuma su gaisa,kansa babu hula ya zauna nan kasa inda Hanan ta zauna dazu,
“Hajiya mun sameku lafiya?”
“Lafiya lau Khalil ya fama da jama’a? Ga abinci zuba kaci”
“Hajiya ai fama da jama’a kam sai godiyar Allah wallahi rabona da abinci tun wani ruwan tea da na sha da safe a office da meatballs guda biyu shikenan,ko gidana sai dazu da zamu taho nasamu naje daga can muka iyo nan…. Kai rayuwar nan tana da wahala babu komai acikinta face gwagwarmaya da fafutuka astagfirullah”
“To ya za ayi Khalil sai dai fatan lafiya da taimakon ubangiji,nauyine Allah yariga da ya dora maka kana yaronka dakai sai dai fatan Allah yabaka ikon saukeshi”
“Amin hajiya,nauyifa mutum da kuruciyarshi da komai wallahi,duk cikin ministocin nan nine yaro wasunsu ma sun kusa haifata ni wallahi banma san ta yadda akayi na zama ba….”
Dariya hajiya tayi ta dan kishingida ajikin kujera,
“To inbanda abinka Khalil shi hukuncin Allah ai ba ruwansa da girma ko shekaru,haka Allah ya tsara maka, Allah dai yabaka ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyanka”
“Amin hajiya,shi wannan yayi bacci ko?”
“Ehh Aryan ba,yayi bacci ai tunda jimawa,kuma nace maimakon ka kai matar taka sashenka shikenan sai akawota nan?”
Dan shiru yayi ya shafi kansa sannan ya ce,
“Hajiya wanne bangaren nawa kuma bayan daki dayane aciki,muje muyi zaman takura haka kawai….”
“Idanma babu dakin ba matarka bace? Ko zaman gaban takura zakuyi kuyi mana ai canne yafi dacewa da ita,kuma kasan ai daki dayanne amma ka daukosu kuka taho”
“Gaskiya hajiya daki daya yayi mana kadan”
“To ba sai kasake gina muku waniba tunda kana da halin yi amma dai babu tsari ace kana can matarka tana nan,yanzu idan kana bukatar tayi maka wani abu sai kazo kana tasota daga nan tana tafiya can?”
“Hajiya ni kwana nawa ma zanyi agarinne? Dududu kwana hudu fa zanyi ko biyar mutafi umarah nida Aryan….”
“Kaida Aryan? Ita kuma matar taka fa? Wa zaka barwa ita?”
Shiru yayi yana tunanin abinda yadace yafada wanda hajiya ba zata yimasa fada ba,ruwa ya dan kurba sannan yace,
“Ai hajiya bana visa dince tayi wahala kuma da har ita naso hadawa amma abun ya faskara mukuma ai kinga permanent Visa garemu shiyasa…”
“Ai shikenan amma gaskiya banji dadin tafiya kubarta ita kuma ananba da zakuyi gaskiya….”
“Hajiya kiyi mana addu’ar dai Allah yasa hakanne yafi zama alkhairi”
“To amin, Allah yadawo daku lafiya, Allah yatsareka ya kareka ya tsare maka dukiyarka da zuri’arka, Allah ya rabaka da mugun ji da mugun gani ya shiga lamarinka akoda yaushe….”
“Amin hajiya…”
Saida yakai wurin karfe 2 na dare shida hajiya sannan yatashi yafita ya nufi bangarensa aransa yana tunanin ai kamar fa tunda yazo baiga Zaid ba anya kuwa yana nan? Kai duk yanda akayi zaid baya garin nan dan kuwa da yana nan da yaganshi. Duk jikinsa a gajiye haka ya lallaba ya daure yayi wanka yasaka kayan bacci yahaye gado yana kallon agogo,karfe 3 saura na dare,yanzu hajiya da take cewa ya hada daki da yarinyar can ai da takurashi za ayi haka kawai abanza shi harma mantawa yake yi da wai ita matarsa ce kawai abinda yasani ya kawowa Aryan friend wanda zata rinka debe masa kewa.
Washe gari ya dan samu zarafin komawa baccin safe, Aryan kuwa tunda yatashi Hanan ta shiryashi cikin kananan kaya bakar t shirt ta polo da blue din jeans tasa masa combos shima baki bata sake ganinsa ba dan wurin hajiya yaje ta can ya gudu wurin babansa dan shine ma ya tashi Khalil din, rungumeshi yayi yana shafa sumar kanshi,
“Waye ya yi maka wanka?”
“Momy ce..”
“Uhmm dan gatan mommy…”
“Mommy tana sona…”
Murmushi Khalil yayi ya tashi zaune yana daukar wayarshi domin kira yashigo,
“Hajiya ina kwana…… lafiya lau….gashi muna tare dashi ai……ehhhh….kokon dai hajiya…..to shikenan sai na shigo”
Daga haka ya katse wayar yabawa Aryan shikuma yashiga bathroom domin yin wanka,har yafito ya shirya Aryan na kwance kan gadon yana ta faman matse matse awayar kamar tashi cemasa yayi kar dai ya yarda yayi masa deleting din wani abu garin wannan matse matsen nasa,shiryawa Khalil din yayi cikin wata farar shadda yasha turare,ba dan hajiya tace yajira akawo masa breakfast ba da fita zaiyi.