MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Hanan tunda ta gama shiryawa tayi zamanta adaki saida hajiya ta turo mufida kiranta sannan tafita,wata dark purple din atamfa ce ajikinta doguwar riga tasha turare mai sanyin kamshi,gaida hajiya tayi sannan hajiya ta nuna mata breakfast din Khalil wai idan tagama karyawa shima taje ta kai masa mufida ta rakata ko zarah,tea ta hada ta sha ta danci awarar da aka soya da kwai sannan ta tashi suka fita ita da zarah dauke da kayan breakfast din Khalil,

Part din nashi dan karami ne bawani babba ba saiko kayan alatu da yasha,suna zaune falo shida Aryan wanda keta waya dasu Nawwar awayar Khalil daga jin Khalid ya kirashi suna magana shikenan yakafa rigimar sai anbashi ana bashi kuma suma su Nawwar din suka karbe kan wayar tun dazu suketa hirar da taki karewa domin sai labari suke ta bawa juna,durkusawa zarah tayi ta gaidashi sannan ta ajiye kayan dake hannunta tafita,itama Hanan din gaisheshi tayi suka gaisa kamar yanda aka saba ina kwana lafiya shikenan,ta mike zata fita taji yace, “Zo nan”

Dawowa tayi ta zauna amma baice da ita komai ba saima kayan breakfast dinshi da yajawo yabude ya tsiyayi koko a cup sannan ya bude flask din soyayyiyar awara da kwai ya diba a plate ya zuba vegetables sos akai yasa spoon yafara ci,duk sai taji ta takura domin basu taba zama haka su biyu ba awuri duk da Aryan yana wurin,

Ganin wayar Aryan ba mai karewa bace yasa Khalil kwace wayar ya kashe yace maza ya zauna suci abinci shi baya son cin abinci sai anyi masa dabara,yanzun ma saida dabarar shima yabashi yaci. Suna zaune shiru amma jifa jifa Aryan na yin surutunshi ahaka akayi knocking a jikin kofa, zaid ne amma ganinsu duka sai yakoma Khalil nata kiransa amma bai dawoba,ita dai duk da tana jin dadin zaman wurin amma ta kosa ta tafi domin zuciyarta kamar zata faso kirjinta tafito dan tsananin bugun da takeyi,saida suka gama sannan yace sutafi cikin gida ita da Aryan,shikuma yafita tun daga nan kuma ganinsa yayi mata wahala dan bata ganinsa sai kowacce safiya da zarar yafita kuma shikenan dan lokacin da yake shigowa da daddare tuni sun kwanta,ita kanta hajiya fadan da take yimasa kenan wai bata ga yana jan matarsa ajiki yana kiranta suna hira ba shi kuma sai cewa yayi wai ai duk sanda taje wurinshi da safe kai masa abinci suna tattaunawa. Kwanansu hudu da zuwa yace ashiryawa Aryan kayansa saboda zasu iya tafiya a kowanne lokaci, lokacin ana saka ran ganin watan Ramadan nan da kwanaki biyu zuwa uku,daren asubar da zasu tashi tana daki kwance har tayi shirin bacci hajiya ta aiko kiranta,koda taje hajiya cewa tayi wai ta je wurin Khalil ta kwana acan suyi sallama, innalillahi ita dai gashi ba damar tayi musu da hajiya gashi bata jin zata iya zuwa gareshi a wannan lokacin,jiki a mace ta tashi takoma dakin da ta sauka tafi minti goma tana tsaye tana kallon Aryan dake kwance yana bacci sannan ta dauki hijabi har kasa tasa ta fita rike da wayarta a hannu,gidan tamkar rana dan tsabar haske baka jin motsin kowa sai karar injin bada wutar lantarki da ke tashi,tana sake kusantar sashen nasa faduwar gabanta na karuwa jikinta na rawa ahaka taje,ta jima tsaye a bakin kofar falonshi tarasa ta yadda zata shiga ciki,dakyar tayi ta maza ta bude kofar ta sa kai tana jin numfashinta yana tsinkewa kamar zai fice gaba daya…………………鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:11 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*26*

      ***Kasa daga kafarta tayi daga nan inda take tsaye bayan tashiga cikin falon nasa wanda kamshinsa ke kai komo acikinsa,

Wuri ta samu ta zauna saman kujera tana kallon kowacce kusurwa da lungu dake cikin falon wanda yake dan madaidaici sai dai kuma antsarashi yadda yadace dan yayi mata kyau kamar irin dan bangaren nan na ango da amarya auren saurayi da budurwa, ango da yar amaryar sa ya ishesu rayuwa kafin su tara ‘yaya,komai na ciki milk  ne and coffee colour gashi tsaf tsaf babu datti babu kura yayi kyau gwanin ban sha’awa. Idonta ne yakai kan wayar Khalil dake kan wani center table na glass dake can gefe daya take ta sake jin faduwar gabanta ta karu da kaso tamanin cikin dari na wadda takeji dazu,

Fitowarsa kenan daga wanka yasaka farar jersey mai ratsin blue agefe da gefenta sai wandon rigar shima fari amma dogone dan har ya rufe gwiwarshi,falo yafita domin dauko daya daga cikin wayarshi da ya ajiye acan,yana fitowa yaganta zaune ta tukunkune cikin hijabi ba dan yasan da zuwanta ba da babu abinda zai hana ya tsorata to dan dai hajiya ta sanar dashi ne dazun nan da yashigo tagama kora masa jawabin wai yakamata matarsa taje suyi sallama kuma yaji ko tana da wata damuwa,

“Kowacce irin sallama hajiya take son muyi oho…”

Yafada acikin ransa yana kokarin daukar wayarshi,cikin sanyin murya yaji tana gaisheshi nan ya amsa kamar koda yaushe cikin rashin son doguwar magana,ita dai tun kallon farko da tayi masa bata sake kallonshi ba domin yau yasake yimata kwarjini fiye da sauran ranakun baya gashi kayan jikinsa sun dan kamashi. Wuri shima yasamu ya zauna afalon yadora kafa daya akan daya yana duba tulin sakonnin dake cikin wayar wadanda aka turo masa kuma mafi yawa ba sanin wadanda suka turo yayi ba,

Hanan gyangyadi tafara domin tuni 12 ta dan gota ita kuma ba saba dogon zama tayiba karkarinta takai 11 wannan dinma sai da dalili amma wani lokacin 10 tayi baccinta saboda fitar sassafe. Lura yayi da gyangyadin da take yi dan haka yayi mata magana cikin muryar sa mai cike da sanyi,taushi da kuma gardi,

“Shiga ciki ki kwanta…” Taji yafada amma bawai dan yasoba domin harga Allah shifa takurashi akayi da aka turo masa yarinyar nan,yanzu dole sai taje ta hau masa kan gadonsa shikuma abarshi yayi kwanan takura a falo,

Kasancewar itama bawai awani sake take dashi ba yasata girgiza kanta tace,”A’a nanma ya isa”

Iya nan din da ta furta kawai ya iyaji dan haka yaci gaba da abinda yake tsawon mintuna goma yagama yatashi yawuce cikin bedroom dinshi harda rofo kofa,saman gadonshi ya haye yai kwanciyar sa bayan ya kara karfin na’urar sanyaya daki,itama Hanan anan ta bingire kan 3 sitter bacci yayi gaba da ita,ba ita ta tashi ba sai asubah kasancewar tasaba tashi yau dinma lokacin salla nayi ta tashi duk jikinta ciwo yake yimata saboda baccin da tayi a takure shikuwa wuyanta ya kage bata ko iya juyashi Sosai sakamakon pillow da tayi da hannun kujera,fitowarshi taji daga cikin daki,sanye yake da jallabiya kalar ruwan kasa hannunsa rike da casbaha,ganinta zaune alamar ta tashi yasashi wucewa yafita zuwa masallacin da ke cikin gidan,tana ganin haka itama taja jikinta tafice ta nufi bangaren hajiya sadaf sadaf kamar wata marar gaskiya,da sand’a ta shiga dakin da ta sauka tasamu Aryan yanata sharar baccinsa cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi tashiga toilet, brush tayi sannan tayi alwala tafito,nan inda tayi salla anan wani bacci mai shegen dadi yayi awon gaba da ita,cikin baccin ta soma wani mafarki da wata mata wai ita Hanan din tana rike da Aryan suna ta gudu cikin dokar daji ita kuma matar tana binsu wai ala dole sai ta kwace Aryan daga wurinta,gudu take cin karfinta har tazo wani bakin ruwa mai yawa ga kuma matar ta kusan cimmusu firgigit tayi ta tashi sakamakon tashinta da Aryan din ke yi,janshi tayi tana dudduba jikinsa domin  taga ko lafiya yake gaba daya ta gama jikewa jagab da gumi,ganinshi tayi ras saima fararen hakoransa da yake washe mata yana nuna mata sabbin kaya yan kanti da hajiya tasaka masa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button