MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Window ta kalla nan taga rana har tafito sosai tayi mamakin irin baccin da tayi daga yar kwanciya, sauri sauri tayi wanka tafito ta shirya ta saka atamfa pink colour dinkin riga da skirt wadanda suka yimata caras cass,tana kokarin fesa turare zarah ta shigo cikin dakin rike da farantin abinci,

“Anty ina kwana? Yau kin makara,ga breakfast dinki inji hajiya”

Da fara’a itama ta juya ta kalli zarah wacce ke kokarin ajiye mata farantin akan rug din dake gaban gado,

“Lafiya lau zarah,wallahi na makara ina kokarin fitowa ma da yanzu,bari to nafara karyawar”

Fita zarah tayi tana murmushi ita kuma Hanan tayi sakare aranta tana fatan Allah yasa dai kar su hajiya su zargi wani abu akan makarar nan tata tunda jiya taje wajen Khalil. Aryan ta kira suka zauna tare suka karya da wainar shinkafa da miyar agushi sai kunun gyada da shinkafa da tea da bread ga kuma wainar kwai agefe,sai da suka koshi damm sannan tafita duk kunya ta cika mata ciki domin aganinta hajiya zata tsammaci dan taje wurin mijine shiyasa ta makara amma koda ta fita hajiya fuska asake kuma awashe ta karbi gaisuwarta har tana cemata umma barira ta tafi funakaye tace afada mata sai nan da sati biyu sannan zata dawo,

Tana zaune tare dasu hajiya Khalil yashigo cikin ash din shadda yau ne kadai Hanan zata ce ta ganshi da wasu kaya sabanin farare tun daga ranar da ta fara ganinsa,

“Hajiya zamuje mu wuce….Sai Allah yadawo damu” Taji yafada yana zama kujerer dake kusa da ta hajiya,

“To mu’azzam Allah yadawo daku lafiya, Allah ya kiyaye hanya”

Tashi hajiya tayi tabasu wuri wai ko zasu tattauna wani abu da matarsa,

“Ina kwana?” Hanan ta fada tana wasa da yan yatsun hannunta kanta akasa,

“Lafiya lau….”

Daga haka bai kara cewa komai ba sai waya da taga ya daga yana magana cikin sanyin murya da rashin hayaniya,

“Kana jina….. Na warewa PA dina komai awurinsa zaka karba,akwai kayan marayu yadina da shaddodi da atamfofi bandir dari biyar biyar na zawarawan da mazajensu suka rasu ma haka da tsoffi,sai kayan abinci shima shinkafa da hatsi  da masara da sugar da man gyada shima kowanne guda dari biyar biyar akai musu a rarraba dan Allah…. Idan kuma akwai wani abu da kuke bukata kayi wa PA dina magana zai sanar dani komai…amin….Amin nagode”

Saida ya gama wayar sannan ya juya ga Hanan wacce har lokacin kanta na kasa aranta tana jin dadin abinda taji Khalil din yayi wato taimakon marayu da marassa karfi acikin wata mai falala kuma gashi harda kayan salla gaskiya yayi kokari dole yarinka ganin budi cikin harkokinsa domin taimakawa marayu da yake yi, muryar sa tajiyo yana cemata,

“Idan kina bukatar wani abu ki fadawa hajiya zata baki…”

Ganin yamike yasa itama ta mike tana jijjiga kai,

“Tom, Allah yadawo daku lafiya”

“Amin”

Kai tsaye dakin hajiya yashiga suka fito tare tana rike da Aryan, rungume ta Aryan yayi suka yi sallama sannan suka fita, itama bin sahun masu yimusu rakiya zuwa compound din gidan tayi tana rike da hannun Aryan,sai bayan da suka ga tafiyarsu sannan suka koma cikin gida kowannensu zuciyarshi cike da kewa musamman ma ita wacce tayi mugun sabo da Aryan.

Kamar yanda ta tsammata hakance ta faru wato daren yau sai takasa bacci tunanin Khalil da gudan jininsa Aryan sune suka tsaya mata arai tana jin kamar tayi tsuntsuwa taje garesu,

Haka tayita kewarsu cikin kwanakin har zuwa ranar da Aryan ya kirata lokacin kwanansu hudu da tafiya kuma ranar aka kai azumi na farko,sunsha hira sosai da Aryan da yake gwanin surutu ne,

Haka rayuwa tayi ta tafiya idan tace acikin zaman da takeyi a gidansu Khalil wani yataba sab’a mata ko yayi mata ba daidai ba to tayi karya,kusan kullum suna gaisawa da yan gidansu ranar ma abbanta yake sanar da ita wai Khalil ya aika musu da kayan azumi da na salla ita dai batace komai ba domin rabonta dashi tun ranar da yatafi umarah sabanin d’ansa da kullum sai sun gaisa,hajiyarsa kuwa tana tattalinta kamar me kullum Cikin hidima da ita ake babu abinda take yi sai dai taci ta kwanta dinkin sallah kuwa kaya kala biyar hajiya ta bada aka dinko mata da mayafinsu da takalmi ko kadan hajiya bata yi la’akari da cewa wai anyi mata lefe mai uban yawa ba. Ana saura kwana biyu salla su zarah suka matsanta mata wai dole sai sunje gidan kunshi tare,ita wallahi a budget dinta babu wani maganar yin kunshi amma irin yanda suka bi suka takura mata yasata yarda zasuje din, Khalil tayiwa text cewa zata fita zataje gidan kunshi,kamar koda yaushe ok kawai yace mata hakan ya tabbatar mata da cewa kenan yabarta taje,

Su hudu suka tafi sukaje akayi musu jan k’unshi mai hade da baki kuma tun safe suka bar gidan amma har la’asar suna gidan kunshin hajiya ajima kadan ta kira tace har yanzu ba agama ba saboda Hanan ce kadai keyin azumi acikinsu ranar su dukansu su ukun basa yi ita Sarah dama sam bata ma yin azumi saboda lalurarta ba mai cikakkiyar lafiya bace ita.

Sai da aka kusan shan ruwa sannan suka baro gidan kunshin nan suna dawowa gida ana shan ruwa sai dai fa amma mai kunshin ta iya kwararriya ce sosai domin duk ta rangade musu kafafuwa da hannaye sai yanzu suka fahimci dalilin da yasa kunshinta keda tsada ashe ta iyane sosai,washe gari kuma kitso aka zo aka yimusu har gida mai kitson hajiya itama ta iya babu laifi,

Bayan ansha ruwa an idar da sallar tarawih suna baje falon Hanan tana kwanciyar gajiya saboda azumin yau dinnan tajishi sosai bada wasa ba kamar bazata kai ba gashi wani abun al’ajabi azumin bana bata sha ko daya ba bata taba fashin shan azumi ba sai wannan karon ita wani lokacin ma azumi sai tasha sau biyu farkonshi da karshensa amma wannan karon bata shaba kwata kwata,babu ko dan kwali akanta hancinta yafara jiyo mata kamshinsa na turaren no 1 ai kuwa wannan turare yaci sunansa domin no 1 dinne wurin zama ajikin mutum dan yariga da ya zauna ajikinsa,

Muryarsa tajiyo yana dososu yana yin magana awaya cikin kwantacciyar muryar nan tashi mai ratsa zuciyar duk wani wanda ke sauraronta,

“Ehh wallahi dawowa ta ma kenan yanzun nan muka sauka…… Ai dama ta gombe natafi wannan karon…. Ehh insha Allah anan zamuyi sallah…. Ok har kashigo ne?….. To Allah yakawoku lafiya”

Sam bata yi yunkurin tashiba dan tasan ba iyawa zata yiba,karadin Aryan suka jiyo shida Zaid wanda ke rike da hannunshi,ayanda take akwancen nan haka suka shigo suka isketa sai dan kwali kawai da taja ta rufe kanta duk su zarah sannu da zuwa suka shiga yimasa ita kuma Aryan yazo ya murkusheta yana murna da farin cikin ganinta,ita ma sannu da zuwa tace dashi idonta na kan farar kafarshi dake sanye cikin takalmi half cover fari tatas,da yawwa kawai ya amsa mata yawuce ciki,

Suna nan zaune Aryan yasasu agaba da labari Khalil din yafito tunda yatafi kuma shikenan sai kayansu aka shigo dashi shi kam har yayi wani wurin,tsaraba kam Hanan tasha ta wacce Aryan yakawo mata kuma ba komai bane sai tarin chocolate kala daban daban da dabino shikenan,shi kuwa uban gayyar babu wanda yasiyowa koda tsinke amma ya sissiyo zam zam da su dabino Sosai shi dama haka tafiyar shi take baya iyo tsaraba idan kaga yasiyo abu to Aryan ya tahowa dashi yanzunma ga kayan wasa nan iri iri yatahowa da Aryan,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button