MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Washe gari yakama ranar salla, babbar Rana kuma mai bikin daya rana haka kuma mai dogon baya,kowa kagani cikin farin ciki da nishadi yake,ita tayiwa Aryan wanka sannan tayi masa shirin masallaci domin tare da Daddynshi zasu tafi,wata arniyar shadda aka dinka masa skye blue riga da wando da babbar riga harda hula dinkin yar bama,da takalminsa sau ciki baki mai masifar kyau,saida ta fesheshi da turare sannan ta yiyyi masa hotuna daga nan yafice yanufi bangaren mahaifin sa,
Ita kam dama bata da niyyar zuwa masallaci sallar idi wankanta tayi ta shirya cikin leshinta dan ubansu golden colour dinkin bubu wanda yayi mata kyau sosai,daurin dan kwalin maryam babangida tayi sannan ta yafa farin mayafi ta fita,tunda aka sauko daga sallar idi gidan ke daukar baki wasu dayawa ma bata sansu ba gashi sai raye raye da bushe bushe ake ta faman yi agidan abinci kuwa kala kala gashi nan sai wanda ka zaba cikin manya manyan warmers wanda aka iyo musamman dan ranar yau,ita dai tuwon shinkafa taci ta kora da lemon jarka,
Bayan ta dan nutsu ta kira duk yan uwa da abokan arziki tayi musu barka da sallah bayan tagama ta yafa mayafi tafita kanta babu dan kwali sai mayafin da ta lullube kanta dashi tana fita falo idanuwanta suka sarke da nashi wanda ke zaune falon hajiya shida Khalid suna cin abinci wata faduwar gaba ce mai tsanani ta ziyarceta cikin gaggawa ta sauke nata idon k’asa,gaishesu tayi sannan ta juya da niyyar komawa amma sai tajiyo muryar Khalid yana cewa,
“Ahh madam dawo mana mu gama gaisawa…”
Dawowa tayi ta zauna duk atakure tana jinsu sunata hira amma muryar Khalid tafi tashi dan shi Khalil ma kamar adole yake yin maganar,
“Wai kasan yarinyar nan me tace min last time? Wai su Nawwar da Nainah sun isheta bata son ta sake haihuwa ita planning zata yi kaza da kaza ko kasan asatin da ta fara planning din a lokacin ta samu ciki…..”
“Baka yi da wasa ba kenan…..” Khalil yafada yana dariya ciki ciki,ita Hanan bata ma ji abinda Khalil din yafada ba kawai dai taji Khalid yace,
“Atoh ba kai ka tsaya wasa ba….”
“Kai ai gashi nan kayi dagaske…”
“To anfada maka ni rago ne irinka? Kai a wannan fannin ai lazy ne….”
“Na taba yi agabanka ne ka gani?”
“Ai alamar karfi tana ga mai kiba,madam saifa kin hadawa wannan tuzurun da yan dabaru ko ya samu yarinka yin abin arziki” Khalid ya karasa maganar yana kallon Hanan wacce sam bata fahimci inda zancen nasu ya dosa ba kasancewar bata jin abinda Khalil yake fada domin maganar tashi k’asa k’asa yake yinta yanda bazata jiba,jin Khalid na shirin yimasa b’arin zance yasashi daga manyan idanuwanshi ya kalleta kamar ance ta kalli wurin da yake nan suka hada ido bakinshi kawai taga ya motsa amma bata ji abinda yace ba sai dai jikinta yabata cewar cewa yayi “Tashi daga nan”,jikinta yayi lakwas kamar anyi mata duka tayi azamar tashi ta wuce ciki ba tare da jinkirin ko sakwan daya ba………………..鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:11 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*27*
***Kai tsaye daki ta wuce wurinsu zarah wad’anda ke ta faman daukar hotuna kamar babu gobe,zama tayi cikinsu sai dai gaba daya hankalinta yana can tare da Khalil wato yau dinnan mutumin ya tsokano kyau kamar dan shi kadai aka kera shaddar da ke jikinsa wadda ta kasance irin ta Aryan sak domin anko suka yi yahadu yau dinnan karshen haduwa,
Acan falo kuwa bayan Hanan ta tashi tabar wurin Khalid kallon Khalil yayi yace,
“Anya kuwa mutumin nan? Anya kuwa?”
“Anya me?” Khalil ya bukata cikin rashin son maganar tayi nisa,
“Gaskiya Khalil ya kamata ka gyara nidai bazan gaji da fada maka gaskiya ba amma yadai dace kayi abinda yadace a lokacin da ya dace,ina dalilin kullum shekaru na tafiya sannan ka kawo yarinya karama ka ajiye a tangamemen gida amma ka kasa kulawa da da ita….”
“Itace ta fada maka bana bata kulawa?”
“Sai ta fada? Ai basai ta fada minba,haba Khalil wai kai wanne irin mutum ne, wannan abun fa da kake yi hadda zalunci idan baka saniba domin itama tana da hakki akanka amma haka kawai dan wani banzan tunani irin naka da taurin kai ka zauna kana cutar da yarinya…. wallahi kaji tsoron Allah”
Shiru Khalil yayi masa hakan yabawa Khalid damar cigaba daga inda ya tsaya ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,
“Kaga malam dan Allah ka rabu dani bana son hayaniya,ko insakar maka ita ka aurane tunda kace ni zaluntarta nake yi? Kai sai ka aureta kayi mata adalci” Khalil yafada yana cigaba da cin abincin dake gabanshi kuma sai ka rantse da Allah bashi ne yayi maganar ba, jijjiga kai Khalid yayi domin yafi kowa sanin Khalil tun kuruciya suke tare, tare suka taso suka yi karatu suka yi komai kuma asalima ai sunansu iri daya shima Khalid din sunanshi na gaskiya Ibrahim duk sunan mutum daya suka ci wato kakansu na wurin uba (moddibo),to dukansu sunanshi aka saka musu tunda ‘yayan wa da kani suke amma mahaifin su Khalil shine babba,
“Allah dai yana gani ai..”. Inji Khalid,shiru Khalil yayi masa yana duba agogon Rolex dinshi dake daure a hannunshi karfe biyar har da kusan rabi yana son yatura adauko Aryan amma baya son Khalid yaji babu dadi domin Aryan din na can tare da su Nawwar daga karshe dai ya zabi yin shiru zai bari zuwa magriba inyaso sai ya tura Zaid ya daukoshi.
Su Hanan kuwa sake sabon shiri suka yi suka fita kallon wasannin da ake gabatarwa acan filin fada dama kuma babu wani nisa daga nan gidan zuwa filin fadar,basu suka dawo gida ba sai dab da sallar magriba. Suna shiga gidan Zaid na dawowa shida Aryan hango Hanan da yayi da gudu ya balle murfin kofa ya fito yaje ya rungumeta,rikeshi tayi tana dariya,
“Cutie ina ka tafi yau kabarni ne da kewa?”
“Gidansu Nawwar Uncle yakaini”
“Kuma shine babu sallama cutie? Tafiya babu ko sallama?”
“A’a”
Bata sake yin magana ba tana rike da hannunshi zasu shiga part din umma ta hango abban nashi yafito da alama masallaci zaije domin gashi nan yana gyara hannun rigarshi wanda ya nannade wurin alwala,sakin Aryan tayi dalilin jiyo kiranshi da uban keyi wai yazo suje salla,ita kam kada kanta tayi zuwa ciki.
Daren yau kamar abun hadin baki dukkaninsu su biyun basu samu bacci ba kowa damuwarsa ce ta hanashi runtsawa ita Hanan tunani da begen ganin Khalil ne ya sa bacci ke neman gagarar idanuwanta,bata gajiya da kallon bawan Allahn nan bata san dalili ba koda yake Allah ne ya kamata tunda abaya babu irin fariya da cika baki da rashin kunyar da bata yimasa ba shiyasa akace kar ka raina mutum ko kuma ka wulakantashi musamman ma wanda baka sani ba ko baka taba ganiba dan Allah na iya jarrabarka da kaunarshi bayan kun hadu,duk da ita dai har yau bata gama tabbatarwa da kanta cewa ta kamu da sonshi ba amma ta damu dashi tunanin sa ya sako ta agaba ta yadda bata yin kwakkwaran minti daya ba tare da ta tuna dashi ba to wai meke damunta ne?.
Shi kuma Khalil maganganun da Khalid ya farfada masa sune suka nemi hanashi bacci wai harda cewa yana zaluntar yarinyar mutane dan haka yaji tsoron Allah,