MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Juyi yayi akan luntsumemen gadonshi sannan yaja dan guntun tsaki ya harde hannuwanshi a kirji,
“Ko me yake son inyi mata oho…” Yafada acikin zuciyarshi yana sake yin wani tsakin,
“Ka bata hakkinta na aure tunda itama mutum ce…..” Maganar Khalid ta sake dawo masa tamkar yanzune yake fada masa,
“Inbata hakkinta? Kai gaskiya bazan iyaba…… Ni in rab’i wata mace wadda ba Ramlat ba? Gaskiya bazan iyaba, Ramlat ita kadai ce matar da zan iya wannan rayuwar da ita kuma tunda ta rigada ta tafi ta barni shikenan zan ci gaba da hakuri har zuwa lokacin da nima nawa wa’adin zai cika….” Ya fada yana lumshe idanuwanshi nan kwalla ta ziraro masa ta gefen idonshi,har yau yakasa mantawa da Ramlat dinsa sannan yakasa daina zubar da hawayensa aduk lokacin da ya tunota,yana yiwa Ramlat son da shi kansa bai san wanne iri bane,akan ya je ya hada jiki da wata macen wadda ba Ramlat ba gara ya zauna bukatar hakan ta zama ajalinsa dan ita kadaice daidanshi a wannan bangaren wannan shine hukuncin da ya yankewa kanshi.
Washe gari da safe da dan ciwo ciwon kai kadan kadan Hanan ta tashi sakamakon rashin samun isasshen bacci da bata yiba,tana zaune ita kadai a falon hajiya saboda su Sarah sunbi umma barira Billiri sai zuwa gobe zasu dawo yanzu gidan babu kowa daga ita sai hajiya sai Aryan sai masu aiki shi Aryan ma tun bayan da tayi masa wanka ya tafi wurin abbanshi bai dawo ba har yanzu,
Text ne taga ya shigo wayarta sai da ta dan ja lokaci sannan ta duba saboda ta zaci ko mujahid ne domin shima yanzu baya kwana biyu batare da yaturo mata da sako ba,
_Ki shirya zan fito yanzu zamuje unguwa._
Shine abinda taga Khalil yaturo mata,tashi tayi ta shiga cikin bedroom ta sake gyarawa ta kintsa sannan ta fito yau shigar shadda tayi kalar ruwan shanshanbale wadda tasha aiki dinkin riga da zanine yayi kyau sosai,sarka da dan kunne da abun hannu ta sassaka sannan tayi dauri wanda yadace da zamani kuma dan yayi da ka ganta dai kaga amarya wacce ludayinta ke kan dawu. Tana zaune bakin gado tana yiwa yaran anty salaha voice note ta WhatsApp tajiyo kamshin turaren shi yana gabato ta,
Bude kofar dakin yayi bayan ya danyi knocking sau biyu bai jira tabashi izini ba kuma yabude ya sako kanshi ciki aranta tace to me amfanin knocking din tunda bai jira izini ba?
“Fito mu wuce….”
Daga haka yajuya yana gyara zaman hular dake kansa, hajiya suka yiwa sallama sannan suka fita da ita dashi da Aryan hajiya sai faman fara’a take yi,yau dama kaya yan kanti ta sakawa Aryan yan ubansu jeans da t shirt jeans din baki da belt dinshi sai brown colour din riga t shirt wadda ajiki aka rubuta 123,sai bakin combos sabo dal,shi kuwa uban farar shadda ce ajikinsa zubin dinkin birni yasha hula sai zuba kamshi yake yi,dukkaninsu baya suka shiga shi kuma Aryan ya shiga gaba yana mikewa tsaye saman kujerar,
Gidan Abba Idris suka fara zuwa wanda ke can sabuwar GRA,gidan babban gidane mai dauke da sassa daban daban, bangaren uwar gidan suka fara zuwa wacce ta karbi Hanan hannu bibbiyu da yake mace ce mai fara’a,shi kuma dama uban gayyar yana can wurin Abban suna gaisawa,bayan tafito daga sashen uwar gidan aka rakata na amaryar itama ba laifi tana da karbar baki,tana zaune ita da Aryan da wasu yara agidan wanda tafi kyautata zaton jikokin gidanne dan harda wadda bata d’ara Aryan a shekaru ba aka leko kiranta wai tafito su tafi,kudi matan gidan suka bata da turaruka,har falon Abba kuma aka rakata suka gaisa shima yabawa Aryan kudi wai gashi nan barka da salla shima khalil rabon kudin yayi agidan kowa da nasa sannan suka tafi,gidan anty Fatu kanwar hajiya suka je wannan kam har falonta Khalil yashiga suka gaisa itama yayiwa yaranta rabon kudi sannan suka fito, Hanan ta lura shi mutum ne mai son zumunci da kaunar yan uwansa domin duka kannensa babu gidan wanda basu jeba yakai mata ziyara, ba dan mai zumunci bane ai hakimcewa zaiyi sai dai shi aje asameshi tunda shine babba kuma yana da kudi amma babu ruwansa yakanje ya gaidasu lokaci zuwa lokaci kuma duk sallar duniya karama ko babba indai yana k’asar sai yaje gidajensu yayi musu barka da salla haka idan anyiwa su Aryan hutu shima kaf dangi sai ya zagaya dashi anganshi sannan yake barin k’asar dashi gaskiya ya rike yan uwanshi kuma ya rike girmansa ya zame musu babban wa uba.
Gidan mai martaba suka je wato fada bayan sun fito daga gidan hamida kanwarshi, Hanan aranta tambayar kanta take tayi to ko dai duk cikin gombe yan uwansu Khalil ne? Saboda sunje gidaje sunfi 20 idan lissafawa zata yi,lallai sai yanzu ta yarda da maganar da taji marokin nan nayi ranar daurin aurenta yanata yiwa Khalil kirari wai ya gaji mulki kuma yagaji sarauta ashe kuwa dagaske hakanne dan tagama kamar gaba daya masu arzikin garin danginsu ne,
Bayan fitowarsu daga fada inda aka hado ta da kayan kamshi kaya guda su turaren wuta,turaren kaya,ban daki da na jiki gidan Khalid suka wuce ta fahimci hakanne dalilin waya da taji yana yi da Khalid din yana cewa gasu nan zuwa,
Acan suka yi sallar magriba duk da Muneerat matarshi bata da saurin sabo amma hakan bai damu hanan ba tayi mata uzuri saboda kowa da irin halinshi. Sai da suka ci abinci sannan suka fito domin tafiya,a compound din gidan suka tarar da su Khalil tsaye shida Khalid suna yin magana amma basu san kowacce iri bace saboda basa jiyo abinda suke fada, sallama sukayi musu suka tafi su Nawwar nata yiwa Aryan bye bye wai suma sai sunzo. Tunda suka koma gida hanan tashiga daki ta kwanta ga gajiyar yawon da suka sha ga ciwon mara saboda tsallaken watan da tayi bata yiba shiyasa take dandana kudarta,tana cikin wannan halin taga text din Khalil wai ta shirya gobe zasu koma Abuja,kasa tashi ta shirya kayan tayi ahaka su zarah suka dawo suka sameta wad’anda suka dawo daga Billiri tare da umma barira………………………鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:11 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*28*
***Tana daga kwancen tana fama da ciwon mara wanda ke nukurkusar ta su zarah suka shigo ita da mufida kowaccensu da alamun gajiya atare da ita,
Cikin wannan hali ta janyo wayarta tana sake duba sakon nashi wanda yarubuto mata,
_ki shirya kayanki gobe da safe zamu wuce Abuja._
“Anty mun dawo…” Mufida ta fada tana kokarin zama gefen gadon nata batayi magana ba sakamakon yawu da ya tarar mata abaki,tashi tayi taje ta zubar ta dawo ta kwanta,
Wasa wasa tashin zuciya ya sako ta agaba ga shegen rashin dadin baki dake damunta kamar wata mai ciki haka yawu zai yita cika mata baki dayake wani lokacin period yana da wannan tsiyar duk sai yamayar dakai mai laulayin dole,zuwa bayan ishah har ta galabaita dan sai da lamarin ya kaita da yin amai,amai tayita kwarawa kuma tana gamawa cikin ta shima ya rude ta sake komawa cikin toilet din ai tuni su mufida suka tafi suka kaiwa hajiya tsegumin ai ga Anty can tana ta amai bata da lafiya,hajiya tare da umma ai da hanzarinsu suka taho kamar zasu tashi sama,