MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Tana kwance ta sauya kayan jikinta sakamakon wanda ke jikin nata sun baci da aman da tayi,cikin rudu hajiya da umma keyi mata sannu tana daga musu kai tana kokarin yin magana wani aman yasake turnuko mata cikin sauri ta tashi ta nufi toilet taje ta yi acan,
Fita hajiya tayi ta kira Khalil awaya lokacin shi yana can ma tare da baki suna ganawa,
“Mu’azzam kabar duk abinda kake yi maza kazo matarka babu lafiya amma ka fara kiran likita tukunna….”
Abinda yaji hajiya tace kenan sannan ta katse wayar, Zaid ya kira yace yaje ya dauko Dr,
Hanan na kwance saman gado tana ta karkarwar sanyi suka shigo shida Dr din kowa fita yayi yabasu wuri,yana gaba Dr yana biye dashi abaya,ajiye dan first aid box dinsa yayi likitan yana dan yimata tambayoyi,
“Akwai juna biyu ne?”
Girgiza kai tayi idanuwanta arufe,
“When last kika ga al’adarki?”
“Last month banyi ba” Tabashi amsa cikeda kunya saboda Khalil dake tsaye kyam yana sauraren su,
“Dama kina tsallaken wata ne?”
Girgiza masa kai tayi kuma cikin yamutsa fuska tace “A’a”
“Akwai amai?” Kai ta daga masa,
“Akwai ciwon kai?” Girgiza kai tayi alamar babu,
Dafa wuyanta yayi yaji akwai zazzabi sannan ya dan dudduba idanuwanta bayan ya dan bubbudesu. Magani ya soma duba mata yana cigaba da bayanin cewa ai ba wata matsala bace dama dayawan mata sukan samu irin wannan laulaye laulayen lokacin da zasu yi period, Khalil na tsaye yana daddana wayarshi kamar baya jinsu,ganin hankalinsa yana kan waya yasata dan bude idanuwanta ta kalleshi sannan ta mayar dasu ta rufe,saida yagama hada maganin tsaf sannan ya bata yace taci abinci komai kankantarshi sai ta sha magani daga haka suka fita shi Khalil bai ce komai ba,afalo ya tarar dasu hajiya dukkaninsu zaune suna jiran fitowarsu cewa yayi bari ya sallami Dr yadawo,baifi minti biyar da fita ba sai gashi yadawo amma bai samensu ba sai acikin bedroom din da take ciki ya iskesu anata lallabata ana tambayar wai me take son ci akawo mata? Tsayawa yayi ya harde hannuwanshi akirjinsa yana kallon ikon Allah domin su duk atunaninsu juna biyu Hanan tasamu wai dan sunga tana amai basu san lalurar su ce ta mata ba duk wata,
“Ki daure kici wani abu kinji…. Kinga ai yanzu dole sai kin kula,me za akawo miki?” Hajiya ta bukata cikin kulawa,
“Custard powder kadai zan sha itama kar asa sugar…..” Ta fada cikin rashin kwarin jiki,
“Ke zarah maza tashi kuje ku hado mata custard…” Inji umma barira,
Shi abinma sai yaso bashi dariya saboda yanda duk su hajiya suka bi suka rude sunata lallabata,sai da tasha custard din tasha magani sannan suka fita suka barta,
Shima yana shirin fita hajiya tazo ta dakatar dashi,
“Khalil nace yaushe matar taka tafara wannan laulayin ne? Idan tana yawan yin aman ai sai insa asamo mata magani,kasan masu juna biyu sai da kula”
“Toh hajiya”
Daga haka yasamu tabarshi yafita,kulawa sosai ake bawa Hanan dan da safe ma kafin su tafi hajiya nata jawa Khalil kunnen yarinka kulawa da Hanan,da tafiyar ma hajiya cewa tayi sai abari wai har Hanan din ta warware sai da Hanan din tace mata ai itama akwai abinda zatayi idan taje Abujan zatayi clearance to jin haka yasa hajiya amincewa suka kama hanya suka tafi tana sake jaddada wai arinka kulawa da Hanan shi dai bai ce ba juna biyun bane yai shiru yana binsu da ido.
Duk da cewa bata baccin mota yau kam ta yi shi dan tunda suka baro gombe take tikar bacci har lokacin da suka shiga garin Abuja lokacin anata sheka uban ruwa dan tun daga farkon abuja ake zubashi,
Har suka shiga cikin compound din gidan Hanan bata saniba domin tana can tana ta sharar baccinta,sai da Aryan ya bude murya yace,
“Mommy ki tashi anzo gida…”
Firgigit tayi ta mike domin kamar acikin mafarki taji maganar tashi,a dan tsorace ta juya ta kalli Khalil wanda ke zaune kusa da ita,tashi tayi tafita ta nufi ciki tana dan dingishi tana zuwa bedroom dinta ta rage kayan jikinta ta sake kwanciya domin a mutukar gajiye jikinta yake tamkar anyi mata dukan tsiya. Ta jima tana bacci dan sai la’asar sannan ta tashi tayi wanka ta fita wurinsu umma da ke babban falon kasa ita da Aryan wanda ke ta wasa da keken sa,itama zama tayi bayan ta zubo abinci dama aikin kenan daga ci sai bacci bayan shi babu abun yi.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya su Aryan tuni sun koma makaranta shi kuma Khalil yakoma kan harkokinsa shima dan ko ganuwa ma bayayi kullum da inda zaije,
Hanan kuwa tun bata damuwa rashin daidaituwar dake tsakaninta da Khalil har tafara damuwa,bata da aiki sai na tunaninsa da mafarke mafarke akansa gaba daya ta rame ta kanjale gata dai a katon gida lafiyayye zata ci zata sha ba aikin komai take yiba amma da yake akwai damuwa acikin zuciyarta shiyasa duk ta zuke dan ko ganinsa ma bata yi tsakaninta dashi text massage ne idan tana son wani abu ko kuma tana son zataje wani wuri kuma duk abinda ta nema ko ta bukata baya hanata yana sawa a kawo mata,
Shima anasa b’angaren har gobe bai daina kukan rashin matarsa ba domin halin da yake ciki yafara damunsa ada yayi tunanin zai iya rike bukatarsa ba tare da shiga wani hali ba amma yanzu ya ga abun yana neman faskara domin kullum cikin shan pills yake wai ko zaiji dama dama gashi yana yin azumin litinin da alhamis amma duk jiya iyau,
Hajiyarshi kuwa duk lokacin da yaje gombe cikin tambayar sa yajikin Hanan take yana dai kulawa da ita ko? Wannan zuwan da yayi last kuwa hajiya harda bashi sassake sassake na gargajiya wai maganin laulayine na masu ciki yana tsayar da amai da sauran su shidai baice komai ba ya karbo yataho dashi da yazo sai yabawa umma saboda su Hanan basa nan suna makaranta ita da Aryan,
“Umma gashi wai maganin Sa’adatu ne idan ta dawo sai kibata…..”
“Na menene?” Umma ta tambayeshi,
“Maganin laulayine wai inji hajiya….”
“Au toh toh, Allah yasa adace Allah sarki dama ai yarinyar nan duk ta zuke ta lalace wallahi cikin nan na wahalar da ita… Allah dai yaraba lafiya”
“Amin” ya amsa daga nan yafita,
Bayan su Hanan sun dawo tana falo tana tsara lesson plan dinta umma tazo ta kawo mata maganin da Khalil yakawo karba kawai tayi tace ta gode,kwalla taji ta ciko mata ido sakamakon damuwar dake ranta gashi kullum mujahid cikin turo mata da massage yake amma tayi biris dashi bata kulawa wallahi kallo daya idan kayi mata zaka fahimci tana da damuwa,sau da dama sai taji kamar ta tura masa da text massage ta fada masa sirrin zuciyarta amma sai taga rashin dacewar hakan,idan tayi haka ta disga kanta kuma bata siyawa kanta daraja ba.
Yau dai tana cikin farin ciki saboda zuwan anty salaha yayarta dan rabonta da ita tun bikinta yau watanni shida kenan kuma wata tara da fara service dinta dan saura yan watanni su gama,
Binta da kallo kawai anty salaha keyi saboda yanda taga ta rame tayi kanjal kanjal da ita kamar ba itace cikin wannan daular ba,
“Gaskiya Hanan banji dadin ganinki ba haka, wannan uwar ramar da kikayi duk ta mecece? Baki rasa ciba baki rasa sha ba meyake damunki?”
Dan jimm tayi dan ta rasa me zata cewa anty salaha,ada tana ta kukan bata son minister bata kaunar shi ayanzu kuma kukan tsananin sonshi da kaunar shi take duk da shi nasa hankalin ba akanta yake ba ko ganinsa yanzu bata samun yi,sai tayi sati daya ko fiye da haka bata ganshi ba,da yake bata da abin fada haka taja bakinta tayi shiru tana sauraren fadan da anty salaha keta faman yimata tana cewa yadace dai yanzu ace ta kwantar da hankalinta ta yi zamanta agidan mijinta tunda ita anty salaha bata san abinda ke cikin ranta ba. Kwanan anty salaha biyu sannan ta tafi kuma ko haduwa basuyi da Khalil ba dan baya nan sai kudi da ya aiko PA dashi ya kawowa Hanan dan tayi masa massage cewa anty salaha tazo.