MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

“To Allah ya kiyaye hanya yabada sa’a,sai ka dawo”

“Amin umma,mutumin yatafi makaranta ko?”

“Tun dazu ai yajima acan,yatafi yana ta rikicin wai sai anhada masa harda wannan lemon madarar da ka hana abashi cikin lunch box dinsa”

“Kar arinka bashi umma saboda rana wallahi”

“Ehh ai shiyasa ban bashi ba nadai lallabashi nabashi dayan”

Fita yayi yatafi abinshi bai ko nemi inda matar gidan takeba kai to ai shi da zaka saka wuyansa gaba gabas bazaice maka ga kalar amaryar nan ba, ita kuwa umma har yau bata san ba agidan yake kwana ba duk d’aukarta agidan yake.

Hanan sai wurin karfe 11 sannan tafito bayan tayi wanka ta shirya cikin wani jan swiss material dinkin doguwar riga,umma ta iske tana falo tana sak’a muficin roba da alama jiya ta taho da kayan yin,

Tea ta hado ta dawo wurin umman ta zauna suna hira,

“Ashe maigidan kaduna zaije ko? Ai kullum baya rabo da tafiye tafiye,ayi mutum kullum da inda zaije bashida ranar hutu? Wannan aiki nasu da wahala yake”

Jin abinda umma tace yasa Hanan fuskarta akan baban Aryan umman ke magana, murmushin yake tayi amma bata nuna cewa bata saniba,

“Wai nikam umma meyasa auren da yafi na yanzu kwanciyar hankali ne dan Allah? Auren yanzu da yawa wallahi ana dai zaune ne kawai amma bawai dan ana jin dadinsa ba”, ita kanta bata san lokacin da tayiwa umma wannan tambayar ba kawai dai kun san abinda ke ran mutum wani lokacin sai ya amayar dashi yake jin dadi,

“To ai mu ada kinga akwai biyayya mijin ma ba saninsa kayiba shima bai sanka ba iyayene zasu hada kuma baka isa kace kai bahaka ba koda kuwa kana da naka zabin haka zaka hakura ka karbi nasu,ka isama kace kai ga wanda kake so? Ai idan kayi haka kayi rashin kunya,haka zaka yi hakuri kuma sai kiga nasu zabin yafi nakan”

“Amma dan Allah umma ya kuke ji idan akayi muku auren dolen nan lokacin”

“Wallahi bama jin komai ‘yarnan tunda dama abune da aka riga aka saba sannan kin san mutanen da akwai biyayya ba irin na yanzu bane,dan ni kinga lokacin da aka kaini daki wallahi ban taba ganin mijinba sai lokacin shima haka kuma haka muka zauna acan muka saba muka so juna har lokacin da mutuwa ta raba,amma ku yanzu mazajen da kuke so din kuke aura amma babu zaman lafiya,mu hadamu akeyi hadin iyaye amma Sai mu zauna lafiya ba fada ba yaji bare aje garin saki da yawa mutuwa ce ke rabawa amma ku yanzu aure wata biyu wata uku sai afara yaji ko ma auren yamutu gaba daya,mu ada bamu san wannan ba,miji yana girmamaki yana girmama iyayenki kema kuma haka sannan kina yimasa biyayya babu reni amma yanzu ku auren ma yazama na zamani…”

Sosai yau Hanan suka sha hira da umma wacce ke zaune tana ta sak’ar muficinta to babu abinyi idan kuma kafiya kwanciya jikinka sai yayi ciwo.  Har lokacin da Aryan yadawo suna tare umma nata bata labarin auren da, Aryan baiko nufeta ba umma yanufa dama da ita yasaba shima kuma yaro yasan mai yimasa inda ake kaffa kaffa dashi yake zuwa shiyasa Aryan baya ko rabarta.

Aranar da yamma su Khadija suka yimata waya wai zasu zo tabasu address din gidan,itama saida ta dan tambaya sannan ta tura musu,tana falo ita da umma shikuma Aryan yana can ana koya masa karatu wani mopol yashigo falon da kayansa na aiki ya tsuke harda bindiga rataye ajikinsa,

Dan russunawa yayi sannan yace “madam kina da baki kin san da zuwansu?”

Ita wallahi sai yau tasan dan zakayi bako sai ka sanarwa securities,mantawa ma take yi da agidan da take nan dai tace masa ehh tasan da zuwansu,fita yayi yaje yashigo dasu sannan yajuya yasake fita,

Mamaki ne yaso kashe su hajara saboda ganin irin aljannar duniyar da Hanan ke ciki haba ai ko haka Allah yabarka sai ka gode masa domin ya daga darajar ka,gaisawa sukayi da umma daga nan takaisu sama falonta ai sai suka sake zama kauyawa sunata yimata murna ita kuwa sai tabe baki take yi bayan tagama cika musu gabansu da kayan ciye ciye da abinci da fruits da juice kala kala,

Ita haushi ma take ji yanda suke ta ikirarin wai tayi sa’a tayi dace,ita da ta auri tsoho komai kudinsa wallahi gara ta auri yaro sun mutu cikin talauci, dariya hajara tayi tace,

“Lallai yarinya baki san talauci ba,wallahi yau da gobe tafi karfin wasa,ai inda kudi bacin ranki kadanne koda bakya sonshi amma komai son da kake yiwa mutum mutukar akwai babu tofa babu zaman lafiya wallahi talauci shi yafi komai hana aure ya zauna lafiya”

“Ki kyaleta hajara,ke nidai ki taimaka min ki hadani da wani acikin abokanshi nima infaso….” Khadija tafada tana kashe ido daya dan ita har zuciyarta dagaske take ita kuwa Hanan wallahi duk haushi suke bata haba me za ayi da auren tsoho ai wallahi akwai matsala yanzu ko abune yatashi na friends kowacce zataje da dan mijinta yaro mai jini ajika kai sai aganka da tsoho? Tsohonma wai abokin babanka,ai ita dai wannan minister ya cuceta wallahi,

Duk maganganun da su hajara keyi ta bayan kunnenta yake shiga har suka gama suka tafi bayan ta cika musu leda da kayan kwalliya,ita dai yanzu alla alla take takoma school taci gaba da zuwa PPA dinta ko ta samu abinyi……………………鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:08 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*18*

       ***Haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum Hanan cikin kunci take sam bata jin dadin zaman gidan minister amma na waje koda yaushe cikin tayata murna suke ana cewa tayi sa’a kuma tayi dacen gidan miji, duk da suna zaune da umma lafiya kuma cikin mutunta juna amma wani sa’ilin ji take yi kamar ta dora hannu aka ta fasa ihu dan tsabar takaici,saida hutunta yakare ta soma zuwa school sannan ta dan fara samun nutsuwa domin kullum idan ta fita bata dawowa sai 2 na rana duk ta zama busy bata samun zama sai weekend Aryan kuwa tare suke tafiya school dashi kullum amma babu ruwanta dashi sam bata sakar masa fuska bare ya kawo mata wargi,

A bangaren oga Khalil shi dinma hakan take domin har yau bai san ko kalar Matar da ya aura ba dama kuma shi ba mazauni bane kullum yana da inda zaije baya shigowa gidan sai dare darenma ba na kusa ba da yazo zaiga Aryan shikenan sai yayi tafiyarsa yakoma tsohon gida amma bai taba kwana a wannan sabon gidan ba umma kuwa yakan zo wani time din da sassafe ya gaishe da ita sannan yawuce bai taba neman hanan ba kuma bazai taba nemanta ba domin bashida matsala da ita shi yanzu matsalar shi ciwon cikin da ke neman zame masa karfen kafa domin kusan kullum cikinsa yake kuma gashi yasha magani yasha magani har yagoda Allah.

Hanan har yau bata ji son mujahid yaragu daga cikin zuciyarta ba kusan kullum sai tayi masa text massage amma baya yimata reply ita kuma kamar yanda kasan asiri yayi mata haka ta makale masa.

***

  Mujahid

Dauriya kawai yake yi amma tun ranar da Hanan ta sanar dashi maganar bikinta hankalinsa yayi masifar tashi domin akanta yafara yin soyayya kuma ita yake so bai taba son wata mace ba sai ita,bacci wannan baya iyawa yanda ya kamata,

Yana zaune cikin falon mami mahaifiyar shi ya rafka uban tagumi yasaka abinci agaba amma tsabar damuwa ya kasa ci ahaka mamin tazo ta iskeshi idanuwanshi jajur yakasa cin abinci sai faman tunani yake yi,zama mami tayi ta dafashi tana son jin damuwarsa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button