MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

“Mujahid meke damunka ne? Kwana biyun nan duk baka da kuzari lafiya kuwa?”

“Babu komai mami….”

Ya fada yana kokarin hadiye kwallar dake kokarin sauko masa,

“A’a wanne irin babu komai bayan gashi nan ina ganin damuwa baro baro atare dakai,ka fada min abinda ke damunka,idan baka fada minba wa zaka fadawa?”

Tallafe kumatunsa yayi da hannuwanshi guda biyu,

“Mami Hanan din da nake baki labarinta itace aka yi mata aure…..”

“Aure? Aure fa kace, yaushe?”

” tun sati biyu da suka wuce nikuma wallahi narasa yadda zanyi indaina sonta”

Shiru mami tayi tana nazari amma tunda yafada mata cewa wai anyiwa Hanan aure tasamu kanta cikin bacin rai domin mujahid din yana tsananin son wannan yarinyar amma shine zata yaudarar mata yaro tasashi cikin matsala da damuwa alhalin ita kuma tana can tana more tata rayuwar,

Shafa kansa tayi acikin ranta tana tunanin abinda yadace tayi domin bazata taba zura idanu tilon danta yashiga cikin matsala ba akan wata,

“Dauki abincin kaci mujahid….. Insha Allah sai Allah yayi maka sakayya,dauki kaci…”

Ba dan yana so ba haka yadauki abincin yafara ci sai dai ko lauma uku kwakkwara baiyi ba yaji wani azababben amai yana taso masa babu shiri yabar abincin yatashi yanufi bedroom din mami yashiga toilet dinta yasoma yunkurin yin amai wanda ke fitowa dakyar harda jini jini,ai hankalin mami wacce ke biye dashi idan yayi dubu saida ya tashi babu shiri ta kira driver suka tafi asibiti mujahid rai a hannun Allah,

Saida yashafe fiye da sati daya a asibitin yana samun kulawa daga ma’aikatan jinya sannan yafara samun lafiya,kullum yana ganin kiran Hanan da sakonninta amma baya bi ta kai saboda yanzu matar aure take bai kamata yarinka kulata ba amma shima kawai danne tashi zuciyar yayi bawai dan yadaina jinta acikin ranshi ba.

***

 Zaman Hanan agidan minister har yau jiya iyau domin babu wani sauyi sannan bata taba ganinsa ba shima haka shi dai Khalil akwai ranar da yashigo da sassafe ita kuma ranar zata fita CDS tana sanye da uniform ya hango shigarta mota shikuma yana cikin motarshi mai dauke da bakaken gilasai yana kishingide a owners corner kamar koda yaushe,suna yin parking ita kuma motarsu na fita daga cikin gidan dama yanzu anware musu motarsu ita da Aryan mutumin nata wanda har yau baya ganin dariyarta kullum cikin cimasa magani take shiyasa yake bala’in jin tsoronta wanda har yau babanshi bai saniba dan da ace yasani da tuni yajima da daukar matakin da yadace.

Kasancewar tana jin haushin uban shiyasa shima dan take jin haushinsa ga shegen surutu da shagwaba awurin wannan yaron amma uban baya gani bini bini zaka ji yakira dan awaya yana tambayar sa ko akwai wani abu? Ita kanta wayar Aryan din ta dubunnan kudice kuma ba uwar komai yake yi da itaba sai game sai waya da uban ita dai wallahi tana jin haushin wannan abu amma tunda ba danta bane ido ne nata,gashi da yadawo daga makaranta zai shiga dakin da kayan wasanshi suke a kasa yayi kaca kaca dasu yahau na hawa ya bata na batawa.

Yau kam ta kama weekend tunda asuba Khalil yatafi gombe zai halarci wani daurin aure da yaso yatafi da Aryan to kuma yasan time din bai tashi daga barci ba,

Hanan kuwa tun da tatashi ranta abace yake saboda weekend ne yanzu zata yita zaman wuri daya daga nan har monday,gashi tunda tazo garin nan batayi kitso ba kanta atsefe tagaji dashi kuma ahaka,text massage ta turawa minister akan tana son fita kitso,shi kam da yake yana can gombe kuma tare da mutane bai ko samu zarafin duba wayar ba saboda jama’ar da yake tare dasu daga wadannan sun fita wadannan zasu shigo kuma duk lokacin da yaje gombe hakane,zakayi mamakin irin mutanen dake tururuwar zuwa wurinshi duk ranar da yaje garin.

Shirun da Hanan taji yayi mata sai tasake kufula ta tunzura dama ta jima da yimasa zargin girman kai wato yanada wulakanci da girman kai anata tunanin dan ko massage sai ya gadama yake amsawa,shiyasa a kule ta wuni ranar da rana ma saida yunwa ta ciyota tazama weak sannan ta sauko kasa Aryan na zaune falon yabaza kayan wasa baja baja yanata wasanshi umma kuma na bedroom tana dan taba baccin kalula,

Kan dining Hanan ta hau ta zuba alalan kwai mai dauke da kayan lambu da sos tana ci,

Aryan ne yacika falon da wata irin kara sakamakon bindigar wasanshi da ya kunna kai sai ka rantse karar bindigar gaske ne nan yacikawa Hanan kunne da kara ita kuma dama a kule take,

“Kai……kashe karar nan” Ta fada cikin fada amma bai kasheba saboda shi bai jita ba sau kusan uku tana yimasa magana amma bai jiba ita kuma ta zaci yana jinta ya kyaleta dan haka ta tashi afusace ta nufe shi tana zuwa ta daka masa wata gigitacciyar tsawa da ba ataba yimasa irinta ba,

“Kai…… Kashe wannan abun naka duk kabi ka wani cikawa mutane kunne shashasha kawai….”

Dama Aryan tsoronta yake hakan da tayi masa sai yasake tsorata da sauri ya kashe jikinsa na rawa,

“Bar nan….fice daga nan”

Tashi yayi da sauri garin yabar wurin yataka wani abu daga cikin kayan wasan nasa santsin tiles yajashi suuu yatafi ya fadi kansa ya bugu da kujera ji kake gummm shikenan ya fadi awurin babu numfashi………………..鉁嶏笍

_*Ummi Shatu*_馃憣馃徎

8/14/20, 10:08 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*20*

     ***Da hasken wayarshi ta hannu yayi amfani wacce ke cikin aljihun gaban rigarsa,caan ya hangosu kwance saman gado sunyi kai da kafa,sake lumshe idanuwanshi yayi sannan yasoma takawa ahankali har ya isa gaban gadon,kamshin dakin nata sai yaji ya banbanta da irin wanda falon nata keyi, bai tsaya kallonta ba yayi abinda yakaishi kawai wato kallon sha lelensa Aryan,ita kam gaba daya lullube take da duvet tun daga kafafuwanta har zuwa kanta dan haka babu abinda zaka iya gani atare da ita sabanin Aryan da dama tun can asali baya son a lullubeshi idan yana bacci sai ko idan baccin nasa yayi nisa,

Shafa fuskar Aryan din yayi sannan yayi kissing dinsa a goshinsa shima ya lullubeshi, ahankali yajuya yafita daga cikin bedroom din amma can kasan ranshi wani dadi ne ke ziyartarsa ganin irin kulawar da Hanan ke bawa Aryan, Allah sarki ashe ya dauki hakkin yarinyar ne da har ada yafara zargin ko itace ke takurawa dan gaban goshin nasa,ashe ba haka bane ita tayashi ma sonshi takeyi,

Zuciyarshi fes yabar gidan yanufi tsohon gidansa inda karfi da yaji can yake rayuwarsa shi daya,wanka yafara yi sannan yahada coffee yasha duk jikinsa jinsa yake yi yana yimasa ciwo kamar wanda ya wuni yana yin aikin karfi, shiyasa ma yau bai samu zarafin yin tsaiwar dare ba kawai dai ya zauna ya karanta abinda ya sawwaka cikin littafi mai tsarki daga nan yayi alwala ya kwanta.

Su Hanan kuwa babu wanda acikinsu yasan cewa wai Khalil yazo gidan sai da suka fito da safe sannan suka ga tsarabar da yakawo musu adaren jiya wato fura da nono sai fruits kala kala harda apple mango irin manya manyan mangoes dinnan, ita umma barira har yau bata san cewa ba agidan yake rayuwarsa ba kuma bata san akwai wata akasa tsakaninsa da Hanan ba da za ta tsawatar musu kuma ta dauki mataki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button