MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Yau ita dai hanan da farin ciki ta tashi,ruwan wanka ta hadawa Aryan sannan ta d’aukeshi duk da bai tashi ba ta nufi cikin toilet dashi tana sakashi cikin bahon wanka mai dauke da ruwan dumi ya bude manyan idanuwanshi irin na ubanshi domin babu ta inda yabar babanshi a kamanni,
“Mommy…..”
“Good morning cutie”
Kwantar da kanshi yayi acikin ruwan nan tayi saurin rikeshi tana dariya, ahaka tayi masa wankan suka fita, direct dakinshi ta wuce dashi domin shiryashi, saida tafara jona masa wayarshi a jikin charge sannan ta zauna ta shafa masa mai ta fesa masa turare sannan ta saka masa uniform, ahankali take taje masa kanshi wanda ke mutukar bata sha’awa, ohh duniya kenan Allah baya barin wani dan wani yanzu gashi shi Aryan uwar ta tafi ta barshi bai ko santa ba shiyasa bahaushe ke cewa da na kowa ne saboda sai ka haifeshi amma baka mora ba wanda zai mora daban,insha Allah tayiwa kanta alkawarin kula da rayuwar Aryan ko dan lalurar dake tattare dashi kuma insha Allah zata soshi zata kula dashi fiyeda yanda zata kula da dan cikinta,
K’asa suka sauka ta bashi breakfast yana ci sai lokacin umma barira tafito ganinsu cikin shiri suna karyawa yasata yin murmushin jin dadi sannan cikin farin ciki tace,
“A’a d’a da uwa har anshirya ne anfito?”
“Wallahi kuwa umma ai idan muka zauna sanya sai mu makara azo ana tare mu”
“Ahh gaskiya kam,kai dan albarka yau babu magana? Zanfa daina mijin dakai”
“Ai sai muma mu samo wata umma”
Dariya sukayi dukkaninsu cike da raha suka rabo bayan Aryan ya gaisa da abbanshi wanda ke can gida kwance har lokacin bai fita ba saboda gajiyar daren jiya bata sakeshi ba har yanzu shiyasa bai bar gida ba yau sai 10.
***
Mujahid yajima yana jinyar son Hanan acikin zuciyarsa,kullum baida aiki sai dai ya tisa hotonta agaba yana kallo duk yabi ya susuce yafita hayyacinsa,ada ya zaci zai iya daurewa ashe abin ba haka yake ba sai yanzu yagane gaskiyar son da yake yimata,
Kullum idan yaga sakonta sai yaji kamar ya mayar mata da amsa domin yanda take ji shima fa hakan yake ji acikin ransa koma fiye da haka,nan dai zuciya ta soma zugashi akan kawai ya fara kula Hanan suje suyi rayuwarsu, gashi akwai yar uwarsa mai sonshi sumayya amma shi hankalinsa baya kanta yana kan Hanan kuma tajima tana sonshi tun yana jami’a agidansu take kasancewar shi kadai ne awurin iyayensa shiyasa suka dauki sumayya suke rikewa,
Zaman asibitin da yayi ma tare sukayi jinyarsa da mami amma har yafara samun lafiya baya sakar mata fuska saboda shifa ba sonta yake ba,yau ma yana zaune a falonshi yana kallon hoton Hanan sumayya tabude kofa tashigo tana sanye da Arabian gown maroon colour,sake hade rai yayi kamar yaga mutuwarsa domin aduniya yaki jinin wannan yarinyar sumayya,
Kayan breakfast din dake hannunta ta ajiye masa tana sussunkuyar da kai alamun kunya,
“Yaya mujahid ga breakfast dinka inji mami….. sannan tace….tace wai ka daure ka kaini school…”
Idan kujerar da yake kai ta amsa to shima ya amsa mata,tafi minti biyar atsaye awurin baice mata uffan ba daga karshe yaja wani dogon tsaki yawuce cikin bedroom dinshi batare da ya ko kalleta ba,jagwab ta tafi ta zauna bisa kujerar da yatashi tana dafe kanta wanda yafara sara mata wasu hawaye ne suka shiga kai komo akan kuncinta wanda ko tantama babu na bakin cikine,inama tana iyawa da ta cire son ya mujahid daga cikin zuciyarta amma tasan hakan bamai yuyuwa bane tunda ba ita ta dorawa kanta ba.
***
Lokaci kankani shakuwa da soyayya mai tsanani ta shiga zukatan Hanan da Aryan,yanzu yaron yasaba da ita sosai kuma yana sakewa da ita kamar umma, dukkan al’amuransa wadanda ada umma ce keyi masa ayanzu Hanan ce ke yimasa,itace wankansa, shiryashi zuwa makaranta,yanke masa farce itace ke bashi abinci abaki yanzu komai ita keyi masa kuma har cikin zuciyarta yanzu tana son Aryan kamar zata lasheshi dan so,shima Aryan din yanzu ya shaku da ita komai ita yake nufa,
A yanzu kam tana jin dadin zaman gidan fiye da farkon zuwanta dama gidane babban gida babu abinda babu na fannin more rayuwa babu ce kawai babu agidan amma komai da kasani akwaishi ga swimming pool,ga wani daki mai dauke da kayan motsa jiki ga library babba mai dauke da littattafai iri iri, can ta kofar baya kuma idan kabi akwai hadadden garden dan debe kewa mai dauke da tsintsaye aciki ga Giggs da dawisu dake sake kawata wurin,agaskiya gidan akwai abubuwan dauke kewa da kadaici sai dai har lokacin tana kewar gida dan duk bayan kwana bibbiyu take kiran mamaye da Abba su gaisa shi kuwa yaya shamsu kusan kullum suna hade ta online.
Har tsawon wannan lokacin Khalil da Hanan basu taba ganin juna ba saboda shi baya shigowa gidan sai sunyi bacci kuma idan yaje ma iyakarshi dakin Aryan da yaje yaganshi zai tafi idan kuma awayane tashi hanan take yi tabar wurin amma tsakaninta da Aryan yanzu akwai kauna mai girman gaske dan har shi Khalil din yafara fuskantar hakan saboda komai sai yaji Aryan yace mommy ce tayi masa idan abu yaci sai yace itace tabashi yaci,tsakaninsa da ita sai dai yaji sunanta abakin Aryan amma ko awaya bai taba jin muryar taba itama haka shi kuma dama ba mazauni ba yau yana wancan gari gobe yana waccan k’asa.
Tana kwance a d’akinta bayan ta idar da sallar la’asar tana karanta wani novel din turanci (Tiers of betrayal) gaba daya hankalinta yatafi ga karatun da take yi taji Aryan ya fada kanta,
Ajiye wayar tayi tana rungumoshi jikinta, “Cutie what happened?”
Kiss yayi mata agoshi sannan ya rungume ta,
“Uncle yace ba gobeba wata goben birthday dina kuma Uncle Zaid zaizo yakaimu aje ayi party…”
“Woww…..my boy zai kara girma”
Rungumeshi tayi tana tambayar shi me yafi so wanda zata bashi a matsayin gift da yake yaro akwai shirme wai sai yace cake yake so,dariya tayi tace insha Allah zata yimasa cake,
Khalil kuwa washe garin ranar yatafi kasar Italy kuma aranar da yamma sai ga Zaid yazo saboda wai shine zai kai Aryan wurin birthday dinshi idan ranar tayi,
Sai yau Hanan ta taba ganin Zaid saboda ranar bikinta bata samu damar ganinsa ba tana kunshe cikin mayafi,tunda Aryan yaga Zaid ya makale masa suna ta tafawa da yin games kamar wani abokinsa,shima Zaid yanada haske amma ba sosai can ba kana dai ganinsa kaga bufulatani,gaba daya tana ta tunanin abunda yadace ta bawa Aryan amatsayin birthday gift dinshi amma ta rasa me zata bashi daga karshe dai sai ta turawa da Khalil text message,
_Ina son zan fita zuwa super market nida Aryan_
Shine abinda yaga ta turo masa, lokacin da yaga sakon nata yana daki ya idar da salla, reply yatura mata,
_me akeyi a supermarket din? Ki kular min da yaro saboda ban fiya barinsa yana fita any how ba._
Yana gama tura mata yakira Zaid yace yakaisu supermarket din sannan dan Allah ya kula da Aryan Sosai,
Shiryawa Hanan tayi tasha bakar doguwar riga mai stones tayi rolling tafita kasa inda Aryan da Zaid ke jiranta,umma suka yiwa sallama sannan suka tafi supermarket din,duk abinda Aryan keso barinsa tayi ya dauka sai da yagama jidar abubuwan da yake so sannan taje wurin biya ta ciro ATM card dinta tabasu suka cire kudinsu ta POS,duk kayan ciye ciye da zaki Aryan ya diba dan harda su ice cream,daga can kai tsaye gida suka wuce dama Khalil sai kiran Zaid yake awaya yana tambaya yaji ko sun koma gida saboda shi duk lokacin da aka fita da Aryan hankalinsa baya kwanciya har sai yaji sun koma gida.