MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Washe gari yakama ranar birthday din aryan kuma tun safe Zaid yafita karfe 2 yakira Aryan awaya yace wai mommyn shi ta shiryashi zaizo masa da kayan da zai saka,suna bedroom dinshi bayan tayi masa wanka Zaid yashigo ya kawo masa wasu tsadaddun kaya shi ba yadi ba kuma ba shadda ba yasha dinki na musamman kalar kayan ash colour ne amma anyi masa kwalliya da baki,ga takalminsa shima baki Aryan yayi kyau kamar babu gobe,
Itama Hanan shiryawa tayi cikin doguwar riga mai shegen kyau ja tayi rolling kamar abun shiri sai kuma mararta tafara yimata wani azababben ciwo dole sai hakura tayi tace suje,
Zaid ne yadebesu a mota banda umma ita kam cewa tayi adawo lafiya,daga shi sai Aryan suka tafi excellent square garden acan ne aka shirya party din cikin wani kayataccen hall mai masifar kyau, Hall din yasha decoration tako ina ga cakes nan manya manya wurin guda hudu kowanne kalarshi daban amma ajiki anrubuta HBD Aryan,yara da manyan dake wurin kwata kwata basu fi guda goma ba nan akayi aka gama saboda Khalil yanata yiwa Zaid takarar wai karsu yarda sukai dare shiyasa ana yin magriba suka tashi bayan anyanka cake anci ansha.
Har suka dawo Hanan na kwance adaki tana fama da kanta saida taji dawowarsu ne ma sannan ta samu dan karfin fita dan ganin gifts din da aka kakkawowa Aryan wadanda ke zube afalonta Zaid yashigo dasu, gifts ne sama da guda goma ko wanne anyi raping dinshi da raping sheet mai kyalli sannan ga manya manyan cakes dinshi nan wasu an yanka wasu kuma ko tabawa ba ayiba banda sauran snacks da drinks, PA ne yazo falon kasa yakira zaid yabashi wani sungumemen gift din shima anyi raping dinshi wai inji oga wato Khalil,
Hanan na zaune da Aryan akan cinyarta suna cin cake Zaid yakawo sakon,itace tafara budewa gift din Khalil din tana cewa Aryan, “Bari mufara ganin na Daddy ko”
Da wani dan karamin greeting card tafara cin karo wanda ajiki aka rubuta,
_Hope your birthday blossoms into lots of dreams come true! May today be filled with laughter and love. Happy Birthday and many happy returns of the day._
Murmushi tayi bayan ta gama karanta masa,wani babban enlargement din hoto tagani mai dauke da hoton Aryan atsakiya yayi kyau sosai ajiki anrubuta HBD boy,sai kuma wani dan karamin akwati koda ta bude agogon diamond ne kirar carat watch sai walwali yake aciki anninke wata yar karamar farar takarda ce wadda ajiki akayi rubutu da biro kamar haka,
_I may not be celebrating your special day with you but I want you to know that I am thinking of you & wishing you a HAPPY BIRTHDAY._
_papa_
Murmushi tayi ta daura masa agogon wanda kamar angwada da hannunsa,gaskiya babansa rikakken dan boko ne jibi rubutu kamar ba hannune yayi ba sai kace injine ya rubuta,raba dare sukayi suna santin gifts din da Aryan yasamu musamman ma na wurin Dad dinshi ga kuma na sauran mutane dan wasu ma ko budesu basu yiba………………鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*19*
***Duk da cikin bacin rai take sai da hankalinta yayi mugun tashi domin gani tayi Aryan yayi wanwars baya ko motsi wanda da alama suma yayi ko kuma rai ne yayi halinsa,
Rasa ma inda zata dosa tayi waje ko ciki? Da gudu ta nufi kofar da zata sadata da waje amma sai takasa bude kofar ma da yake arude take sai kokarin budewa take amma ta kasa,kamar daga sama Allah ya kawo mata security guda daya wanda yanufo cikin gidan,cikin rudu da rikicewa dan ko maganar ma ta kasa tafara nuna masa Aryan wanda ke can cikin falo asheme kamar wanda ya mutu,
A mutukar hanzarce suka shiga ya daukoshi,umma na can daki tana bacci bata san abinda ke faruwa ba har suka tafi asibiti,suna zuwa Dr Al’amin ya karbeshi dama shine family Dr dinsu nan yashiga bashi agajin gaggawa ita kuwa Hanan na waje ta rasa inda zata tsoma ranta tun daga yanzu tafara nadamar abinda ta aikata, bawai matakin da minister zai dauka shine tsoronta ba a’a shi dama tasan dole ne ya daureta har igiya tayi rara amma tsoronta kashe dan mutum da tayi,
Tafi awa tana kaiwa da komowa tasan idan minister yaji abinda yafaru ai yau sai kwanan prison tunda ta tabo shalele,yaron da yake jinsa kamar ransa, tana nan tsaye tana ta faman kaiwa da kawowa saiga umma barira da daya daga cikin securities din gidan itama ya kawota hankali atashe,
“Sa’adatu….. Me yasamu Aryan din? Ni natashi daga bacci na duba naduba ban ganshi ba sai da nafito nemansa wai ko yafita karatu sai suke fada min kun taho asibiti, me yasameshi?”
“Umma faduwa yayi yabuge da kujera,wallahi babu abinda ya sameshi bayan wannan….”
Kafin umman tasake magana sai ga Dr Al’amin yafito,
“Insha Allah nan da anjima ko zuwa dare zamu iya barinku ku tafi gida saboda ya farfado dama ba wani abu bane furgici ne da tsoro da ya shigeshi shi ya haifar masa da wannan suman amma insha Allah babu komai zai tashi normal…”
Sai lokacin Hanan taji hankalinta ya dan kwanta ta samu yar nutsuwa da taji cewa bai mutuba yana numfashi,umma kuwa ai arikice take dan kallo daya kadai zaka yimata ka fahimci hakan,tana dai tsaye ne kawai amma hankalinta yagama tashi,
Wurin Aryan din suka shiga suka iskeshi yana bacci amma ga numfashinsa nan yana fita yanda ake bukata, dukkansu jugum suka yi babu wanda yake cewa uffan har tsawon wani lokaci. Koda Aryan din ya tashi jikin umma yaje ya boye yana leken Hanan cike da jin tsoronta, murmushi Hanan tayi masa idanuwanta jajur sanadiyyar kukan da tayi,
Hannu ta mika masa, “Zo mana cutie”
Kin zuwa yayi har suka tafi gida yana nanuke da umma suna zuwa gida suka iske miss calls din Khalil yafi abinda yafi yakira Aryan yakira umma saboda tunda yakira Aryan yaji bai sameshi ba yakira umma yaji ko lafiya ita dinma shirun yaji,
Hanan kam sai sake shiga jikin Aryan take tayi tana son yaron yasaba da ita yadaina tsoronta yasake da ita kamar kowa tunda lalura tashigo ciki dan a mota har suka zo gida umma nabata labarin dama haka yake yi tun yana jariri idan yayi kuka yayi kuka sai kajishi difff yasuma shiyasa uban baya son bacin ransa,
Chocolate ta debo masa irin wadan taga umma na bashi idan zai tafi makaranta, “Cutie zaka sha wannan?” Girgiza mata kai yayi alamar a’a da tace yazo yakarba sai ya makale kafada yahaye kan cinyar umma,
Bata hakura ba taje ta zubo masa tuwon semovita miyar egusi wanda ke cikin fridge a ajiye saida ta dumama masa sannan ta zubo cikin plate ta kawo inda yake zaune yana ta danne danne awayarsa yaran yanzu kamar da ilmin danna waya ake haifarsu saboda yanda yaketa latsa wayar sai ka rantse babba ne,
“Cutie zo inbaka tuwo kaci kaji….”
Kallon umma yayi sannan ya kalleta,make kafada yayi,
“Ni umma ce zata bani”
“A’a ni zan baka yaron kirki dan babansa,zo kaci kaji,akwai dadifa tuwone ko incinye abuna? Kaga zan cinye to…”
Kamar baya son zuwa haka ya sauka daga kan cinyar umma wacce ke cemasa maza yaje yaci,tafiya yake kamar yana taka kwalba ahaka yaje wurinta,murmushi tayi ta dorashi kan cinyar ta tafara bashi abaki yana ci,tashi umma tayi tabarsu tashiga daki tana waya da Khalil wanda ya kara kiranta tana dauka tajishi arikice,