MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

“Umma meya samu Aryan ne? Na kira aka ce mun kunje asibiti…”
“Waye yafada maka Aryan muka kai? Matarka muka raka kanta na ciwo kuma tasamu sauki”
Ajiyar zuciya taji yasaki mai karfi,
“Allah yabata lafiya,yanzu ina Aryan din?”
“Gashi can tare da ita afalo tana bashi abinci”
“Ok to bari na kirashi”
Suna zaune tana ta bashi tuwon yana ci yana game din Disney magic awayarshi amma yafi maida hankali kan game din haka dai take ta lallaba shi tana bashi,kiran Khalil ne yashigo sai jinsa tayi yana fadin,
“Papa….”
“Na’am Aryan….”
Bata jiyo maganar uban ta iya Aryan take ji kawai,
“Ina kaje dazu na kiraka baka nan?” Khalil ya tambaya dan son tabbatar da gaskiyar abinda daya daga cikin securities din yasanar dashi,
“Munje asibiti nida umma da Mommy”
Wani sanyi Hanan taji jin ya kirata da mommy ashe haka iyaye ke jin dadi idan ‘yaya suka kirasu da wannan sunan?
“Shikenan naje gombe idan zan dawo me zan kawo maka?”
“Yogurt…..”
“To shikenan sai nadawo”
Katse wayar yayi yajuya ya kalleta, “Na koshi”
Murmushi tayi ta shafa kansa, “Daure ka cinye dai cutie nah”
Karba yayi taci gaba da bashi har sai da ya cinye din sannan ta d’aukeshi suka haura sama, dakinshi ta kaishi tayi masa wanka ta sake daukoshi zuwa cikin dakin ta zauna ta shirya shi yasha turare,pink din riga t shirt ta saka masa da bakin jeans ta daura masa belt,akan cinyarta ta dorashi tana gyara masa sumarshi,
“Kai wai ba a yimaka aski ne cutie?”
Jijjiga mata kai yayi alamar a’a baya so,dariya tayi ta d’aukeshi suka fita zuwa falonta,carton ta kunna masa a tv dinta itama tashiga ta watsa ruwa ta fito, doguwar riga ta saka marar nauyi sannan ta dawo wurinsa bayan ta dauko robar ruwa,
“Mommy Daddy yace min kin mutu….”
Cak ta tsaya daga shan ruwan da takeyi ta kalleshi tabbas yataba fada mata haka,
“Yaushe Daddyn ya fada maka” ta tambayeshi tana janyoshi jikinta,
“Da dadewa ya nuna min wani hoto yace na mamata ne awurin haihuwata ta mutu bayan an fito dani mu biyu sai dayan ya mutu itama mommyn sai ta mutu sai ni dashi kadai…..”
Hawaye taji yana kokarin zubo mata wanda bata san ko na menene ba amma tausayin yaron taji akaro na farko sannan taji tana nadamar abubuwan da tayiwa yaron na rashin jansa ajikinta da sakar masa fuska, Allah sarki maraya,
“Kuma sai naganki a school….”
Shafa kansa taci gaba dayi cikeda tausayinsa tana jin kaunar yaron na sake shigarta ta ko wacce kafa. Ranar tare dashi suka kasance har lokacin bacci yanata bata labari da yake yaro ne mai wayo da surutu,bacci ma adakinta yau yayi ta kwantar dashi
Misalin karfe 1:30 Khalil yadawo daga gombe kuma basu zarce ko inaba sai sabon gida domin yazowa da Aryan da tsarabar da yace yakawo masa. Agajiye yake lilis dan kana kallonsa ma zaka fahimci hakan,cikin fridge yasaka masa su fura da nonon daya kawo masa sauran kayan kuma sai yadora musu kan dining,duk da yasan Aryan din yayi bacci amma haka yanufi dakinsa,amma yana shiga yaga wayam baya ciki,gabansa ne yaji ya fadi nan yafita agigice da kamar yashiga dakin umma sai kuma yasake komawa sama ya nufi falon Hanan wanda bai taba shiga ba sai yau,
Wani kamshi ne mai sanyaya zuciya da narkar da ita gamida saukar mata da nutsuwa ya bakunci hancinsa dayake turaren wutar da take amfani dashi mai masifar kamshi ne daya daga cikin irin gudunmawar da anty badi’a ta kakkawo mata,sai da ya lumshe idanuwanshi sakamakon irin kasalar da kamshi da sanyin falon ya haifar masa dashi, kofar bedroom din nata yabude zai shiga amma duhu didim babu haske ko kadan……………….鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:08 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*22*
***Bai kokalleta ba kai da alama ma kamar bai san tashigo cikin dakinba domin shi ta lafiyar dansa yake yi gaba daya hankalinsa na kansa,
Tana tsaye tana kallonsu shida Dr Al’amin wanda keta kokarin kwantar masa da hankali ta hanyar yimasa bayanin cewa wai jikin Aryan dinma ai da sauki akan yanda aka kawo shi,shi dai Khalil duk bai gamsu ba domin irin yanda yaga ramar da yaron yayi sannan duk yafige yayi wani iri kamar wanda ya shekara yana jinya gara kawai yafita dashi waje aje can adubashi, sakin hannun Aryan din yayi yajuya suka fita shida Dr Al’amin domin Aryan bacci yake tayi. Awaje ya tsaya wurin su umma da hajiya yana yimusu bayanin gaskiya daga yau zuwa gobe zai fita da Aryan k’asar chairo ko India domin lalurar yaron ta tayar masa da hankali,wuri hanan tasamu ta zauna kamar wata munafuka sai faman rabe rabe takeyi,
“Banki ta takaba Khalil amma da dai ka dan sake basu lokaci nan din tukunna dan ni wallahi bana son harka da turawan nan,nan dinma likitocinmu babu abinda basa yi sai dai ko da yake ku kuna dashi shiyasa fitar bata yimuku wahala….”
“Shikenan hajiya amma fa duk kiduba kiga yanda Aryan yakoma…”
“Hakane,mudai muyi fatan Allah yabashi lafiya”
“Amin hajiya,bari naga Dr Al’amin”
A office ya iske Dr Al’amin yanata yan rubuce rubuce ajikin file din Aryan,abunku da dan jarida zama yayi ya tsare Dr Al’amin da tambayoyinsa masu zafi wadanda sunfi guda goma daga wannan sai wannan daga karshe yatashi yafita yasake komawa wurin Aryan, Hanan na zaune gefensa ta rafka uban tagumi,atsaye ya tsaya kyamm yanata faman safa da marwa hannuwanshi goye a bayansa,ta gefen ido take kallonsa wallahi ba dan kar tayi karya ba sai tace bata taba cin karo da halittar da ta dauki hankalinta kamar tashi ba,bata taba ganin namiji mai kyau da kwarjini da kuma cikar haiba kamarsa ba. Gaba daya ta raja’a a kallonshi bata ko kiftawa yayinda shi kuma hankalinsa kacokan ya tafi kan abinda yadace yayi wurin samowa Aryan lafiya baima san tanayi ba domin hankalinsa ba akanta yake ba dan baiko san da itaba awurinma,
Tunda yazo bai matsa ko nan da canba salla kawai ke fitar dashi,har lokacin magriba yayi,lokacin su hajiya suka dawo asibitin itada Zaid ita kuma Hanan suka tafi gida ita da umma barira,tun acikin mota take jin zuciyarta na addabarta da tunaninshi wanda bata taba jin irin hakanba akan wani namiji a iya tsawon rayuwarta,daga kallo daya da tayi masa duk tabi ta rikice ta gigice ta kuma dimauce,
Kasa katabus tayi kamar wacce aka zarewa laka daga jikinta motsi kadan sai taga fuskarshi ko shi kanshi yana kaiwa da kawowa cikeda damuwa a dakin da Aryan yake,ji take yi kamar ta koma taje taci gaba da kallonsa babu ko kiftawa,haka dai tasamu tayi bacci sama sama amma bawai cikakken bacci mai cike da nutsuwa ba,washe gari da sassafe ta tashi ta shirya ta hada breakfast din da John yashirya acikin basket wanda zata tafi dashi asibiti ita da umma, Arabian gown ta saka pink colour tayi rolling tasa hill sannan suka tafi PA yajasu, tunda suka shiga suka san abu yasake rikicewa domin Aryan sai razana yake kamar wadanda Aljanu suka shafa abun dai babu dadin ji gaba daya uban yashiga wani hali.
Abu kullum gaba yake kara yi duk Aryan yabi yayi wani irin baki kamar bashi ba,cikin sati daya kacal yazama duk wani iri baya ko iya tashi zaune ga firgita da yake ta faman yi ko bacci yake yi sai aga yanata firgita hakan yasa hajiya cewa su tattara su koma gida dan da alama wannan ciwon ba ciwon asibiti bane dan haka suje gida ayi magani,suna komawa gida aka fara maganin gida amma duk shi dinma jiya iyau Khalil kam ba acewa komai domin karshen tashin hankali ya shigeshi,