MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

Waya Hanan tayiwa abbanta ta sanar dashi lalurar Aryan nan yafada mata duk abubuwan da yadace tayi kafin yasamu yazo,
Dakin Aryan ta nufa bayan tagama wayar da abbanta ta iske Khalil zaune gefen Aryan wanda ke kwance yayi baki sosai, tunda yazo k’asar ko kalma daya bata taba hadasu ba sai yau dinnan,
Durkusawa tayi agabansa kanta a kasa tace,
“Abban Aryan nayi waya da abbanmu kuma na fada masa irin lalurar da Aryan ke ciki yace asamo ruwan zamzam sai ahada da ruwa inkaranta masa ayoyin warware sihiri sai abashi yasha sannan ashafe masa jikinsa dashi dan abisa dukkan alamu sihiri ne…..”
Baice mata komai ba sai kai da ya daga mata,nan take yaciro wayarshi ya turawa da Zaid massage akan yaje yasamo pure zam zam mai kyau ba fake ba,tashi hanan tayi takoma bedroom dinta taje ta dauko littafin ta na ayatusshifah,tana zaune tana duddubawa Zaid ya leko yasanar da ita yakawo zamzam din, magunguna kam Aryan na shansu dan gasu nan jarka jarka anata kawowa daga wurare daban daban,
Cikin babban jug ta zuba zamzam din ta hada da normal bottle water ta dauka ta kakkaranta ayoyin karya sihiri kamar yadda Abba yasanar da ita bayan ta gama ta mikawa Zaid, shida Khalil suka daga Aryan suka bashi yasha sannan suka shafe masa jikinsa dashi tas,tun atake awurin suka fara ganin alamar sauki domin yabude idonsa harda yin magana yana kiran Daddyn sa duk da maganar bata wani fita sosai. Tunda Hanan taga haka sai suka mayar da ruwan wannan addu’ar yazama shine ruwan shan Aryan kuma alhamdulillah sauki yana samuwa dan ana ganinsa,bayan kwana biyu Abban Hanan yazo duba Aryan sannan yataho masa da wasu magungunan irin na musulunci musamman na karya sihiri,dama yan dubiya kam suna shansu dan kullum gidan baya rabo da baki yan zuwa dubiya danginsu Khalil kuwa kusan babu wanda baizo ba,
Mamaki ne ya lullube Hanan saboda ganin yanda abbanta da Khalil keyi tamkar wasu abokai,yau shine karo nafarko da zata shiga sashen Khalil wanda tun bayan dawowarsu daga asibiti yakoma can tunda dama ashirye yake babu abinda ba asaka ba shine dai kawai baiga damar dawowa ba sai yanzu da Aryan baida lafiya sannan yadawo dan aganinsa Menene amfanin shi yana gabas dansa yana yamma baya ganin motsinsa,
Fruits da drinks ta jera cikin farantin silver ta dauka ta nufi sashen oga,suna daga ciki suna hangota tana tahowa amma ita bata ganosu sakamakon daga waje glass din mai duhu ne taciki kuma mai haske ne sosai kana kallon na waje tsaff,riga da zani ne ajikinta na atamfa tasaka hijabi,hanan taso tayi kauyanci domin bata san ta yanda zata bude kofar falon nashi ba tana tsaye da faranti a hannunta yataso da kansa yazo ya bude mata bata hanya yayi tawuce ciki sannan ya rufe kofar yabi bayanta,agaban abbanta ta dire farantin tana jin wani farin ciki yana mamaye ta tare da kaunar mahaifin ta wanda tasan har duniya tatashi banda Allah babu wanda zaiyi mata ko rabin gatan da yayi mata,tashi tayi tanufi kofar fita tana zuwa ta danyi tsamm da ranta tana kallon madannan dake gefen kofar bawai dan ta saniba kawai tayi shahada ta danna green din nan take taga kofar ta bude,kasa ta sauka taje ta harhado abinci kala daban daban wadanda John ya dafa saida ta dauko komai sannan ta sake komawa, yanzun ma shine yataso yasake bude mata sannan ta shiga, fruits din da ta kai musu ta iske suna sha da fork kowannensu,
Sunkuyar da kai tayi ta soma gaida abbanta wanda fuskarshi ta cika da fara’a dan bakinsa yaki rufuwa,
“Lafiya kalau uwar masu gida,mun sameku lafiya ko? Ya jikin yaron naki? Allah yabashi lafiya, Allah yasa takin arzikine”
“Amin Abba”
Magungunan da yazo dasu yafirfito dasu wadanda yawancinsu da zuma da zaitun da habbatussauda aka hada yana yimusu bayanin yanda zasu yiwa Aryan amfani dasu,sai bayan da yagama yimusu bayanin sannan ya kalli Khalil wanda ke sanye da farin yadi tsadadde dinkin boda yace,
“Dama ahar kullum ina fada maka yaron nan sai shima ka kula dashi da addu’o’i da zikirin safiya da maraice,wani abun idan kai anyi maka aka ga bai sameka ba to za a iya komawa ayiwa danka,kai kam bani da jaa akanka kana da kariya sosai atare dakai saboda duk wanda yayi riko da ibada ya tsaida salla kuma ya kiyayeta sannan yake yawaita tsayuwar dare da sadaka kuma yabi iyayensa to babu mahalukin da zaiyi nasara akansa sai dai makiya su gaji su barshi dan yafi karfinsu to amma shi sulaimanu ai kaga yarone dole sai ankula dashi, Allah yabashi lafiya kuma insha Allah nasamo bakin zaren,insha Allah zai samu waraka,sihiri ne akayi masa kuma mace ce tayi amma idan nace gata to nayi karya,amma tabbas mace ce dan naganta acikin mafarki,wato kasan wani sihirin akwai addu’ar da akeyi ayi salla raka’a biyu to Allah yana haskawa mutum inda aka yimasa sihirin idanma binnewa akayi duk za anuna maka wurin….”
Daga Hanan har Khalil jikinsu ne yayi sanyi Sosai, Hanan aranta cewa takeyi wannan wanne irin rashin imani ne da mutum zai nemi halaka dan tahalikin yaron da baiyi masa laifin komai ba? Ita kuwa wannan matar me Khalil yayi mata da har take kokarin hucewa akan dansa? Kwalla taji ta ciko mata ido bata gogeba saida tabarta ta sauka,
Shi kam Khalil shiru yayi yana tunanin to wacece wannan? Zuwa caan ya sauke ajiyar zuciya ya tankwashe kafafuwanshi yana lankwasa yan yatsun kafarshi domin yagano ko wacece, Abba ne ya kalli Hanan sannan yace,
“Yanzu kiyi azamar zuwa kibashi magungunan nan yasha sannan ki shafe masa jikinsa da wadannan mayukan,insha Allah zai samu waraka”
“Toh Abba”
Tashi tayi ta dauki maganin tafita,sai bayan da ta fita sannan Khalil ya kalli Abba yace,
“Nagode madallah malam, Allah yasaka maka da alkhairi,kuma ba dan kar kace nayi zargi ba wallahi har nagano wadda tayi min wannan abun…., bazai wuce yesmin ba,tajima tana bibiyata kuma ita ba da aure take sona ba a’a da sabon Allah nikuma ba halina bane,babu wanda bai san zaman kanta take yiba…., Yanzu last zuwan da nayi Denmark sai da tabini hotel din da nasauka…..”
“Ai shiyasa nake fada maka dole sai ka dage da addu’a da rokon Allah saboda mata iri iri zasuyi ta kawo maka farmaki sai dai Allah ya tsareka ya kareka daga kaidinsu….”
“Amin” yafada yana sunkuyar da kanshi kasa,shi dai Abba cigaba da bashi shawarwari yayi ta yi yanda zai cigaba da neman tsari daga kowacce irin mace. Hanan na zuwa dakin Aryan ta samu hajiya da umma atare dashi,sune suka taimaka mata tabawa Aryan magungunan yasha sannan ta shafe masa jikinsa da wadanda abba yace mata na shafawa ne,kuma sauki kam ana samu sai godiyar Allah dan ko minti 20 baiyi da shan maganin ba yace zaici abinci wanda rabon da yaci anjima,abinda yake son ci Hanan ta tambayeshi yace shinkafa dama akwai shinkafa acikin abubuwan da John yadafa yau dan haka ta sauka da sauri taje ta zubo masa a plate ta kawo,itace ta zauna ta bashi abaki kuma babu laifi ya dan ci dayawa daga nan bacci yakoma ita kuma tafita taje d’akinta tayi wanka sannan tayi sallar la’asar,wurin Aryan ta sake komawa tasamu suma su umma har lokacin suna tare dashi yatashi daga baccin da yake yi yanata game a wayarshi, gefenshi ta samu ta zauna ta dora kanshi saman cinyarta tana tofa masa addu’a ahaka Khalil yabude kofa yashigo ya samesu ganin Aryan yana game yaji dan sanyi sanyi acikin ransa,hannu yakai saman goshin Aryan yace,