MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

“Sannu abba na,jiki yafara sauki ko?”

Kai Aryan ya daga sannan yace,

“Uncle zaka tafi dani Italy ko?”

“Zanje dakai duk inda kake so abbana, Allah dai yabaka lafiya”

Daga haka yajuya yafita yakoma wurin Abban Hanan wanda ke can yana jiranshi, ita kuwa Hanan tana wurin Aryan har magriba tayi dan anan ma dakin Aryan tayi sallah tana idarwa taji shigowar text cikin wayarta,

_Kizo abbanki na kiranki._

Shine abinda taga minister yaturo mata tashi tayi tafita saida tafara shiga bedroom dinta ta shafa turare sannan tafita tana sanye da doguwar riga yar kanti da farin hijab ajikinta, tsayawa tayi bakin kofar tana wurwurga ido shin ina zata taba? Jan ta danna sai kuwa kofa tabude,ahankali cikin nutsuwa take takawa har zuwa cikin hadadden falon nashi wanda yafi kowanne falo dake gidan haduwa,komai nashi farine tas babu sirki,hatta Rug din dake shimfide a tsakiyar falon farine sai dai an diddiga masa kalar baki dan sake fito dashi,falon tafkeke ne na gaske amma sai dai babu tarkace masu yawa acikinsa,iya kujeru ne wato (Turkish Sofas) farare guda biyar sai glass tables manya da kanana an a’ajjiye su a muhallin da yadace dasu sannan ga kayan kallo manya manya sai fridge acan gefe daya sannan ga dining table da yan kujerunsa kwaya hudu shima farare acan gefen dama,daga gefen hagu kuma wasu fararen kujerunne kwaya biyu masu laushi an ajiyesu da farin Rug dan karami a tsakiyar su sai center table atsakiya,kai falon dai yayi ba karya kuma ya hadu karshen haduwa,ga toilet nan aciki sannan sai kofar bedroom dinshi agefe ta can bangare daya kuma kofar da zata sadaka da valcony ce wadda aka shiryata domin hutawa dan yanzun ma haka su abba acan suke suna hira,

Hanan tsaye tayi domin bata san inda zata nufaba, maganar su tajiyo suna kokarin shigowa,

“A’a ashe ma ga mai babban sunan har ta karaso”

Tajiyo muryar Abba yana fada cikin raha shi dai minister bata ji me yace ba, Abban ne yafara shigowa ya nemi wuri ya zauna sannan itama ta zauna akasa tana sunkuyar da kanta,

Sake sabuwar gaisuwa sukayi da abba sannan suka cigaba da hirar gida wanda ba karamin dadin hakan Hanan tajiba shi kuwa Khalil har har lokacin yana valcony yana shan iska daga Allah bai shigo falonba sai da yaji ana kiran sallar ishah, Hanan tasake sosai da abbanta yashigo,dan satar kallonsa tayi taganshi sanye cikin wasu kayan wadanda ba na dazu ba saboda yanzu milk colour din shadda ce ajikinsa sai kyalli takeyi dinkin half jamfa yayi kyau yayi kyau har ya gaji,

“Bari muyi salla ko…” Taji abbanta yafada,tashi tayi tana fadin,

“To Abba,bari naje na kawo muku abinci”

Fita tayi sukuma nan cikin falon suka tada kabbarar sallarsu ita kuma tawuce kitchen taje ta zuzzubo musu abincin da aka shirya na dare,suna salla duk ta kawo ta ajiye musu sannan tafita.

Bata sake komawa sashen minister ba sai wurin karfe 9 shi lokacin ma yana d’akin Aryan tare dashi dasu hajiya yadora Aryan din asaman cinyarsa yana yin game awayarsa,bata ga abbanta ba sai kayan kawai ta debo ta fito dasu tasan watakila abban yana masaukinsa dan dakyar ma ya yarda zai kwana da cewa yayi ayau zai koma,

Dakin Aryan ta shiga inda su hajiya ke ciki itada umma dakin gauraye da kamshin turaren Khalil na no 1 wanda ya mamaye dakin gaba daya,sai bayan da ta rufe kofar dakin sannan idanuwanta sukayi arangama dashi zaune dare dare bisa kan gadon Aryan ga kuma Aryan din akan cinyarshi,zama tayi gefen umma tana satar kallon Khalil wanda ke cikin blue din riga ta polo sai dogon blue din wando mai santsi,kamar lokacin da tafara ganinsa yanzu ma shagala tayi da kallonsa yana ta yiwa Aryan wasa wanda ke yin game,

“Mommy zan sha ruwa…” Taji Aryan yafada,

Tashi tayi ta dauko masa ruwan maganinsa wato ruwan addu’a taje ta mika masa,karba yayi yatashi zaune yasha sannan yakoma ya kwanta,ayanda ta lura Khalil ba mai yawan magana bane domin idan aka bata dama tsaf zata kirge adadin maganarsa tun shigowar ta dakin,iya umma da hajiya ne kawai ke ta hirarsu. Sai da Aryan yayi bacci sannan Khalil yafita,bayan fitarsa da yan mintuna itama tafita ta nufi bedroom dinta,shirin bacci tayi ta kwanta tana lumshe idanuwanta cike da begen Khalil………………..鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:08 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*21*

    ***Khalil na kwance kan gadonshi adakin hotel din da yasauka yana kallon pics din birthday din Aryan duk da baya nan aka gabatar da party din amma zaid yayi kokari kamar yana nan saboda yanda aka shirya abin cikin kyau da tsari bugu da kari kuma gashi yaga fuskar Aryan cikin farin ciki sosai hakan kadai da yagani yaji inama shima yana wurin ko kuma inama zai iya yin fuffuke yatashi da yaje anyi dashi,har yagama kallon pics din baiga Hanan ba koda yake ai ba saninta yayiba kuma ta yuyuma babu ita awurin.

Hanan kam har washe gari ma bata samu fitaba dan har lokacin bata jin dadin jikinta tadai shirya Aryan ta hada masa komai yatafi school,kuma har yaje yadawo tana kwance a bedroom dinta tana kallon hotunanshi dake cikin wayarshi wadanda sunfi dari,kuma duka nashi ne shi kadai bata ga na babanshi ba duk shi kadai ne akasashe daban daban gaskiya yaron nan ya zagaya duniya domin tun baifi shekara biyu ba ta ga uban yafiffitar dashi manya manyan k’asashen labarawa da na turawa dan wasu hotunan ga larabawa nan wani kuma turawa zaka gani gasu nan dai burjik wani kuma a saudiyya ne dan ga ka’aba nan da sauran kyawawan wurare dake cikin birnin k’asar,ta shagala sosai da kallon hotunan shiyasa har Aryan yadawo bata saniba tana ta kallon hotunanshi shida wasu yara kyawawa suma guda biyu kamarshi mace da namiji taji shigowar Aryan yana zuwa ya haye kanta kamar yadda yasaba, rikeshi tayi tana murmushi,

“Welcome back my Cutie…”

Kankameta yayi suna dariya pic dinshi da yaran nan ta nuna masa tana tambayarshi suwaye wadannan sai yace mata wai nawwar ne da Naina yaran Abba Khalid wai yan uwanshi ne, lallabawa tayi ta tashi taje tayi masa wanka bayan ta cire masa uniform dinshi tabashi abinci yaci sannan yafita islamiyya wurin malaminsa.

Bayan birthday din Aryan da kwana biyu Zaid yakoma gombe yanzu gida yarage sai iya Hanan da Aryan da umma barira,duk wani abu da yashafi Aryan yanzu Hanan ce keyi masa itama shagwabashi yanzu takeyi sosai wanda har Khalil yasan da haka dan komai sai Aryan yace masa wai mommyn shi ce tayi masa idan abinci ne sai yace itace tabashi shi kansa yasan tana kulawa da yaron Sosai ba kadan ba.

***

 Har yanzu sumayya bata samu ta shawo kan mujahid ba domin kullum cikin wulakantata yake yauma hakance tafaru tana daki tana ta sharbar kuka mami ta shigo ta zauna gefenta,cikin lallashi tace,

“Sumayya daina kuka kinji,yi hakuri,ki daina sakawa kanki damuwa akan mujahid kedai kawai kici gaba da addu’a idan har mijinki ne babu makawa sai ya aureki….kiyi shiru kinji”

Kai ta daga alamun to,haka mami taci gaba da rarrashinta daga karshe ta tashi tafita,tana fita ta dauki wayarta ta kira k’awarta muhibba ta zayyane mata dukkan abunda yake faruwa sannan cikin kuka ta karasa maganar tata da fadin,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button