MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 21 to 30

“Muhibba da me Hanan tafini da yake wulakanta ni akanta bayan ma tayi aurenta ita ta manta dashi amma shi kullum cikin kallon hotonta yake….”

“Babu da abinda tafiki sumy,ki kwantar da hankalinki kiji abinda zan fada miki…..”

“Ina jinki muhibba”

“Yawwa kema ki shareshi ki fita harkarsa kuma ki daina kulashi,ki nuna masa idan dashi ko babu shi zaki iya rayuwa,ki shareshi fa sosai dan shima yana sonki bawai ke kadai ke haukan sonshi ba saboda duk wanda kake so wallahi shima yana sonka sai dai ko wani dalili ya hanashi bayyanawa amma dan so shima yana sonki,ki danne zuciyarki ki shareshi shi da kansa zai sauko”

Shawarwari sosai muhibba tabata kan yanda zata share ya mujahid har sai yakawo kansa da kanshi,ita dai sumayya ji take yi kamar bazata iya ba saboda irin yanda a kullum wutar son mujahid ke ruruwa a cikin zuciyarta gashi shi kuma yayita disgata agaban kowaye babu ruwansa dazu fa agaban yan aikin gidan yayi mata rashin mutunci dan kawai tashiga dakinsa abinda yasata kuka kenan amma insha Allah zata danne zuciyarta tabata hakuri ta gwada aiki da shawarar muhibba.

***

 Bayan birthday din Aryan da sati daya Khalil yadawo nan yakawowa Aryan tsaraba mai tarin yawa ta takalma da jeans da t shirts masu tsada,

Kullum baya shiga gidan sai cikin dare misalin karfe 1 ko 2 wani lokacinma har 3 dan sai kowa yayi bacci agidan,bai jima da dawowa ba yasake komawa k’asar Italy amma kullum suna makale awaya shida Aryan wanda ada yamakale masa wai sai yabishi dakyar ya shawo kansa ta hanyar cemasa ankusa yin hutun makaranta ana yin hutu zai fita dashi duk k’asar da yake so.

Khalil baifi sati daya da tafiya ba Aryan yawayi gari da wani zazzabi mai zafi ga tari da ciwon kirji babu shiri aka kira Dr Al’amin yana zuwa da yadubashi yace su tafi asibiti dan dole sai ya kwantar dashi,

Asibitin suka tafi dukkaninsu cike da damuwa da tashin hankali ita kam umma ma kashe wayarta tayi dan kar Khalil yakirata haka ta Aryan dinma arufe take,kwantar dashi Dr Al’amin yayi yafara bashi taimakon gaggawa,

Aranar da yamma sai ga Zaid yazo kamar yanada masaniyar abinda ke faruwa,can asibitin yabisu dan ajikinsa ma aka debi jinin da aka karawa Aryan din,

Khalil shi bai san abinda yake faruwa ba amma haka kawai yaji jikinsa duk babu dadi kamar irin baida lafiya dinnan alhalin kuma shi lafiyar sa kalau amma dai jikinsa yayi masa wani irin sanyi kalau haka dai ya daure yaci gaba da al’amuransa wadanda suka kaishi,

Yana ta kiran Aryan awaya kuma baya samunshi haka itama wayar umma bata shiga daga karshe sai Zaid ya nema dan jin meke faruwa amma sai Zaid ya ce masa wai babu komai da ya tambayi Aryan sai yace bacci yake yi,cewa yayi to ya gaidashi shida umma sukayi sallama,

Duk dangi kuwa babu wanda bai san rashin lafiyar Aryan ba Khalil kadai aka boyewa saboda ba ason afada masa saboda kar hawan jininsa ya motsa,tun a washe garin ranar da aka kai Aryan asibiti hajiya tazo Abuja suna tare a asibitin suna kula dashi,

Zaid kuwa sai hanya hanya yake yiwa Khalil idan ya kirashi yace ya hadashi da Aryan sai yace yana toilet ko yace yana bacci ko kuma yace wai yana makaranta,da Khalil ya tambayeshi to me yasamu wayar Aryan din da yasa baya samu idan yakira sai yace wai ai swimming pool tafada a hannun Aryan shiyasa ta daina yi nan Khalil yace masa to idan yadawo ya daukeshi suje wurin siyar da wayoyi ya siyo mishi duk wacce yakeso komai tsadarta da toh Zaid ya amsa masa sukayi sallama suna yin sallama yakashe shima tashi wayar gaba daya.

Yau kam tashin hankalinsu yafi na kullum domin tunda garin Allah yawaye Aryan yake ta faman suma daga safe zuwa yamma ya suma yafi sau biyar,shi kansa Dr Al’amin yagama shiga tashin hankali saboda yanda jikin Aryan yarikice Sosai,

Hanan shawara tayi da zuciyarta bata sanarwa da kowaba aranta tace gara ta fadawa Khalil abinda ke faruwa tunda boyewar bata da amfani da afada masa mutuwar dansa gara afada masa rashin lafiyarsa yazo ya ganshi kar aje yamutu,

Text massage ta tura masa tana turawa ta kashe wayarta itama, Khalil na kwance yakasa bacci dan a yan kwanakin nan sam baya iya bacci gashi dai lafiyarshi kalau amma kamar baida lafiya yake jinsa,jin shigowar sako yasashi kallon agogo,karfe 3 da kusan kwata dan asubah ma ta kusa,daukar wayar yayi yabude sakon nan yaganshi kamar haka,

_Abban Aryan kazo gida domin Aryan ba lafiya muna asibitin Dr Al’amin._

Yana gama karantawa yaji yashiga cikin tashin hankali,acikin wannan daren yafita akayi cuku cukun jirgin da zai tashi da asubah zuwa Nigeria,bai dauki komai ba sai wayoyinshi yanufi Nigeria.

Kamar yadda babu wanda yasanar dashi rashin lafiyar Aryan shima babu wanda ya fadawa cewa yabaro Florence yataho Nigeria har saida jirginsu ya sauka sannan yakira PA yace yazo ya d’aukeshi,

Kai tsaye asibitin suka wuce PA ne agaba sai securities dinshi abaya shi kuma yana tsakiyarsu,

“Ni wallahi bana son yaron nan Khalil yaji maganar nan saboda hawan jininsa” umma barira tafada cikin damuwa domin dukkansu suna waje su hudun zaune kofar dakin da Aryan ke ciki kan wasu kujerun karfe wadanda aka tanada awurin domin zama,

“Ai gashi nan ma dan halak” Zaid yafada yana mikewa tsaye,

Hanan kam kanta asunkuye yake ta dunkufar dashi bayan tasha kukanta ta more dan har idanuwanta sunyi jajur ga shi sunyi luhu luhu,wani arnan kamshi ne yafara kaiwa kofofin hancinta sumame wanda ya tilastata ta dago kanta domin ganin mamallakin wannan kamshi,

Dakatar da securities din nashi yayi yakarasa wurinsu umma shi kadai,ai Hanan ji tayi tai suman zaune, dama wannan shine minister? Shine mahaifin Aryan? Shine abokin Abbanta? Mamaki ne ya mamaye dukkan ilahirin zuciyarta domin bata taba zaton zata ganshi hakaba kyakkyawa mai cikar halitta da kwarjini ba,kamarshi daya da Aryan da Zaid amma duk ya kere su a kyau domin farine kal dogo Sosai dan har ya dan rankwafa ma’abocin bakar suma wuluk mai matsakaicin jiki, fuskarshi dauke take da manyan eye balls farare tas ga hanci kamar biro bakinshi kuwa dauke yake da lips masu taushi suba red ba kuma su ba pink ba akwai saje a fuskar tashi wanda yataho har zuwa habarshi yahade da dan kyakkyawan gemunsa amma bawai buzu buzu da yawa ba a’a dan gwanin sha’awa dashi kuma shine ya karawa fuskar tashi kyau da annuri, kuruciyarshi afili  dan sam babu maganar tsufa atare dashi sannan jin dadi da hutu sun sake fito da kuruciyarshi da kyakkyawar halittar shi dan duk da yana yawace yawace baya zama wuri daya amma hakan bai samu nasarar hana jin dadi da hutun da yake ciki bayyana agareshi ba,bafulatani ne na usul daga kallonsa zaka fahimci hakan,samun kanta tayi da nadamar yimasa rashin kunya da tayi abaya ita wallahi ta zaci zata ganshi tsoho kuma mummuna ashe abin bahaka yake ba sai gashi ta ganshi mai kyakkyawar halitta ma’abocin cikar haiba da kwarjini,shagala tayi da kallonsa domin tunda yazo ya dauke mata hankali wanda bata farga ba har saida yagama gaisawa dasu umma yanufi dakin da Aryan ke ciki batare da yako kalleta ba dan shi hankalinsa ma bai kai kanta ba, firgigit tayi daga duniyar da tatafi kamar kazar da kwai ya fashe mata aciki haka ta mike jiki babu kwari tabishi cikin dakin………..鉁嶏笍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button