MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

Tunda wannan abun yafaru shikenan Hanan ke kunyar sake cin karo da Khalil dama kuma shi ba mazauni bane hakan yakara nisanta fuskokinsu da haduwa da juna,wurin da glass din yafashe kuwa tuni har an dauko ma’aikata sun gyara sun saka sabon glass awurin,
Text ta sake turawa Khalil akan maganar tafiyar ta kano dan gano gida amma sai yayi mata reply da wai ba yanzu ba,to wai sai yaushe zataje gidanne? Ranar ma tayi kuka dan har yafi na waccan ranar da ya hanata zuwa,ita zaman gidanne ma gaba daya ya isheta babu inda mutum zaije ko makota bazai fita ya shiga ba kai wannan zaman baiyiba gaskiya,haka tayita rayawa aranta,ko kuma dan shi baya zaman gidanne shiyasa yake ganin kamar zaman dadinsa sukeji?.
Khalil yau tun yana office yake jin zazzabi yana neman saukar masa amma dai yayita daurewa ga mura dake damunsa tun jiya amma ita bata yi tsanani ba sai yau din yake jin tafara takura masa,
K’arfe 10 yau ya koma gida bayan ya gama ganawa da lauyansa wato barrister muhsin wanda ke cigaba da kareshi akan karar da yesmin ta shigar, barrister muhsin yace masa akwai alamun nasara sosai dan reshe ne ma ke neman juyewa da mujiya duk da ita ce tayi k’arar,
Yana komawa gida ya ajiye wayoyinsa yasaka su a flight mood sannan ya canja kayan jikinsa ya shige bargo ya kwanta domin izuwa yanzu zazzabin yagama rufeshi ga mura wacce ke haddasa masa tari da atishawa harda ciwon kai. Washe gari yakira likita yazo ya dubashi sannan yatafi ita Hanan bata san yana gida ba ranar dan babu inda yafita da yayi bakima hakuri yace abasu saboda bazai iya fita ba,zuwa yamma dai zazzabin ya sauka sai iya murar kadai gashi baya kaunar shan maganin murar nan dan duk sai yabi ya kashe masa jiki kuma yayita sakashi bacci,ko yau dinma wuni yayi yana bacci kamar wani dan kwaya,da suka yi waya da Khalid yake dubashi shine Khalid din yake tsokanarsa wai ayi masa farfesu mana dahuwar kalwa da attaruhu yaci Wallahi da haka zai fatattaki wannan murar, shawarar Khalid ya dauka dan haka da yasamu yatashi yayi wanka yayi salla sai yafita da niyyar yaje k’asa ya sanar da umma dan baya son kunna wayarsa yanzun nan mutane zasu dameshi da kira,ahankali yake takawa saboda jikinsa babu karfi sosai,ta gefen part din Hanan yajiyo k’arar kida dan haka yakoma yabi ta wurin domin dubawa, muryar m Sharif ce ta fara dukan kunnuwanshi cikin wakarsa ta _hafiz_ koda ya leka Hanan ya hango ita da Aryan sun takarkare sai casa rawa suke yi…………………………..鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*35*
***Samun wuri yayi ya harde hannuwanshi akirji yayi crossing legs dinsa ya jingina yana kallonsu,daga ita har Aryan din basu san yana tsaye awurin ba har saida wakar ta kare wata ta shiga nan fa hanan tafara bi tana wata irin rawa ahankali idanuwanta arufe “Sabon salon soyayya na kirkiro…. Kai zan yiwa amma sai munje gida…..sabon salo…sabon salo…. Sabon salo”
Juyowar da Hanan zatayi taga mutum jingine yana kallonsu,guduwa tayi ta shige cikin bedroom dinta,sai lokacin shima Aryan ya hangoshi da gudu yatafi ya rungumeshi,
“Papa….”
“Sakeni Aryan kar ka kada ni mana,tun jiya baka ganni ba amma shine baka nemana ko?”
Girgiza kai Aryan yayi,”Ina nemanka Daddy”
Kama hannunsa yayi suka sauka k’asa wurin umma barira nan yake sanar mata da bukatar shi na son yimasa farfesu ko wanne iri amma yasha daddawa da attaruhu saboda mura ke damunsa, daga nan sama yakoma shida Aryan yana yiwa Aryan takarar kar ya dameshi da surutu baida lafiya idan kuma ya dameshi koroshi zaiyi, bedroom dinshi suka wuce kai tsaye ya kwanta saman gado shima Aryan yabishi ya kwanta akanshi, murmushi yayi ya rungumeshi yana cemasa,
“Wato duk da nace maka karka dameni shine saida ka fara ko? Zan koraka wurin mommy yanzun nan kuje can kuci gaba da rawarku tunda rawa momyn ke koya maka…”
“Daddy tana koya min karatu ma”
“Me da me take koya maka? Fada min inji”
Kamar Aryan jira yake yafara jero masa irin karatuttukan da Hanan ke koya masa tiryan tiryan,
“Tana zaneka idan bakayi karatu ba ko?”
“A’a bata zaneni…..” Yabashi amsa yana sake hawa kanshi wai zaiyi doki. Hanan sai da ta tabbatar da cewa Khalil yatafi sannan tafito ta sauka k’asa,a kitchen ta samu umma tana gyara kaji manya manya wad’anda zata yiwa Khalil farfesu dashi, karba tayi tana tambayar umma saboda tunda tazo gidan bata taba ganin umma barira a kitchen ba tunda akwai kuku,
“Ai kin san mu’azzamun baya jin dadi mura ke damunsa to shine yace ayi masa farfesu mai yaji dahuwar kalwa…”
Dariya Hanan tayi jin umma tace wai dahuwar kalwa,ita kam agida duk lokacin da wani ke yin mura mamaye wani shayi take dafawa na na’a na’a sannan yasha kayan kamshi,
Gyare kajin tayi guda uku manya manya sannan ta hada kayan kamshinta ta dafasu rigib sannan ta dora shayin bayan ta gama ta zuba masa ta zubawa umma nata ta dauka ta nufi dakinsa,suna falo shida Aryan bayan sun idar da salla,shi yana saman kujera shikuma Aryan yana kasa yana wasa akan rug sai burgima yake yi,da sallama a bakinta ta shiga ta jawo glass table din dake gefenshi ta dora masa akai sannan tafara gaisheshi,
“Ina wuni….?”
“Lafiya lau…”
“Ya jiki?”
“Da sauki”
“Allah yakara sauki”
“Amin”
Daga haka ta kwashi yanmatan kafafunta ta fita. Farfesun yabude tun kafin yakai bakinsa yawunshi ya tsinke,kasa ya sauko ya tankwashe kafafuwansa yasoma yaga yana ci dama kuma gashi yadahu sosai irin yanda ake so kuma farfesun yasha kayan kamshi da daddawa sosai,tare da Aryan suka kusa cinye naman dan sai da kowannensu yaji ya koshi sannan suka hakura Khalil ya rufe sauran ya ajiye,shi duk a tunanin sa umma barira ce ta dafa bai taba kawowa Hanan bace,tun bayan da yagama cin farfesun yaketa fama da face facen hanci, Aryan yatura zuwa cikin bedroom dinshi ya dauko masa tissue,babu laifi yaji dadin naman domin yaji yajin da yaci yafara yimasa amfani. Har lokacin bacci yayi suna tare da Aryan wanda tuni shi yajima da yin bacci ma,
Hanan na kwance dakinta abun duniya ya taru yayi mata yawa,inbanda tunani da begen Khalil babu abinda ke damun zuciyarta,tana tsananin sonshi da bukatarshi wanda har bata san yanda zata kwatanta ba,
Tashi tayi daga kwancen da take domin ta kasa yin baccin,kamar wacce akace tafito ta bude kofa tafito sanye da night gown dinta milk colour,gaban corridor taje ta dan jingina da jikin karfen da ke kewaye da wurin tana jin iska tana kadata tamkar zata dauketa,kanta ta daga sama tana kallon taurari wadanda suka yiwa sararin samaniya ado suka kara haskashi,daidai lokacin shikuma Khalil yafito rike da Aryan a kafadarshi zaije ya kwantar dashi acikin dakinsa,har yazo ya wuceta bata sani ba saboda hankalin ta baya wurin yana can wata duniya ta daban mai cike da soyayya, kauna,shauki da kuma bege,babu abinda take son kasancewa tare dashi ahalin yanzu sama da Khalil kuma tasan bazata taba gajiyawa da shiba domin kallonsa kadai zai dauke mata hankali ya debe mata kewa sannan zai nisantata da dukkan damuwa.