MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

Ahankali yake tahowa yana dosota amma bata saniba har yazo inda take tsaye kanta asama idanuwanta kyarr tana kallon sararin samaniya ko kiftawa bata yi,akusa da ita kadan ya tsaya yakai hannunshi yadafa karfen dake wurin shima sannan yakai dubansa izuwa sama dan ganin abinda take kallo wanda ya shagaltar da ita har haka,

Samun kansa shima yayi da jin dadin kallon da yake yiwa saman nan ya lumshe idanuwanshi sannan yabudesu yasake kai dubansa izuwa sama,shi dan soyayya ne kuma ma’abocin sonta akoda yaushe irin wannan yanayin shi ake kira da lovers moment domin idan masoya guda biyu suka samu kansu a irin wannan yanayin sukan manta da kowa da komai, sannan sukan manta da damuwarsu da duk wani abu da ka iya kawo musu cikas acikin duniyar soyayyar su,

Sake lumshe idanuwanshi yayi sakamakon wata irin iska mai dadi da ratsa jiki da ta shigeshi,a wannan lokaci bazai iya fada maka takamaimai halin da gangar jikinsa da ruhinsa ke ciki ba,fata yake inama yabude idanuwansa yaganshi tare da Ramlat,inama ace yaga Ramlat akusa dashi koda cikin mafarki ne,

Saura kadan Hanan ta fasa ihu saboda ganin mutum da tayi akusa da ita wanda sam koda wasa bata ji zuwanshi ba saboda tana can duniyar tunani,

“Abban Aryan….” Ta fada bakinta na dan rawa,juyowa yayi ya jingina ya harde hannuwanshi akirji yana kallon ta bayan yayi crossing legs dinsa kamar yadda ya saba tsayuwarsa,kallonshi take yi daga sama har kasa kamar yaune tafara ganinsa, bakin dogon wando ne ajikinsa na sport sai farar t shirt ta kamfanin Adidas kafarshi sanye da takalmi slippers dama shigarshi kenan kullum fari baida kayan da suka wuce wadannan ko meyasa oho,

“Abban Aryan yaushe kazo nan?” Ta bukata bayan ta rufe bakinta da hannayenta,

“Kina can duniyar tunani…… Tunanin saurayinki wanda na rabaku kike yi ko?”

Sake rufe idanuwanta tayi da dukkanin tafukan hannayenta tana girgiza masa kai alamar A’a,

“Fada min gaskiya karki yimin karya….”

“Hmmmm” tafada tana gyara tsayuwarta,

“Nasan zafin rabuwa da masoyi…. Nasan irin radadi da azabtuwar da zuciya kan shiga aduk lokacin da ka rasa wanda kake so….. Nasan kema acikin wannan yanayin kike rayuwa ahalin yanzu….. Har yanzu kina kukan rabaki da masoyinki da nayi….”

Lumshe idanuwanta tayi take wasu hawaye suka gangaro mata wanda ba na komai bane face na tsantsar soyayyar da take yimasa,inama zata iya,inama tana da dauriya da kwarin gwiwar da zata iya duban kwayar idonshi ta fada masa ita shi take so shi take kauna ba waninsa ba,inama,zata iya kallonsa cikin ido ta sanar dashi akansa ne zuciyarta ke shiga duk wadannan abubuwan da ya zayyana,

Ganin hawaye na bin kumatunta ya sake tabbatarwa da kansa cewa abinda ya fada ko kuma yake hasashe gaskiya ne domin gashi nan har kuka take yi saboda fama mata raunin dake zuciyarta da yayi,

“Hmmmm…… Wai meyasa masoyi bai fiya kasancewa da masoyinsa ba har tsawon lokacin da yadace?….. Me yasa aduk lokacin da kake tare da masoyinka sai wata k’addara ta rabaku?…… Meyasa yawancin masoya basa samun happy ending?……”

Kawar da kansa yayi ya furzar da wata zazzafar iska kwayar idanuwanshi har ta sauya daga launin fari zuwa ja, karfen wurin ya dafa yana jin tamkar ya fashe da kuka,ita kuwa Hanan dama kukan take wanda zata iya kiranshi da kukan bakin ciki wai Khalil shi duk azatonsa kukan soyayyar wani take yi ba soyayyar shi ba,meyasa yakasa ganewa cewa ita shi take so? Wanne irin makaho ne shi da ya gagara gane tsantsar soyayyar da take cikin idanuwanta wanda take yimasa?

“Kiyi hakuri kowa da yadda Allah ke tsara masa rayuwar sa…. Wasu masoyan sukan kasance da juna tamkar tif da taya ko kuma kamar wata da zara amma lokaci guda sai wata k’addara ta rabasu…. Babu abinda yafi zama da masoyi dadi nasani….. Sannan babu abinda yafi rabuwa dashi daci,tashin hankali da shiga damuwa…. Nasan kina cikin damuwa amma ki kara hakuri har zuwa lokacin da Allah zai kawo karshen zamanki atare damu….”

Wata faduwar gaba ce tasoma ziyartarta jin abinda yafito daga bakinsa wai karshen zamansu,ita da take fata da burin kasancewa tare dasu har karshen rayuwar ta amma yana yimata maganar rabuwa da ita,bata san lokacin da kuka ya subuce mata ba…. Dagowar da zatayi taga wayam babu Khalil babu alamarsa har yabar wurin,da kuka ta koma dakinta ta fada kan gado taci gaba da rusar kuka.

Shima Khalil cike da damuwa yashiga sashensa ya yada zango a falonsa ya zauna cikin tsantsar damuwa da radadi,wai ma meyasa yabi ta son ran Aryan ya auro yarinyar nan? Meyasa ya rabata da masoyinta wanda take so dan kawai biyan bukatarshi alhali kuma yasan zafin radadin rabuwa da wanda kake so? Shi dai gashi Ramlat bata raye amma kullum cikin damuwar rashinta yake wani lokacin har zubar da hawaye yake yi to inaga Hanan wacce ita masoyin yana raye amma aka rabata dashi ai dole tayi kuka idanma akwai abinda yafi kuka dole tayi,

Zamewa yayi ya kwanta kan doguwar kujera idanuwanshi suna kallon sama, tambayar kansa yake shin menene mafita? 

“Ka saketa kawai….”

Zuciyarshi tabashi amsa tana sake karfafa masa gwiwar aikata hakan domin hakan shi kadai ne mafita kawai,sabanin haka kuwa zai sa yazama azzalumi mai son kansa kuma marar tausayi,tashi yayi dakyar ya nufi cikin daki zuciyarsa na raya masa wani abu……………………..鉁嶏笍

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button