MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

Da yake ranar aikine Aryan baya nan yana school,shiryawa tayi taci kwalliya cikin atamfa exclusive koriya dinkin riga da skirt kamar yadda ta saba dinkunanta, green din mayafi ta yafa sannan ta dauki handbag wadda ta dace da shigarta haka ma takalminta, tana falon k’asa zaune ita da umma tana jiransa amma har azahar shiru wai meeting yakeyi da mr president daga k’arshe dai sai PA yaturo wai yazo ya dauketa yakaita office dinshi sai su wuce ta can basai yadawo gida ba,
Office din nashi yayi masifar haduwa kamar kar ka fita daga ciki dan tsabar kyau baya ciki yana can meeting dan haka ta shiga ciki ta zauna a inda aka kebance dan baki na musamman, kamar yanda yake babu hayaniya to haka office din nasa shima babu wasu takarcen hayaniya aciki,komai atsare kuma ashirye,kan table dinsa kuwa kambun girmamawa ne sunfi abinda suka fi irin wadanda ake bashi sannan ga hotunanshi nan manya manya kafe acikin office din wani shi kadai wasu kuma tare da mutane,wasu kuma tare da matasa yan kwallo,kan teburinshi kuwa wani dan karamin frame ne mai dauke da hoton Aryan ajiki,
“Ohh ni Sa’adatu wannan bawan Allah yana kaunar d’an nan nasa…… Har a office dinma?”
Tana nan zaune tana zaman jiransa duk tagama kosawa duk da cewa ga kayan kallo nan tv katuwa nata faman aiki ankamo tashar labarai ga fridge can kuma shima gefe guda dama kishin ruwa take ji dan haka ta mike ta nufi fridge din da kanta tana zuwa ta budeshi nan ta ganshi tafare da kayan sanyaya makoshi iri iri sai dai kuma abinda idanuwanta suka gane mata sune suka yi sanadiyyar tsayawar numfashinta cakk take ta firfito da ido kamar zasu fado kasa dan tsananin firgici da tsoro…………………鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:12 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*30*
***Jikinta rawa yashiga yi babu bata lokaci cikin hanzari ta mayar da fridge din ta rufe ta koma ta zauna tana al’ajabin wannan lamari me neman sakata cikin wasi wasi,
“Giya?….. Dama minister mashayin giya ne? Kai anya kuwa iyayensa da abbanta sun sani? Kai ko iyayenshi sun sani abbanta bai saniba dan idan har yana da masaniyar haka to babu abinda zaisa ya dauki auren yarsa ya baiwa mashayi….. Innalillahi” Ta fada acikin zuciyarta tana mai rafka tagumi saboda takaici da nadamar fadawa tarkon sonshi da suka lullubeta lokaci guda,
Gaba daya ma ta rasa abinda zatayi taji sanyi acikin ranta,gaskiya Abban Aryan yayi bala’in bata kunya,ohh Allah kowa dai ka gani kabarshi ayanda ka ganshi domin Allah kadai shine yasan sirrin cikinsa da wajensa,ai ko cikin mafarki bata taba kawowa kanta cewa wannan bawan Allahn zai sha giya ba ashe ashe,
Zaman jiransa taci gaba dayi duk zaman yasoma gundurarta domin ta gaji da jira,ta saka ta warware ahaka yashigo office din tare da wasu mutum biyar wadanda take kyautata zaton cewa bakinsa ne, kasancewar tana wuri daya babu wanda yayi mata magana saida yagama dasu ya sallamesu sannan yamike daga kan kujerarsa ita kuma sai daure fuska take yi kamar me,
“Muje ko…..” Daga haka yayi gaba itama ta mike tabishi abaya securities suka dafa musu baya,
Har acikin mota babu wanda yace uffan saida suka fara tafiya sannan yayi magana hankalinsa yana kan wayar dake hannunsa,
“Me zaki kai mata?” Shine tambayar da taji yayi mata idanuwanshi akan screen din wayarsa,saida ta dan yi jimm sannan tabashi amsa,
“Duk abinda yasamu….”
Bai sake magana ba itama haka asalima dauke kanta tayi zuwa glass din motar tana kallon birnin abuja domin bata taba zuwa nan haka ba sai yau,awani katafaren supermarket taga sun tsaya,dan karkacewa yayi yana laluba aljihunsa duka guda biyun,
“Ohh Allah ashema kudin nawa sun kare….” Yafada yana kokarin ciro yan canjin da suka rage masa ajikinsa domin duk ya rabar da kudin mawa masu neman taimako da bakin da suke zuwa office gaisuwa,
Sabbin yan dubu dubu taga ya mika mata amma bai kai rafa guda ba sai dai da dan yawanshi badai zata iya kiyasta ko nawane adadinsu ba,
“Gashi ki siyo mata abinda kika ga yadace….. Karki zauna ki bata min lokaci inada abinyi”
Hannu biyu ta saka ta karba sannan tafita wasu daga cikin securities din suka take mata baya har zuwa cikin supermarket din,duba abunda yadace ta siya tafara saboda nafarko dai tasan tunda danginsu masu kudi ne idan ta siyi atamfa watakila arena ko akushe dan haka sai kawai ta yanke shawarar siyan kayan babies,
Hadaddun rigunan jarirai ta siya guda biyar masu tsada sannan ta siyi takalma da socks dinsu set daya sannan ta kara da kayan shafe shafen yara irinsu sabulun wankansu,turare,man shafawa,powder da sauransu shima set daya, atakaice dai tayi siyayya ta kusan fin dubu hamsin,kuma kayan bawani dayawa fal bane ba a’a kawai dai da yake masu tsada ne shiyasa,
Tana shiga mota aka mika mata kayan ta ajiye atsakiyarsu, “Gashi….”
Sannan ta mika masa canjinsa da yayi saura wanda shima bata san ko nawa bane,
“Ga guntun canjinka”
“Ajiye awurinki” Yabata amsa atakaice yana kokarin kara wayarshi a kunnenshi,
“Na’am Aryan….. Andawo daga school ko?…… Kaci abinci?……Ka koshi sosai?…… Yawwa lovely son……ok bye bye…..i love u too”
Tana jinsa har yayi wayar tashi yagama,yana gamawa ya mayar da ita aljihunsa ya ajiye ya sake ciro dayar itama yashiga latsawa,yanda ya manta da lamarinta itama haka ta manta da nashi ta jinginar da kanta jikin kujera bayan ta lumshe idanuwanta cike da takaicinsa duk kamshinsa yabi ya rikitata ya cika mata hanci,ba dan kar tayi karya ba to da zata iya cewa tunda take bata taba jin kamshi mai dadi mai sanyaya rai da zuciya kuma mai saka nutsuwa kwatankwacin nasa ba,wato kamshin nasa ne na dabanne ko acikin dubbai. Har suka hari gombe zaman kurame suke yi sai shi da yake yin waya jifa jifa dan daga tahowarsu zuwa yanzu taji yayi waya yakai sau goma, lallai mulki ba sauki ne dan koda amsa waya aka barka anbarka da aiki tuk’uru,
Basu suka shiga garin gombe ba sai la’asar,gidan Laila suka fara zuwa wato mai jego,tare suka shiga ciki ita dashi dan shine ma yayi mata jagora saboda ita ba taba zuwa tayi ba wancan karon da suka je barka da salla basu samu damar zuwa gidan laila dinba dayake sunyi yawo da yawa ranar,
Yanayin yanda taga gidan ya tabbatar mata da cewa itama Laila din wani hamshakin take aure dan gidanta kadai abin kallo ne,a falo aka yi musu masauki mai dauke da kayan alatu,suna zaune tana kan kujerar da take kusa dashi laila tafito rike da jaririnta wanda ke nannade cikin towel mai laushi,
“Oyoyo yaya Khalil….. Sannunku da zuwa” Laila ta fada fuskarta dauke da fara’a lokacin da tayi ido biyu dasu,
“Laila maman 3” Ya fada yana murmushi, karasawa tayi ta mika masa jaririn tana yiwa Hanan barka da zuwa,zama tayi da kyar tana dan ciccije baki, Khalil ta fara gaisarwa sannan ta juya suka gaisa da Hanan cikin sakin fuska,
Basu fi mintuna goma ba agidan suka fito dan ruwa kadai suka sha suka yimata sallama suka fita bayan Hanan ta ajiye mata kayan barkar da ta tafi mata dashi,