MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

Daga can gidan su Khalil suka wuce acan suka yi sallar la’asar suka ci abinci hajiya sai kaffa kaffa take yi da Hanan tana ta tambayar ta wai ko akwai abinda take so? Shi kam shiru yayi yana saurarensu yarasa wanne irin so hajiya ke yiwa yarinyar nan dan tunda taji zasu zo tayi musu tanadi shiyasa da zasu tafi harda su garin kubewa busasshiya da garin kuka da su daddawa ga kindirmo mai kyau da sauran kayan gargajiya wai tasan mata masu juna biyu akwai kwadaye kwadaye to gashi nan ko zata bukaci wani abu aciki ta huta nema,duk yadda Khalil yaso dakewa kasawa yayi dan saida ta kaishi da yin murmushi yawuce yabarsu suna sallama,
Kofar gidansu lokacin da suka fito cike yake dam da mutane yara da manya da matasa,hakuri yace abasu zuwa nanda kwana biyu zai dawo,gaskiya yan gombe suna yinsa kuma suna kaunar sa sai yau ta sake tabbatar da hakan domin har suka bar cikin garin mutane suna biye dasu sunyi convoy ashe dama kusan duk lokacin da zaizo haka suke yimasa sai sun rakashi har gida idan kuma zai tafi nanma sai sun rakashi wajen gari sannan suke komawa. Wannan karonma kamar dazu haka tafiyar tasu ta kasance baya da amsa waya babu wani abu da yake yi,ita kam duk zuciyarta babu dadi inbanda kuna babu abinda take yi,bacin ran abinda ta gani dazu yaki gogewa cikin zuciyarta,
Bayan sallar magriba suka shiga garin Abuja wanda ke dauke da daddadar iska tana kadawa garin lullube da ni’imar ubangiji,ajiyeta suka yi daga nan ko gidan bai shiga ba suka sake juyawa zasu koma office a wannan lokacin,
A dakin umma ta samu Aryan da umman yana kwance yayi pillow da cinyarta yana game a wayarshi sai shagwaba yake tayi umma nata shan kansa tana lallaba shi yaci abinci wai sai yagama game, shigowar Hanan ta sashi zabura ya yar da wayar yatashi yaje ya rungumeta yana yimata oyoyo,itama rungumeshi tayi tana shafa kumatunsa,
“Cutie”
“Mommy sannu da zuwa”
“Yawwa cutie nah”
“Sannu da zuwa,to kaga shikenan ma tunda ga ummanka ta dawo nima sai inhuta” inji umma barira,
Dariya Hanan tayi ta kama hannunsa,
“Au umma haka zakice? Mai gidane fa”
“Wannan mai gidan ai rigimamme ne kyaleshi”
Dariya Hanan tayi taja Aryan suka hau sama domin ko salla bata yiba,sai da ta kammala sallolinta sannan suka koma dakin umma can suka raba dare suna hira dan har 11 lokacin tuni Aryan yajima da yin bacci,
Saida ta kaishi dakinshi ta kwantar dashi sannan ta wuce zuwa nata,sam babu alamar bacci acikin idonta tunani ne kawai keta mutsuttsukar zuciyarta,ta rasa dalilin da yasa abun ya tsaye mata arai har haka ko dan tana yimasa kallon mutumin kirki na arziki ne shiyasa yanzu abun ke damunta? Tasan watakila yanzu ya shigo gidan tunda 12 tayi,text massage ta rubuta ta tura masa,
Fitowarsa daga wanka kenan yana saka kayan baccinsa yaji shigowar text dinta,karasa shiryawa yayi ya dauki wayar yazauna gefen gado,
_Dan Allah ina son yin magana dakai Abban Aryan amma ina so kayi min kyakkyawar fahimta…._
Shine abinda yaga Hanan ta turo masa,dan yatsanshi yakai bakinsa yana shafa lips dinsa,magana to wacce irin magana take son yi dashi? Kodai har yanzu bata saduda bane ta rungumi k’addarar ubangiji,
_Ok,ina jinki._
Dama tasan amsar dai bazata wuce haka ba tunda shi kamar dogon bayani wahala yake bashi,sake gyara kwanciyar ta tayi ta tura masa da reply kamar haka,
_Dan Allah kana shan giya ne?._
Ganin sakonta yasashi bude idanuwanshi sosai sannan ya tura mata da,
_Zo ina son ganinki._
Gabanta ne taji yafara faduwa jin wai tazo yana kiranta,a tsorace tasaka rigar saman kayan baccinta sannan ta yafa mayafi ta fita,wata iskace mai sanyi da dadi ke kadawa sannan ga sararin samaniya yayi kyau taurari sun kara masa ado da k’awa, ta samu damar ganin hakanne dalilin fitarta kuma dan gaban corridor din da zai sadaka da sashen Khalil open ne babu roofing awurin shiyasa zaka samu damar ganin sararin samaniya,
Tamkar marar gaskiya haka ta shiga falon nasa wanda yake shiru dan babu kowa aciki,Allah ya sota ta taho da wayar ta da bata san yanda zatayi ba,text ta tura masa cewar gata tazo tana falo,kimanin mintuna biyu taji motsin fitowarsa,kallo daya tayi masa ta sunkuyar da kanta kasa, sanye yake da kayan bacci na maza white colour riga da wando masu santsin gaske,
Zama yayi a opposite dinta yana rike da wayarshi,
“Kika ce ina shan giya ko me?”
Shiru tayi tana wasa da yan yatsunta,
“Ba kiji ne?”
Dago kai tayi ta kalleshi nan taga idanuwanshi kyarr akanta ya tallafe kumatunsa gaba daya da hannuwanshi,
“Ina ji….”
“Waye yafada miki ina shan giya…?”
“Babu kowa…”
“To meyasa kika yimin wannan tambayar?”
Duburburcewa taso yi saboda tambayoyin nasa na neman yimata yawa to abunka da kwararren tsohon dan jarida,
“Meyasa kika yimin wannan tambayar? Kin taba ganina ina Shane ko kin taba ganina acikin maye?”
Girgiza kai tayi alamar a’a,
“To why did you asked?”
“Gani dama nayi dazu a office dinka acikin fridge….”
Shiru yayi yana kallonta baice komai ba har saida ta fitar da tsammanin zaice wani abu sai kuma taji yace,
“To abinda kika gani ba giya bane,lemo kika gani saboda ni babu abinda ya hadani da giya banko taba dandanata ba bare insha,ki rinka tabbatar da ingancin magana kafin kiyi comment akanshi…… Bakauyiya kawai kinga lemo kince giya”
Duk da bata gane ayanayin da yayi maganar ba shin cikin bacin raine ko sabanin haka ita dai hakuri ta fara bashi,
“Kayi hakuri bazan kara ba”
Sai da ta sake maimaitawa sannan yamike yana fadin,
“Is alright”
Fita yayi tabi bayansa,shi dakin Aryan ya hara ita kuma ta wuce nata tana jin nutsuwa na saukar mata, murmushi tayi da tuno sunan da ya kirata dashi wai bakauyiya gaskiya taji kunya dan tabbas kam bata karanta sunan lemon ba kawai dai taga kwalba kuma green an kawatata,ashe dan Allah wai lemo ne dole ne yace da ita yar kauye.
***
Yau ne su Hanan ke yin Pop dinsu ranta fari tass taje ta karbo certificate dinta wahala dai ta kare hutu zai samu zata huta da wannan gayyar fita PPA da CDs dinnan masu hana mutum isasshen bacci,hotuna suka sha Sosai ita da friends dinta yan batch dinsu wadanda suka gama tare da ta dawo gida ma sunyi da Aryan yafi kala ashirin,shima uban gayyar lokacin da takai masa certificate din “congratulations” yace da ita kadai.
Bayan kwana biyu da gamawar su kuma duk sai taji babu dadi domin tayi bacci har ya isheta wuni take yi tana bacci yanzu har takai minzalin da ko baccinma bai fiya daukarta sosai ba,
Satinsu biyu da gama service tana daki tana gyara wardrobe dinta umma ta shigo mata agigice cikin tashin hankali da dimuwa hannunta aka………………….鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:12 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*31*
***Sake gigicewa tayi ta rikice ganin umma na hawaye tuni jikinta ya dauki rawa dan tasan babu ko tantama mutuwa akayi kuma abu mai yuyuwane kila ace minister ne ya mutu,
“Umma waye ya mutu? Shikenan ya mutu….”
Goge hawayenta umma tayi cikin damuwa da yanayin dimuwa tace,
“Ba mutuwa bace amma har gara mutuwar Allah na tuba, Aryan ne ba aganshi ba tunda aka tashi daga makaranta wai ance wasu ne sukaje suka daukoshi daga makarantar wadanda ba asan ko su waye ba…..”