MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

“Innalillahi…..” Hanan ta fada gaba daya idanuwanta awaje,haba shiyasa taji shiru bai dawoba aranta har tana cewa ko kuma dai yadawo ita dince bai shigo wurinta ba,
Hawaye take son yi amma tashin hankali ya hanata sai yau ta tabbatar da cewa yaron yashiga ranta fiye da tunanin ta domin jin numfashinta take yi kamar zai dauke,
Fita umma tayi ita kuma ta samu gefen gado ta zube bayan ta kifa kanta, innalillahi kawai take ambata ahaka taji anbanko kofar d’akinta anshigo kafin ta daga kai taga waye taji anshakota,
Khalil tagani tamkar wani mahaukaci saboda yanda duk ya furgice ya rude, bata taba sanin haka ya iya fada da daga murya ba sai yau,
“Da sa hannunki acikin b’atan d’ana ko babu…..?” Yafada yana jijjigata kamar zai ballata idanuwanshi aburkice kamar wanda yasha wani abu,sake rikicewa tayi ta gigice tama rasa amsar da zata bashi,
“Dake nake magana,nace da sa hannunki cikin batan yarona?” Yasake fada cikin karaji,
Girgiza kai tashiga yi muryarta na rawa,
“Wallahi tallahi ban san komai ba akai Abban Aryan, wallahi babu hannuna, taya za ahada baki dani acutar da Aryan….”
Sake wujujjugata yayi sannan cikin kausashasshiyar murya yace, “Wallahi idan har bincike na ysnuna min cewa akwai sa hannunki sai na kasheki…..”
Daga haka ya hankadata kan gado yajuya yafita da sauri gudu gudu,sai lokacin ta samu damar fashewa da kuka ai daga ganin yanda yakeyi kasan yashiga rudu jifa harda maganar kisa,kuka take yi sosai,
Shima Khalil yana can anbaza jami’an tsaro kowanne lungu da sako dake cikin garin, yan gombe kuwa tuni labari yaje musu wai ansace Aryan,sai wayar umma da Hanan ake kira amma duka wayoyinsu akashe shi kuwa dama Khalil ba asamu call forwarded wayarshi ke nunawa.
Har magriba gidan tsit kowa yana cikin daki abun duniya ya isheshi daga ita har umma babu wanda yaci koda kwayar abinci haka shima Khalil yana can yanata yawo daga nan sai nan har gidansu principal din Aryan yaje yace Wallahi idan dansa bai fitoba sai yarufe wannan makarantar tunda har cikin makaranta akaje aka sace Aryan bawai fitowa yayi wajeba,shi dai principal hakuri kawai yake bashi yana cewa insha Allah Aryan zai bayyana,masu gadin makarantar kuwa da securities sunsha tambayoyi kamar babu gobe dan tambayoyin da Khalil ya tsaresu yana yimusu ko agaban alkali ba lallai ayi musu itaba,Emah kuwa ranar yaga tashin hankali saboda shine drivern Aryan shine ke kaishi school yadawo dashi saboda shi PA abubuwan sunyi masa yawa, Emah sai da yaji kamar ya gudu kauyensu dake can anambra state kawai dai dan yasan ko ya gudune oga sai ya nemoshi shiyasa ya zauna amma daga lokacin da yaje dauko Aryan bai ganshi ba zuwa yanzu ya zagaya bandaki yafi sau goma.
Hanan tana d’akinta ta idar da sallar ishah lokacin misalin karfe 11 na dare umma ta shigo wai tazo suje asibiti ankwantar da Khalil baida lafiya hawan jininsa ya kada shi,
Wani tashin hankalin hankula suka sake shiga domin Khalil baya ko gane wanda yake kansa dayake hawan jini shima akwai kisan mummuke,daren yau dai yanda suka ga rana haka suka ganshi Hanan tayi kuka har ta gaji,
Washe gari da sassafe su hajiya suka bayyana a asibitin kowa jikinsa a sanyaye kuma fuskarsa dauke da alhini,kamar masu zaman makoki haka suka zama,shi kuwa Khalil yana can Dr Al’amin yana fama dashi dan acewar Dr nisan kwana ne da Khalil amma da ace mai kararren kwana wannan ciwon yasamu to da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba,
Kwanansa biyu a asibitin sannan ya dan farfado duk da baya gani yadda ya kamata haka kuma jinsa ma ya danyi kasa amma ahakan yake son wai sai yatashi yatafi neman Aryan, Zaid ne ya rirrikeshi yace yayi hakuri shi zaije neman nasa yanzu, Zaid yana fita yasake yunkurin tashi ta hanyar riko Hanan wacce ke zaune gefe,
“Karki barshi yatashi…. Idan yatashi faduwa zaiyi” Anty saudat ta fada sannan ta fita daga cikin dakin,
Riskeshi Hanan tayi ta mayar dashi ta kwantar kwalla tana fita daga cikin idanuwanta,
“Kayi hakuri Abban Aryan insha Allah, Allah zai bayyana shi,mutane sunata addu’a suma kuma jami’an tsaro suna iyakar bakin kokarin su dan ko dazu saida ministan tsaro yazo yace afada maka ka kwantar da hankalinka kaci gaba da addu’a insha Allah suna gab da samo Aryan……”
Lumshe idanuwanshi yayi wasu zafafan hawaye suka zubo masa duk sai Hanan taji tausayinsa ya kamata saboda duk abinda zaka ga babba yana kuka to abin ba karami bane, lallabashi aka yita yi har yasamu bacci,
Aranar abbanta shima yazo ya jajanta musu dama kuma mutane nata zuwa kamar anyi musu busa,asibitin kullum cika yake dam da matasa da manyan mutane sai yanzu ta sake tabbatarwa da cewa Khalil mai jama’a ne kuma ana sonsa shiyasa idan Allah yabaka dama to kayi iya bakin kokarin ka wurin kyautatawa mutane dan tayuyu zaka bukacesu agaba sai suma su taimakeka a lokacin da kake neman taimakon da kudinka baza suyi maka ba dan wani taimakon kudi bai isa yayi ba sai dai jama’a ce zasuyi maka.
Kullum cikin garin Abuja sake baza jami’an tsaro ake sannan gaba daya kafafan yada labarai koda yaushe maganar batan Aryan ne to abunku da dan masu abun,shi kuwa Khalil ya dan fara samun sauki sakamakon ruwan zamzam da Abban Hanan yasa aka nemo ya hada masa maganin hawan jini na musulunci gaskiya zamzam maganine sosai kuma sadidan. Cikin Kashi dari kashi 70 na hawan jininsa ya sauka dan tangararau yake ganin komai yanzu sannan kuma yana jin komai radau kamar da sai dai tarin damuwa dake sakashi zubar da hawaye da rashin cin abinci,idan yatuno Aryan yana hannun wadanda ba asan ko su waye ba sai yaji kamar ya hadiyi zuciya ya mutu dan bacin rai, damuwarsa bai san inda yaronsa yakeba bai san wanne hali yake cikiba sannan bai saniba ko yana raye ko ya mutu shi idanma mutuwarce to har gara Aryan ya mutu agabanshi yakaishi ya binne hankalinsa zaifi kwanciya akan ace bata yayi gaba daya, wannan al’amari shi yake sake daga masa hankali har baya kunyar zubar da hawayensa agaban koma waye dan da yan jarida suka zo asibitin domin ganawa dashi kasa cewa komai yayi inbanda kwalla da yayita fitarwa sai fitar da yan jaridar akayi daga dakin,gashi ko bacci baya samu sai idan allura Dr Al’amin yayi masa shine zai dan samu bacci akalla na awa shida zuwa bakwai,
Yau kam saida safe yasamu baccin saboda jiya da daddare kasawa yayi duk da cewa anyi masa allurar, Hanan na zaune kasa kan sallaya tana kallonsa wallahi duk tausayi yake bata idan ta kalleshi dama shi ba jiki ba kuma gashi yasake ramewa cikin kwanaki hudu kacal,yana sanye da farar t shirt da bakin jeans duk yasake zama yaro sakamakon ramar da yayi,ahankali taga ya bude idanuwansa sai kuma taga ya mayar dasu ya rufe hawaye na zirarowa ta gefen idonshi,
Tashi tayi ta matsa gaban gadon ta durkusa akan gwiwowinta ta kai hannu kan nashi wanda ke soke da cannula ajiki,bai bude idonsa ba kuma bai motsa ba,kwantar da murya tayi koda yake dama muryar tata akwance take sakamakon kukan da itama ta shassha,
“Dan Allah Abban Aryan kayi hakuri muci gaba da addu’a insha Allah Aryan zai bayyana kuma baza su samu ikon cutar dashi ba domin yana tare da kariyar ubangiji…..”
Shiru tayi tana sake zuba masa ido ji take yi kamar ta rungume shi ajikinta taci gaba da rarrashinsa kamar jariri,jin za abude kofa ashigo yasata dan matsawa, Khalid ne yashigo shima hankalinsa duk yatashi dan shi bai san hakan tafaru ba sai jiya da daddare dama matsalar zaman nesa kenan sai ayi abu agida kai baza ka ji ba shiyasa har gobe yake takaicin zaman Calabar dinnan da yakeyi domin abubuwa da dama baya sanin anyi sai yazo yake ji,