MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

Zuwan Khalid dinnema yasa Khalil ya dan samu saukin damuwarsa kasancewar wani lokacin childhood friend dinka yana da abubuwa daban daban wad’anda zai yimaka har yasamo kanka,duk da dai akwai damuwar amma ya dan ji saukinta.

Bayan sallar la’asar kawai sai ganinsa suka yi yafito daga cikin dakin da yake kwance yana bacci,kowa tashi tsaye yayi har securities dinsa, Khalid ya kalla,

“Bani aron key din motarka zanje wani wuri indawo….”

Kowa dake wurin zaro ido yayi nan aka fara tambayar ina zashi? Hajiya kuwa tiburewa tayi tace babu inda zaije idan kuwa ya dage sai ya tafi to dole yatafi da masu kula dashi shi kuma yace A’a,dafashi Khalid yayi yace,

“Haba Khalil…. Ina zaka je acikin wannan halin kuma? Kafa san yanda kuke koda yaushe mutane suna fakonku….. Dan Allah ka koma ka kwanta”

Hannun Khalid yaja suka shiga dakin mintuna biyu suka sake fitowa,

“Hajiya babu matsala insha Allah kubarshi yaje yadawo din…” Khalid yafada cikin kwantar da hankali,

Duk da haka dai hankula basu kwanta ba da fitarsa shi daya nan suka dunguma suka bishi har harabar asibitin inda yashiga motar Khalid mai dauke da bakaken gilasai,yafita daga cikin asibitin kamar zai tashi sama saboda yanda yake sharara gudu,zuba ya hara cikin kankanin lokaci ya isa yana tuki yana duba wayarshi yana bin direction din da aka bashi har ya isa wani hamshakin tangamemen gida,horn yayi wasu garada su kimanin guda biyar suka zo suka bude dukkaninsu fuskokinsu rufe da mask, ahankali yatura hancin motar tasa ciki sannan yayi parking yafito,

Sakashi suka yi atsakiya suka yimasa jagora har cikin wani kerarren falo mai dauke da Royal furnitures,juyawa sukayi suka fita yarage saura shi daya acikin falon,

Minti biyar yana tsaye hannayensa cikin wandon jeans din dake jikinsa yaji wani azababben kamshi yasoma ziyartar hancinsa ahankali cikin takun jan hankali da kasaita ta bude kofa tafito tana taunar cingum,

Daga idonsa yayi ya kalleta tana sanye cikin kayan bacci na daukar hankali farare tatas wadanda babu abinda suka boye na daga kyakkyawar surar da Allah yayi mata,doguwar rigace iya gwiwa da yar top dinta asama wacce ta tsaya iya kirjinta,

“Yesmin……” Yafurta akan labbansa,

“Barka da zuwa fadata mai girma minister…..” Ta fada cikin jan hankali tana kokarin zama kan daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya,

“Yesmin…… Ina kika kai min yaro na?” Ya fada fuskarshi babu rahma ko kadan,

“Karka damu yaronka yana nan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali….. Babu abinda ya sameshi”

“To me kike nufi da hakan da kikayi? Me kike bukata daga gareni?” Ya bukata cikin bacin rai domin tuni hakan ya bayyana akan fuskarshi,

“Yawwa sai yanzu kazo gabar da najima ina son kazo….” Mikewa tsaye tayi tana karairaya da salo na jan hankalin duk wani da namiji mai cikakkiyar lafiya,

“Abinda najima ina so daga gareka tsawon shekara da shekaru…..”

Marairaicewa tayi harda kwallar karya da yaudara,ta matsa dab dashi kamar zata rungumeshi,

“Dan Allah Khalil kaji kaina….,ka taimaka min kada ciwon sonka ya zama ajalina…..pls….pls”

Juya mata baya yayi domin yasan idan yaci gaba da kallonta ahaka za a iya samun matsala domin tausayin ta zai iya shigarshi shi kuma baya son yaji tausayin ta adaidai wannan lokacin,

“Yesmin abinda najima ina fada miki yau ma shi zan sake jaddada miki…. Bana zina ban taba yinta ba kuma bana sha’awar inyi har tsawon karshen rayuwa ta…. Ina yarona yake? Kifito min dashi dan shine yakawo ni bawai bukatar ki ba….”

Dan lumshe idanuwanta tayi sannan ta budesu akanshi wannan fa wani lakani ne aka jima da bata akanshi kuma dole sai yayi zina da ita sannan maganin zaiyi tasiri har yayi aiki gashi wannan itace damarta ta karshe idan har hakanta bai cimma ruwa ba to komai zai rushe,

“Gashi can cikin wancan dakin….”

Ta nuna masa dakin dake kusa da wanda tafito daga cikinsa, Cikin jarumta da rashin tsoro ya dirfafi dakin,

“Sadauki…”

Tafada ahankali tana kokarin bin bayansa wannan yana daya daga cikin abubuwan da ke kara ingizata duniyar son taga ta mallakeshi domin baida tsoro ko kadan ga nuna shi namiji ne agaban ko waye,

Cikin kwarin gwiwa Khalil yabude kofar dakin yashiga mai dauke da duhu dan kamar ba a halicci haske ba aduniya haka dakin yake,laluben makunnar hasken dakin yafara yi amma yarasa sai shashimawa yakeyi yana kiran,

“Aryan….. Aryan”

Haske ne yaga ya gauraye dakin cikin sauri yajuya ya kalli kofa,yesmin yagani tsaye tana rike da key din kofar dakin sannan ta cire yar rigar saman rigar baccinta gaba daya kirjinta yafito fili ta yar raga ragar dake saitin kirjin rigar,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un….” Yafada yana juya mata baya, murmushi tayi ta kai hannu zuwa ribon dinta dake daure da yalo yalo gashin kanta nan tacire ribom din ta jefar ta baza gashin nata ya sauka saman kafadarta,takawa tafara yi ahankali tana dosarsa maganganun malaminta na sake fado mata “Sai kin yi zina dashi tunda bai taba yin zina ba sannan bukatarki zata biya…” Lumshe idanuwanta tayi cikeda kwarkwasa takai hannu zuwa gareshi………………….鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:13 AM – Ummi Tandama: Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.

*32*

       ***Dafa kafadarshi tayi sannan cikin sanyin murya mai dauke da tsantsar yaudara yaji tace,

“Wai meyasa kake guduna ne Ibrahim? Gaka dai ahaka kamar wayayye….. Kana da kudi,kyau, kuruciya uwa uba ga mulki to meyasa bazaka more rayuwarka kaji dadi ba? Sai yaushe ne zaka waye? Idan baka huta yanzu ba sai ka tsufa ko yaya?”

Lumshe idanuwanshi yayi domin tab’ashin da tayi ji yake yi kamar ta watsa masa garwashin wuta ajikinsa,

“Yesmin….. Ki nuna min inda yarona yake kawai domin ni ba wannan ne ya kawoni ba…”

Rigar baccin dake jikinta ta soma sabulewa tana kokarin shan gabansa,

“Me kake ci na baka na zuba? Zaka ga yaronka amma har sai nima ka amince da bukata ta…”

Bude idanuwanshi yayi da zummar balbaleta da fada amma abinda idanuwanshi suka gane masa yasashi saurin runtse idanuwanshi yana furta,

“Wa’iyazubillahi…. Yesmin dama bakida hankali? Ke wacce irin sakarya ce?”

Rabon da yaga sankaceciyar budurwa tsirara har yamanta sai yau da yayi mummunan gani sanadiyyar ta,

Kokarin rungumeshi take yi yayi gaggawar matsawa nan ta sake matsowa yasake matsawa bata hak’ura ba ta sake yunkurin matsowa bai san lokacin da ya dauketa da wani gigitaccen mari ba abunka da bahago bai iya duka ba shiyasa sai da taga wasu taurari sun gilma ta idanuwanta sannan taji jinta ya dauke na dan lokaci, kuncinta ta dafe tana kallonsa cikin mamaki da bacin rai,

“Ibrahim ni ka mara? Dan kawai na nuna soyayya ta agareka?”

“Na mareki….. Ai kadanma kika gani tunda ke wawiya ce dakikiya marar tunani… Ina yarona yake? Wallahi idan baki fito min dashi ba sai nayi miki dukan kawo wuka,sai nayi shari’a dake ke saima na kasheki……sai nayi ajalinki…..”

“Ka fita waje zaka samu yaronka acan amma ka sani Wallahi sai kayi nadamar abinda kayi min….sai ka san ka mareni kuma ka wulakanta ni”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button