MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

Bai sake tanka mata ba yawuce ta yafita tare da bugo kofar dakin da wani mugun karfi,abakin kofa yaga biyu daga cikin garadan nan na dazu masu kama da samudawa,wani mugun kallo yayi musu sannan ya ratsa ta tsakiyarsu yawuce yana kaiwa tsakiyar falon yaga Aryan yataso da gudu yazo ya rungumeshi yana kiran,

“Daddy…. Uncle….”

Rungumeshi shima yayi sannan ya durkusa gwiwowinsa akasa yana dudduba jikin Aryan din,

“Abba na babu abinda suka yimaka? Sunyi maka wani abu?”

Jijjiga kai yayi yana sake makalkale Khalil,daukarsa yayi yajuya ya kalli bakin kofar dakin nan yaga yesmin tsaye tare da garadanta tana yimasa wani kallo mai cike da ma’anoni kala kala,fita yayi yabude motar da yazo da ita ya saka Aryan sannan ya bude side din driver shima yashiga ya zauna yayi reverse da mugun gudu yafita yabar gidan,

“Aryan ya akayi ka bari suka sace ka? Haba Aryan kaida nake ganinka kamar mai wayo ashe bahaka bane….”

“Daddy da aka tashi daga school ne sai naga mota irin tamu kuma wani mai kamada Emah yazo yakama hannuna shine nabishi muka tafi…..”

“Kaima dai soko ne Aryan,you are such an idiot….daga ganin mutum sai ka bishi? Suna baka abinci kana ci?”

Kai ya daga babu bakin magana duk ya tsure dan yasan watakila sai Khalil ya zaneshi saboda duk wannan soyayyar da yake yimasa fa idan yayi laifi babba to rufe ido yake ya zaneshi da belt shiyasa tun yanzu tsoro ya darsu a zuciyarsa dan yasan zaisha duka.

Can asibiti kuwa hankula sun sake tashi domin anata kiran wayar Khalil baya dagawa kuma gashi shiru shiru bai dawo ba, hajiya fadi take,

“Sai da nace yaron nan kar yadauki motar nan ya fita amma ina sai da yafice…. Ko meyasa yakeda taurin kai oho”

Suna tsaye carko carko kowa na fadin albarkacin bakinsa Khalid ya koma gefe ya dauki wayar da Khalil ke yimasa,

“Ya andace kuwa?”

“Ehh gashi na taho dashi dagaske ai itace ta saceshi,ku tattaro ku taho gida kawai…”

Katse wayar Khalid yayi yakoma wurin su hajiya yace suje su tafi gida shima khalil din ya tafi gida ansamo Aryan dan tare suke nan sukaje suka dudduru amota suka nufi gida tare da securities dinsa. Shi kam tun daga zuba yake haduwa da jami’an tsaro amma da zarar sun tsayar dashi yana sauke glass idan sukayi ido hudu sai su matsa gefe suna fadin “sorry sir” 

Duk mamakin ganinshi shi kadai sukeyi ba tare da securities ba gashi mugun gudu yake yi dan shi sam bai iya jan mota a hankali ba gudu yake kamar zai tashi sama,

Yana zuwa gidansa kuwa wani uban horn yashiga zubawa duk yabi ya cikawa masu tsaron kofar kunne sukuma basu san shi bane, full light yayi ya haskesu hakan ya kular da ben daya daga cikinsu ya taso da sauri yana gyara zaman bindigarsa akafadarsa alamar zaiyi rashin mutunci,tun kafin ya karasa Khalil ya sauke glass din zuwansa keda wuya yaga Khalil idonshi na kallon gate din yana mamakin wannan lamari wai shi da gidansa amma anbarshi yana jira sai sun gama shuka rashin mutuncinsu sannan zasu bude,

Da gudu ben yaje yabude gate din sannan ya matsa gefe yana neman afuwa, Khalil baiko kulashi ba ya saka hancin motar zuwa cikin gidan,shi kuwa ben alama yarinka yiwa sauran da baki wai ogane fa da kansa a wannan motar,

Yana kokarin fitowa daga cikin motar bayan yayi parking securities din suka karaso suna yimasa sannu da zuwa da tayashi murnar bayyanar Aryan wanda yafito rike da school bag dinshi,

Ciki suka shiga yawuce part dinshi Aryan na biye dashi,

Yana bathroom yana wanka su hajiya suka shigo dukkaninsu sashen Khalil suka shiga har Hanan ganin Aryan aka shiga yiwa juna barka da taya juna murna,a lokacin Hanan taje tayi masa wanka tasako masa kananan Kaya har lokacin suna part din Khalil acikin falonsa sai ciye ciye akeyi cikin farin ciki,

Khalil ta kalla yana sanye da jajayen jersey da dogon wando da juice a hannunshi yana kurba,kan cinyar Khalil Aryan yaje yahaye ya zauna ana shan hira ohhh wai yau sune cikin farin ciki haka kamar ba sune kwanaki biyu da suka gabata suke cikin damuwa da zubar da hawaye ba. Raba dare suka yi a b’angaren Khalil dan ita kam Hanan saima tafiya tayi ta barsu lokacin karfe 11 na dare,wanka tasamu tayi da ruwa mai dan zafi sannan ta saka rigar baccinta ta kwanta,

Su hajiya kuwa har wurin 1 na dare suka kai daga bisani suka tafi suka bar Khalil da Khalid, kallon Khalil Khalid yayi yace,

“Malam ni zo ka nuna min nawa makwancin nima inje insaka hakarkarina dan gobe asubanci zanyi inbar garin nan…. wallahi hutun kwana daya kacal suka bani…”

“Ga bedroom nan kana gani kaje ka kwanta mana…” Khalil ya fada yana nuna masa da hannunshi,

“Dan Allah ni ka kaini dakin da zan kwana,ya zaka nuna min master bedroom dan wulakanci? Idan matarka tazo fa…. Kasan kai babban mutum ne sai dai abiyoka”

“To nidai bani da wani dakin idan ba wannan ba…”

Tashi Khalid yayi yana kokarin cire rigar jikinsa yanufi cikin dakin yana fadin,

“Ni dai nashiga ciki idan zaka takura kuma saika bakunci dakin matarka”

Banza Khalil yayi dashi yaci gaba da danne dannen wayarshi. Bayan wasu mintuna da shigar Khalid shima yatashi yashiga,kwance yasamu Khalid yana waya da matarsa Muneerat sai wani lankwashewa juna murya suke yi tamkar saurayi da budurwa,

Gefen gadon yasamu ya lallaba ya kwanta kanshi yana dan sara masa Allah sarki Ramlat yanzu da tana raye da shima yana da gata irin gatan da duk wani magidanci yake samu idan har ya amsa sunan dan gata awurin matarsa,

Abubuwane suka shiga dawo masa kamar yaune suke faruwa,tuno lokacin da suke samari yashiga yi Khalid haka zai raba dare yana waya da budurwa shi kuma abinda bai iyaba kenan dan sam baida jimirin yin waya sai idan ta zama dole amma zai iya wuni yana chaten ta waya yafi yimasa sauki akan yayita magana,yanata tunane tunanensa shi dai ahaka bacci ya d’aukeshi yabar Khalid yana ta fama, dayake rabon da yasamu bacci mai dadi tun gabannin sace Aryan shiyasa yau ya nutsu yayi daga shi har Khalid din da yake ta kurin zaiyi asubanci duk makara suka yi dan har aka fito daga masallaci basu saniba,koda Khalil ya farka tuni gari yayi haske fayau sai dai shi nasa dakin kamar dare, fitilar dakin ya kunna ya mike yashiga bathroom yayi wanka sannan yayi brush da alwala yafito rike da dan karamin towel yana sake goge jikinsa,

“Khalid…… To sai ka tashi ai kayi salla ko har yanzu ana nan dai hali bai canja ba? Ka raba dare kana soyayya kuma ka kasa tashi sallar asubah….. Kanata cika bakin asubanci zakayi waye waye ni dama kawai jinka nake yi ai”

Tashi Khalid yayi yawuce cikin bathroom,sai da yayi wankan shima sannan yafito saboda ason samunshi yana yin salla zai wuce,jam’i suka yi duk da sun makara bayan sun idar Khalid yace,

“Ranka yadade ni baka karasa sanar dani abinda yafaru ba jiya ina gama waya naga har kayi bacci….”

“Khalid Wallahi yarinyar nan a daki ta sakani ashe wai wayo zata yimin tace Aryan yana ciki ashe karya take,intakaice maka labari dai wallahi niked tayi agabana…… Dakyar na kwaci kaina”

“Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,ai wasu matan hatsabibai ne nake fada maka,makirci dama ta shirya sai dai Allah ya cigaba da tsareka daga sharrinsu….”

“Amin Khalid ni wallahi narasa gane da me nafi sauran naza da kowacce mace ke kawo min farmaki,kaga idan office naje suna biye dani,idan kasar na bari suna biye dani duk inda naje suna bina…… Ni Wallahi mulkin nan duk ya isheni baida wani dadi ko kadan sai tarin stress da wahalhalu”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button