MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

“A’a ka daina fadin haka,mulki fa Allah ke baiwa wanda ya zaba kuma yaso,kai dai kaci gaba da addu’a… Amma ya kamata ka dauki mataki akan yarinyar nan gaskiya ko dan saboda gaba”
“Ehh akwai matakin da zan dauka amma ina sone inyi magana da lawyer dina first inyaso sai inji shawarar da yake ganin yadace mubi….”
Wayarshi ya dauka yana duba time 6:30, text ya turawa Hanan akan ta kawowa Khalid breakfast tafiya zaiyi,
Allah yaso ta tashi kuma wayarta a kunne take,sauka tayi zuwa kitchen ta samu john na ta aiki yana soya dankali sannan gefe daya yana hada vegetables sos, diban wanda ya tsame tayi sannan ta harhada masa sauran kayan tea ta dauka ta haura sama,a bakin kofa ta jira bayan tayi knocking domin har yanzu bai bude kofar ba,fitowa yayi yazo ya bude mata tawuce ciki yana biye da ita,kan dining table ya nuna mata taje ta dora kayan sannan ta juyo ta dan kalleshi yana kokarin kunna tv da remote a hannunshi,
“Ina kwana?”
“Lafiya lau…..”
Juyawa tayi zata fita taji muryar Khalid yana cewa, “Madam mun saki fitowa da sassafe ko?”
“Lahh ai babu komai,ina kwana?”
Suna gama gaisawa tayi waje domin Khalil sai daddaure fuska yake yi dan baya son Khalid yayi masa baran barama ya jawo masa reni,
Aranar suma su hajiya suka tafi gombe,duk da anga Aryan Khalil bai fitaba dan Dr Al’amin har gida yazo ya dubashi yace ya dan bari tukunna har sai yakara warwarewa,
Manena labarai da yan jarida har gida suka biyoshi suka ji ta bakinsa dangane da batan Aryan da kuma yanda akayi aka ganshi,bai fito fili yasanar dasu yanda aka ganshin ba kawai dai ya basu tabbaccin cewa masu yin garkuwa da mutane ne suka saceshi kuma yana kan yin bincike dan gano ko su wanene,bayan tafiyar yan jarida ya kira emah yasake tsareshi da tambayoyi domin Aryan yace wani ne mai kama da Emah din yazo ya kama hannunshi yakaishi mota to shikuma wannan din yake son gano ko waye saboda yanzu duniya ba abar yarda bace kana tare da mutum sai a iya hada baki dashi a cutar dakai, sai da yagama yiwa emah tambayoyi masu kada masa yan hanji sannan ya sallame shi yatafi yana fita ya danko kunnen Aryan guda daya har cikin bedroom dinshi belt ya dauka yana tambayar shi,
“Nan gaba zaka kara bin wanda baka saniba? Zaka kara bin mutumin da baka san ko waye ba?”
Girgiza kai Aryan yayi yana fadin,
“Allah Daddy bazan sake ba….”
Zaneshi yayi sannan ya sakeshi, cikin fad’a yace,
“Get out of here wawa kawai….”
Fita Aryan yayi yana kuka yatafi wurin Hanan, bata taba ganinsa yana kuka haka ba sai yau tunda tazo gidan,daukarsa tayi tafara lallashinsa tana tambayar meya sakashi kuka,
“Uncle ne ya….zaneni….”
Gwalalo ido Hanan tayi dama Khalil yana dukansa? Tohh ashe dai duk soyayyar yana daukar mataki, rarrashinsa taci gaba dayi har yayi shiru bacci ya d’aukeshi. Tana can wurin umma suna hira Aryan yasauko yazo ya hau jikinta duk jikinsa zafi alamar zazzabi, daukar shi tayi ta nufi sashen uban dashi,samunshi tayi zaune da laptop dinshi kan glass table agabanshi yana aiki, wannan mutum dai ko shine agogo sarkin aiki sai haka dan koda yaushe cikin aiki yake,
Daga ido yayi ya kallesu itada Aryan wanda ya kwantar da kai a kafadarta,
“Ka taba jikin Aryan kaji kamar zazzabi yake yi…..”
Mika hannu yayi ya karbeshi,
“Na zaneshi ne shiyasa watakila zaiyi zazzabin….”
Shiru tayi bata ce komai ba ta tsaya tana kallon su yana ta tattaba jikin Aryan yana fadin,
“Am sorry lovely son, zazzabi ne ko? Bari inkira Dr yazo yabaka magani kaci abinci?”
“Baici abincin ba,yanzun nan yatashi” Hanan ta bashi amsa dan tasan Aryan cewa zaiyi yaci saboda baya son cin abinci,
“Ok je ki kawo masa”
Fita tayi shikuma yakira Dr Al’amin ita dai tana ta mamakin Khalil saboda a tsananin son da taga yana yiwa Aryan to bata taba tsammanin Wai zai iya saka hannu ya dakeshi ba. Zazzabin kwana biyu Aryan yayi sannan yakoma school domin yawarke garau haka shima uban ya warware domin har ya soma fita office.
A ranar da yamma mummunan labari ya sameta wai wata matashiya takai Khalil kara babbar kotu akan yunkurin yimata fyade adaren ranar larabar da ta gabata……………………..鉁嶏笍
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM – Ummi Tandama: *33*
***Tsoro,mamaki da kuma damuwa sune suka taru suka rufe Hanan lokaci guda,jin wai wata matashiya takai Khalil kara kuma da laifin yunkurin yimata fyade kai jama’a wannan abu da me yayi kama,
Rasa abinda zatayi tayi kawai sai ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tayi tagumi,to shin dagaske ne kodai sharrine kawai wannan matar take kokarin yimasa dan dukda cewa ita bata wani zauna tare dashi na tsawon lokaci ba amma sai taga kamar baida lokacin aikata hakan,shiru dai tayi da bakinta bata ce komai ba sannan kuma babu wanda ta fadawa ahaka Aryan yashigo ya sameta yadawo daga makarantar yamma wato islamiyya wadda shi agida ake yimasa tashi,
Kafin kace me tuni labari ya karade kafafan yada labarai wai Khalil yayi yunkurin yiwa yesmin fyade agidanta dake can zubah, nanfa wad’anda basu sanshi ba suka fara Allah wadai dashi wadanda suka sanshi kuma suka fara karyatawa suna fadin ai wannan shaci fadine kawai irin na wasu matan marassa tsoron Allah amma Khalil bazai aikata hakaba dan haka wannan labarin baida maraba da kanzon kurege.
Khalil Kam shi bama ya k’asar dan haka baima san abinda yake faruwa ba yana can Seoul babban birnin k’asar Korea, Khalid ne yaci karo da posting din a Instagram shine yayi gaggawar Kiran Khalil yana tambayar sa, murmushin takaici Khalil yayi zuciyarsa na tafarfasa saboda bacin rai,
“Wallahi wannan karon sai na nemi hakkina awurin yarinyar nan…… Text massage fa tayi min Khalid cewa inje inkarbo Aryan wai yana wurinta kuma kar natafi da securities saboda wani dalilinta marar amfani kuma na yarda natafi ahakan ni daya…. Taje tayita kaiwa k’arar dan Allah karta fasa amma nima yanzu zata ga the other side of me….”
Kitt ya kashe wayarsa cikeda bacin rai saboda yasan zubar masa da mutunci kawai yesmin ke sonyi, so take ta goga masa bakin fenti abanza gashi yan media sam basu iya daukar abuba sai ayita yamididi dakai ana nuna ka kamar watan ramadan, tamkar Khalid ya bude kofar kiran Khalil nanfa yan uwa da abokan arziki suke ta go slow din kiransa daga kiran wannan yashigo sai na wannan,
Bai dauki kiran kowa ba sai na anty saudat babbar yayarshi wacce yake bi,yana dagawa yaji ta rufeshi da fada tana cewa abinda yayi ya kyauta kenan? Yanzu yadace da girmansa da komai arinka buga labarinsa a jaridu da mujallun k’asar nan cewar yayi yunkurin ketawa mace hadddinta? Fada anty saudat take yi ta inda tashiga ba ta nan take fita ba dayake itama mafadaciya ce akwai fada babu laifi, kwata kwata taki tabarshi yayi magana sai zuba masa ruwan masifa take dama shima to afusace yake dan haka ya katse kiran dan ta cika masa kunne da fadanta,
Sake kira tayi tana jin ya daga tafara fadin,
“Ibrahim ni kake kashewa waya? Ni ka katse mawa waya saboda na kiraka ina fada maka gaskiya?”
“To danme zaki kirani ki sakani agaba kina wani yimin fada kamar karamin yaro? Ba zaki tambayeni kiji abinda yafaru ba….”
“Anki atambayeka din…”
“To kar Allah yasa ki tambaya din,duk abinda kikaji akaina ance hakane ina shikenan? Ko da….”