MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

“Kaje kayi fin haka ma idan kaso sunan wa zaka bata? Ba sunanka bane….”

Yana jiyowa daga kusa da ita ana yimata magana kan cewa bai kamata ba wannan abun da sukeyi kamar wasu kananan yara yasan bazai wuce mijinta ba dan kamar muryarsa yaji yana cemata tayi shiru,”Ni baka jin abinda yake fada min? Ba kanina bane shi? Akan me zai rinka gaya min kananan maganganu?”

Shi dai katse wayar yayi yana kokarin ajiye ta kiran lawyer dinshi yashigo wato Barrister muhsin nan ya dauka ya zayyanewa barrister duk abunda yafaru sannan yakara da cewa,

“Barrister nima ashigar min da Kara a nema min hakkina na sace min yaro da tayi har tsawon kwana biyar wanda sanadiyyar hakan har saida ta kaini ga kwanciya a gadon asibiti, sannan a nema min hakkina na bata min suna da tayi…”

“Babu matsala ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai daidaita kuma sai tayi nadamar abunda ta aikata,ai bata san me ake kira da shari’a ba shiyasa har tayi saurin kai k’ara…”. Barrister muhsin yabashi tabbaci sallama suka yi suna gama waya da barrister ya kashe wayar gaba daya bayan ya sakata a flight mood. Kwana biyu da faruwar lamarin ya dawo Nigeria yaci gaba da gudanar da harkokinsa, Hanan na son tambayar sa dangane da rade radin da ake tayi akansa amma bata ga fuskar yin hakan ba domin Khalil wani kwarjini gareshi na musamman idan har ya tsare gida to sai kaji tsoron tunkararsa ko kai waye dan su kansu yan jarida suna ta son suji ta bakinsa amma abun ya gagara.

Dawowarsa da kwana biyu yatafi gombe saboda anshirya family meeting akansa amma iya manyanne babu yara, Abban su Khalid tsareshi yayi da tambayoyi to amma da yake mutum idan da gaskiyar sa baya tsoron amsa kowacce irin tambaya haka ya amsa musu dukkan abunda suka tambayeshi daga karshe tattaunawar ta tashi bayan kowa ya yarda dashi. Daga wurin family meeting din nasu gidansu yawuce duk da sun hadu da su hajiya acan sai da suka sake zama da hajiya suka tattauna sannan yatafi ya koma abuja,

Haka dai labari yaci gaba da yaduwa har aka fara zaman kotu shi dai baya samun halattar zaman kotun sai lauyansa shine ke ruwa da tsaki domin acewar lauya shi Khalil ayyukansa bazasu bari ya samu damar zuwa ya zauna a kotu ba.

Ita kam Hanan zaman gida da rashin sanin takamaimai abinyi sune suka taru suka sakata agaba,wata zuciyar sai tace mata kodai ta koma masters degree dinta ne koda kuwa online ne,gashi yanzu inbanda kwadayin zuwa gida babu abinda take yi tana ta son taje gidansu dan wani lokacin har mafarki take yi saboda tsabar yanda ta saka abun aranta haba aima tana ganin kamar tayi kokari wata tara fa yanzu rabonta da gida tasan da akusa da gida tayi aure ai da tuni taje gida yafi akirga,tana son tambayar Khalil amma tana jin tsoro dan tunda abun nan yafaru yasake zama wani marar son magana,daurewa dai tayi ta rufe ido tayi masa text wai tana son taje taga yan gida,reply yadawo mata dashi lokacin yana wurin wani taro acan garin yola shida mataimakin shugaban k’asa,

_Me akeyi agidan?_

Shine tambayar da taga yayi mata, murmushi tayi aranta tace “wai shi dai mutumin nan baya rabo da tambaya ne? To kawai sha’awar zuwa gidan nakeyi” hakan kuwa ta tura masa amma sai taga yadawo da reply yace wai ba yanzu ba,ranar Hanan harda kukanta au dama haka mata keji idan suka bukaci futa aka hanasu? Wallahi sai yanzu take nadamar zaman gida da tayi ta rinka kunshe kanta agida bata fita ko ina daga makaranta sai gidan anty salaha dama ita ba kawaye gareta ba sai abokan mutunci balle ta rinka yawon bin gidan kawayen,ranar har yajin cin abinci tayi sai uban kuka da tasha dan har agaban Aryan tayi.

Bayan sallar ishah Khalil yadawo gidan, Aryan na dakinsa yana game din zumah a laptop dinshi khalil yafito daga wanka sanye da rigar wanka ajikinsa,

“Papa….. Mommy yau tayi kuka…. Kuma taki taci abinci….. Bata da lafiya”

Dakatawa yayi da goge kanshi da karamin towel da yake yi ya kalli Aryan,

“Jeka ka kirawo min ita….”

Tashi Aryan yayi ya fella da gudu yafita ita kuma tayiwa Aryan wayone da yake tambayar ta wai meyasa take kuka sai tace bata da lafiya ne,tana zaune falo tana kallon tashar Bollywood inda suke haska wani film _Ek villain_ Aryan yashigo yana kiranta,

“Mommy kizo inji Daddy… Uncle ne yake kiranki”

Daga haka yanda take ta mike tabishi saboda doguwar rigace ajikinta yar kanti da bakin siririn mayafi akanta sai kawai ta cire mayafin ta warwareshi ta yafa akanta,

Lokacin da suka shiga a falo ta tsaya bata bi Aryan zuwa bedroom din Khalil ba,agaban mirror Aryan ya sameshi yana fesa turare hannu daya kuma yana gyara sumar kanshi,

“Unlce tazo….. Taki shigowa”

Murmushi Khalil yayi yace “Abbana baki abun magana,akwai ka da surutu yaron nan kamar zaka sauko da sarki daga kan doki,jeka wurin umma tana kiranka”

Shi dai Aryan daukar laptop dinshi yayi yafice,da yaje falonma bai tsaya ba wai Daddy yace yatafi wurin umma,

Tafi mintuna goma azaune bai fito ba Wallahi wannan mutumin da jan ajin tsiya yake da mulki ta raya hakan aranta,bata gama tunanin hakanba taji motsin fitowarsa,farar riga t shirt ce ajikinsa ta kamfanin Nike sai bakin wando jeans kamar yadda yasaba shigarsa amafi yawan lokuta,gaba daya kamshinsa ya karade farfajiyar cikin falon,

“Ina wuni….?” Ta fada kanta akasa,dan kallonta yayi sannan ya amsa,

“Lafiya lau…”

Daga haka babu wanda yakara magana acikinsu har tsawon wasu mintuna,

“Me ya sameki kike kuka? Bakida lafiya ne?”

Jin tambayar da yayi mata yasata girgiza kai alamar A’a,

“Lafiyar ki lau kika zauna kina yiwa mutane kuka?”

Shiru tayi bata amsa masa ba domin tasan ai yasan dalilin kukanta bashine ya hanata zuwa gida ba da ta tambayeshi,tasan Aryan ne zai fada masa cewa tayi kuka,

Shiru yayi yana dan nazarinta kadan,shi baya son ta tafine tabar Aryan domin akwai shakuwa mai karfi tsakaninsu,yanda ta damu da yaron haka shima ya damu da ita,

“Ko akan na hanaki zuwa gidane? Shikenan bari zan kira Abban naki infada masa….”

Nan dinma shirun tayi duk da taji abinda yace wai zai kira abba yafada masa,bata yi magana ba dan haka yace,

“Tashi kije…”

Tashi tayi tawuce tafita,tana fita kuma kamar daga sama taji wata kara taratsatsaaaa gaba daya glass din wurin ya tarwatse awurin ya watsu jikinta babu shiri ta durkushe awurin saboda azaba, Khalil dake zaune a falonshi shima yajiyo karar tarwatsewar glass dan haka da sauri yatashi yafita domin duba abinda yafaru,yana fita yaganta durkushe ga gilasan nan tarwatse awurin da sauri ya nufeta dan ganin halin da take ciki…………………..鉁嶏笍

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:13 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*34*

       ***Kamar acikin mafarki taji ya rikota ya dagota hankalinsa amutukar tashe saboda ganin irin yawan glass din da ya tarwatse,cikin tashin hankali yake furta,

“Ya yanke ki?…… Ya sameki?”

D’aga kai tayi cikeda azaba sakamakon jin glasan da takeyi acikin jikinta,fuuuu taga ya jata zuwa cikin falonsa kuma tun daga cikin falon yasoma cire dan mayafin dake lullube kanta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button