MIJIN MATACCIYA Page 31 to 40

Tiryan tiryan yarinka janta har zuwa cikin bathroom din dake cikin falon domin aganinsa shi yafi kusa fiyeda wanda ke cikin dakinsa duk hankalinsa yagama tashi wanda bata san dalili ba,
Suna shiga cikin bathroom din yasoma cire mata mitsi mitsin gilasan dake wuyanta domin kaifine dasu kamar anfeke ita kanta tana jin radadin shigarsu acikin jikinta kuma sunfi shiga wuyanta da bayanta,lumshe idanuwanta tayi jin yana kokarin cire rigar jikinta,duk sai taji kunya tabi ta dabaibaye ta ganin da gaske cirewar yayi yana cigaba da cire mata glass din,a lokacin da yake kokarin cire mata doguwar rigar jikinta sauran gilasan dake jikin rigar sun zuba cikin farar bra din dake jikinta nan taji shima kirjinta yadauki radadi amma bata fatan azo gabar da zaice nan dinma sai ya cire,shi bama ta jikinta yake yiba ta ganin yarabata da wadannan mitsi mitsin gilasan yake yi domin suna iya kashe mutum har lahira shiyasa bai tsaya wata wata ba yafara kokarin cire bra dinma, hannu biyu tasa ta kare kirjinta bai kulaba yaci gaba da abinda yake yi domin harsu cikin gashin kanta duk gilasan sun shiga kuma ciresu dole saida dabara dan ahakanma gashi nan wurare da dama duk sun dan yanyanketa,
Ganin ya maida hankali kan gashin kanta yana ciccirosu daya bayan daya yasata dan daga ido ta kalleshi nan shima ta hango glass din a wuyansa abinka da farar fata shi har yankan ya bayyana,hannu ta mika tama manta ahalin da take ciki ta zaro glass din, “Kaga ashe kaima ya yankeka….”
Sai da ya tabbatar da ya cire mata su tass sannan ya kalleta cikin sauri ta kare kirjinta da hannunta,kawar da kanshi yayi,
“Kiyi wanka ina zuwa bari zan kira Dr ya dubaki…”
Daga haka yajuya yafita wayarshi ya dauka yabi ta kofar baya yasauka k’asa yana tafe yana yiwa Dr Al’amin text akan yazo cikin sauri yana nemansa,
Securities dinsa na hangoshi lokacin da yake kokarin fitowa nan sukayi saurin mara masa baya,dama shi idan abu yafaru da kansa zaka ganshi yafito,idan kaga Khalil agidanshi zakayi mamakin jin wai shine minister,saboda irin yanda yake gudanar da sabgoginsa da al’amuransa da lokacin da yana tsohon gida sai kaje ka samesu shida Aryan suna yin ball wani lokacin harda yaran neighbors idan sun shigo,
Wurin chief security yaje yarinka yimasa fada yana cewa menene aikinsu agidan idan har abu irin wannan zai rinka faruwa,kenan zamansu bashi da wani amfani matsawar ba zasu rinka kulawa da kyau ba,yanzu gashi nan an iyo jifa ya fasa glass har yasamu Hanan,da Aryan ne ma awurin haka zai sameshi ko shi kansa,shi dai chief security hakuri kawai yake bashi yana cewa insha Allah haka bazata kara faruwa ba kuma yanzunma zai zurfafa bincike har sai yagano musabbabin faruwar hakan,
Wanka Hanan tayi kamar yanda yace ta dauki towel dake rataye cikin bayin ta daura ta kwaso kayanta da ta cire ta fito sadaf sadaf kamar wata marar gaskiya,ganin baya cikin falon yasata fita ta wuce part dinta tana zuwa ta saka doguwar riga mai gajeren hannu ta dauki turare tafesa nan taji kamar tayi kuka sakamakon zafin da taji ajikinta ta manta ashe ta yanyanke, muryar Aryan tajiyo afalo kuma da alama shida umma barira ne dan itama tajiyo maganar ta,dan karamin gyale ta dauka tafita, sannu umma tayi mata tana cewa ashe abinda yafaru kenan yanzu Khalil ke sanar dasu a k’asa,
Suna nan zaune tare da su umma yaturo mata da text wai taje yana kiranta,tashi tayi ta fita nan taga wurin da glass din ya tarwatse har an tattare an share an gyara numfashi ta dan ja ahankali dama ai wannan kasada ne wato siyan mai yarda inbanda kasada taya za ace gaba daya ayi katanga da glass,ace ko ina glass ne ai dole wata rana irin haka ta rinka faruwa,tare da Dr Al’amin ta samesu zaune shi yanata matse matsen waya yana duba posting din da S A na labarai yayi akan yajin aikin da likitoci ke son tafiya,zama tayi ta gaida Dr Al’amin wanda ke murmushi yana fadin,
“Amarya ashe abinda yafaru kenan….. To Allah ya kiyaye gaba,insha Allah zan baki magani saboda jikinki da glass din ya shisshiga”
“Tohm” ta fada batare da ta daga kanta ba saboda ita kunyar hada ido take yi da Khalil, magunguna Dr Al’amin ya harhada mata yabata tana karba ta tashi sim sim ta fita saboda bata son su sake yin ido hudu da Khalil kuma,
Har ta koma sashenta umma barira da Aryan na nan suna jiranta suna kallon tashar MBC 3 inda Aryan ke kallon cartoon sunata drama da umma tana cewa ita wadannan robobin masu kama da aljanu sun isheta ya canja shikuma yaki ya kama remote ya kankame yana zaune daram akan cinyarta,
Abinci ta zubo taci sannan tasha magungunan da Dr Al’amin yabata, Aryan ta dauka takaishi dakinsa ta kwantar sannan ta fito tazo tayi shirin bacci ta kwanta,tunanin Khalil ne yafara yawo acikin kwanyarta yana kaiwa da kawowa, hannayensa masu taushi da laushi duk da rikon da yayi mata dazu bada wata manufa bane amma tajishi har cikin ranta,kuma har yanzu tana jinsa, lumshe idanuwanta tayi tana sakin murmushi ita kadai sakamakon tunowa da tayi yanda dazu ya rude lokacin da abin yafaru,rufe idanuwanta tayi da tafukan hannayenta kamar yana ganinta saboda kunya,
“Yanzu shikenan ya ga jikina”
Da tunaninsa tare da sabuwar kaunarsa fil bacci yazo yayi awon gaba da ita. Khalil bayan fitar Hanan kallon Dr Al’amin yayi yace masa baya jin dadin jikinsa yabashi pills,
Kallon mamaki Dr Al’amin yafara yimasa kafin daga bisani ya cire farin gilashin dake fuskarshi,
“Amma ranka yadade anya kuwa bazaka hakura da shan relief pills dinnan hakaba…. Kar muje kuma ya fara haifar maka da matsala saboda kajima fa kana shan shi for over 5 years….. For how long zaka yita amfani dashi bayan kuma yanzu kana da iyali….. Ai sai ita ka cutar da ita….”
“Wai wadannan suratan duk waye ya tambayeka? Nifa pills kadai na bukata ba dogon bayani ba…”
“Sorry sir….” Dr Al’amin yafada yana kokarin fito masa da pills din,karba yayi sannan ya sallameshi yatafi,saida yasha pills din sannan yashiga bedroom dinsa,kai tsaye bathroom yawuce yacire kayan jikinta ya sakarwa ruwan sanyi,yajima yana kwarawa kansa ruwan sanyi sannan yafito yana daure da towel,zama yayi gefen gadon yana dafe kansa da hannayensa guda biyu,hoton Ramlat kawai yake gani acikin zuciyarsa, Hanan tayi kama da Ramlat dinsa ata wurare da dama,shi ba Hanan dince ta jefashi cikin wannan halinba,matarsa da yatuno shine silar samun kansa cikin wannan yanayi amma ita Hanan tausayi da kuma kaunar da take yiwa Aryan ne yasa shi dazu yaji hankalinsa yatashi lokacin da glass ya fashe kuma ai ko babu komai yanzu a karkashin kulawarsa take dan haka dole ne ya kula da ita,rasa abinda yake yimasa dadi yayi domin ko pills dinma yau ji yayi kamar baisha ba dan babu abinda ya canja na damuwar da yake ciki,kwanciya yayi saman gadonshi mai laushin gaske duk aikin bada sanyin da na’urar sanyaya dakin keyi shi gumi yake yi kamar ana gasashi cikin oven,yau yasha wahala dan saida ya gwammace kida da karatu daga karshe dai ya lallaba yatashi yasa jallabiya da short din wando sannan yafita, kitchen yasauka yaje yaduba fridge cikin sa’a yasamu lemon tsamin da yaje nema nan take ya yanka yashanye guda daya sannan yakoma sama,abin salla ya shimfida yahau yasoma sallar nafila.