MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

“Ki shirya gobe za muje gombe Muneerat ta haihu…..” Ya fada yana rike da wata jotter da pen yana rubutu amma bata san abinda yake rubutawa ba,
Tun adaren tayi shirinta ta hada kayanta set biyu sai ko kayan bacci da inner wears,humrar da hajja hasinah ta kawo mata ranar da tazo ta saka cikin akwatin kayanta sai da ta tabbatar tagama hada komai sannan ta kwanta,
Washe gari bayan ankai Aryan makaranta Khalil yaje office yafito suka nufi gombe bayan sunje store ta sai kayan baby,duk yau tunda ta tashi jikinta babu dadi ahaka dai suka karasa da rana fatse fatse nan ta samu tarba kamar yadda aka saba yimata,saida suka fara zuwa gidan Khalid suka ga baby anan Muneerat ke yimusu albishir din wai sunan Khalil Khalid yasakawa jaririn,ba karamin dadi Khalil yajiba nan ya ajiyewa Muneerat damin kudin da Hanan bata san ko nawa bane amma dai yan dubu dubu ne sabbi fil dasu,daga nan suka tafi cikin gida can Hanan ta samu tarba ta musamman awurin su hajiya da su zarah, bedroom din da take sauka idan tazo yauma anan aka sauketa,tunda tazo tashiga cikinsu sarah suna shan hira har dare, Khalil kuwa dama bata kara sakashi a idonta ba kuma shima agarin zai kwana.
Misalin karfe 11 da wurin rabi tana kwance suna chaten da yaya shamsu nan yake sanar da ita rashin lafiyar abbansu wai ciwon koda sunje asibiti yau,ai agigice tasa hijabi ta fita ta nufi bangaren Khalil tana hawaye,
Fitowarshi falon kenan bayan yafito daga wanka yashirya bata tsaya yin knocking ba ta bude kofar ta shiga, kallonta ya tsaya yi yana son jin ba’asin kukanta,
“Abba nane baida lafiya wai ciwon koda….. Dan Allah kasa akaini kano yanzu” haka take ta fada sam taki barinsa ma yafurta koda kalma daya saiko uban hawayen dake ta faman bin kumatunta kamar anballe bakin fanfo,hannunta yakama akaron farko ya zaunar da ita kusa dashi har jikinsu na gogar juna saboda kusancinsu kuma har lokacin yana rikeda hannunta,hakuri yasoma bata domin dare yayi yanzu bazai yuyu akaita kano a wannan lokacin ba,kuka ta fashe dashi hakan yabashi damar sakata acikin jikinsa yana rarrashinta,tun shigowar ta kamshin jikinta ke neman rikita masa lissafi domin humrar hajja hasinah yau ta shafa wato giredi nan da nan ta tayar masa da hankali,ita kuwa yau mamakinsa ne ya cika mata zuciya ganin ya biye mata harda rarrashi shiyasa ta bararraje taci gaba da shagwabarta…………………..鉁嶐煆?
_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:15 AM – Ummi Tandama: 48
***D’aukarta yayi gaba dayanta ya dorata kan cinyarsa wanda hakan yayi mutukar bawa Hanan kunya sosai, rungume ta yayi cikin jikinsa yana shafar bayanta alamar rarrashi,ji tayi kamar ta nutse kasa saboda tsananin kunya,shi kuwa gogan hankalinsa ne yakai kololuwar tashi saboda sosai kamshin jikinta ya rudashi kuma ya jefashi cikin kogin bukatarta,
Cikin dabara yasamu ya rabata da hijabin da ke jikinta wannan ba shine karo nafarko da yafara ganinta ahaka ba amma wannan yana da banbanci da na lokutan baya,sosai yau dinnan Khalil ya dauki dumi domin wata irin matsa yayi mata sai faman aikin sinsinar jikinta yake yi sakamakon kamshin da jikinta keyi wanda ke kara masa kaimi yana ingizashi gareta,cak yatashi da ita yanufi cikin bedroom dinshi yana rike da ita,ita kam idanuwanta arufe suke ta runtse su dan ba zata iya hada ido dashi ba cikin wannan yanayi,
A saman katafaren gadonshi yayi musu masauki bayan ya rage hasken dakin izuwa haske marar karfi, jikinta har rawa yake yi saboda rashin sabo ga kuma tsoro duk da cewa abun yazo mata bagatatan batare da shiri ba,tun kafin ya aiwatar da kudirinsa shima nasa jikin ya dauki rawa babu bata lokaci wani matsanancin zazzabi da ciwon kai suka rufeshi nan take batare da ya cimma burinsa ba,
Kasa aikata komai yayi sai ko uban kakkarwar sanyi da gangar jikinsa keyi kamar ana kwara masa kankara,
“Sa’adatu lullube ni…….. Sanyi nake ji”
Gaba daya duk ta rude itama ganin abinda ke faruwa domin wani irin rawa jikinsa keyi, lullubeshi tayi da bargo amma yanda yake jin sanyi na kadashi gani yake yi kamar bata rufa masa komai ba shiyasa yayi azamar jawota jikinsa ya rungume jikinsa ya dauki zafi sosai,
Haka suka kasance zuwa wani lokaci yanata kakkarwa har lokacin yana rungume da ita kamar zai mayar da ita can cikin cikinsa,ya dan fara samun bacci sama sama ciwon ciki ya turnikeshi kamar zai mutu har da su yunkurin amai amma kuma yakasa, Hanan kuka tafara yi tana son ta tashi taje cikin gida ta kira su hajiya amma ya riketa tsam kamar me,kuka take ta faman yi tana yimasa sannu shi kam ko magana ma yakasa yi sai yunkurin amai yake ta yi cikinsa na murda masa haka suka kusan kwana dan sai kirjin asubah sannan yasamu ciwon ya lafa masa har bacci yayi nasarar daukarshi,sakashi agaba Hanan tayi tana kallonsa cikin tausayawa har lokacin yana manne da ita yana bacci,ita kam sai bacci barawo domin tana cikin hali na zullumi dan yanda taga Khalil din yayi ba karamin tayar mata da hankali yayiba dan kamar wanda zai mutu haka yazame mata fa,
Misalin karfe 7:30 na safe ta farka nan idanuwanta suka sauka akan bawan Allah Khalil da keta faman baccin wahala duk yagama jigata takai kimanin mintuna biyar tana kallonsa sannan da dabara ta raba jikinta da nashi ta tashi, kayan baccinta ta maida jikinta sannan ta shiga bathroom,bata wani jima acan sosai ba tagama abinda zatayi ta fito tazo tayi salla,bayan ta idar ne ta samu zarafin kallon dakin,daki kam komai yaji ne babu ma abinda yafi burgeta irin dan karamin farin gadonshi wanda ke girke cikin dakin,mikewa tayi ta nufi bakin gadon nan idonta yasauka kan wani madaidaicin hoto dake ajiye kan bedside drawer dinshi,zama tayi ta dauki hoton tana dubawa bakinta abude mamaki karara kwance saman fuskarta domin badan tasan cewa ba ita bace ta dauki wannan hoton to da babu abinda zai hana tace itace saboda tamkar kara aka tsaga da ita da wacce ke jikin hoton tana sanye cikin purple din atamfa tana dariya, Allah mai iko to ko wannan itace mahaifiyar Aryan? Ta kissima hakan acikin ranta,tajima tana kallon hoton kafin ta ajiyeshi ta juya ga Khalil wanda ke kwance ya dunkule wuri daya,so take ta tasheshi yayi salla amma tana tsoron kar kuma yatashi da ciwon cikin tunda ansamu ya lafa masa,
Bargon da yake ciki ta dan yaye tafara tashinsa har lokacin jikinsa akwai zafi sosai,riga mai nauyi yasa ta dauko masa yasaka sannan ta rikeshi ya sauka daga kan gadon yashiga bathroom,daurewa kawai yayi yai sallar amma shi kadai yasan abinda yake ji,tun akan abin sallar yafara rike ciki dakyar ta taimaka masa yakoma saman gado ya kwanta nan tafita zuwa cikin gida da sauri domin sanarwa dasu hajiya. Cikin lokaci k’ank’ani aka kira Dr yazo yafara dubashi amma ciwo kamar karashi akeyi,gaba daya hankula sun tashi musamman ma Hanan da hajiya,wurin azahar yasamu ciwon cikin ya lafa dan har yasamu damar yin bacci, Hanan na zaune awurinsa yaya shamsu yakirata awaya saida taji hankalinta yatashi gabanta ya fadi nan ta amsa wayar jikinta na rawa tunda shima Abban nasu tasan baida lafiya,