MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

“Yaya shamsu yajikin Abban?”

“Jikinsa da sauki Hanan gamu ma agida…”

“Kajini shiru banzo ba ko? Shima Abban Aryan ne yatashi da ciwon ciki shiyasa wallahi amma zanzo…”

“A’a kiyi zamanki ki kula dashi tukunna…..ga Abban ma”

Jin Abba ya karbi wayar yasata fashewa da kuka, Nan Abba ya dan kwantar mata da hankali yace mata yama samu lafiya dan har fita zaiyi anjima,saida suka gaisa da mamaye sannan sukayi sallama ta kashe wayar ta zubawa Khalil ido kamar lokacinne tafara ganinsa, tausayinsa take ji har can cikin ranta wanda bata san daliliba koda yake kila tausayin yanada nasaba da irin son da take yimasa,

Zuwa la’asar ya farka da wani azababben ciwon cikin ga yunkurin amai amma yakasa yin aman ganin dai abun kamar gaba yake kara yi Zaid ya kwashesu suka nufi asibiti can aka bashi gado aka kwantar dashi,daren ranar kuwa daga shi har Hanan basu runtsa ba saboda murkususun da yaketa faman yi sai asubah sannan yasamu bacci,

Misalin karfe 7 nasafe su hajiya suka zo harda wani dattijon bafulatani tare suka shiga cikin dakin sannan ya tsaya akan Khalil yana kallonsa har na wani tsawon lokaci daga bisani yajuya ya kalli hajiya ya kalli Hanan sannan yace,

“Wannan aikin shaidanu ne,ko shakka babu sihiri ne kuma mai karfin gaske sai dai Allah yabamu nasarar warwareshi cikin sauki…., Yanzu hajiya abani kwana uku zanje innemo makarin wannan asirin dake jikinsa,amma zan aiko jikina salisu zai kawo masa tsumin da zaisha saboda wannan ciwon cikin dake damunsa, Allah yabashi lafiya….”

“To shikenan nasalla,mun gode, Allah yasa adace,mun gode” hajiya ta fada tana sharar hawayen dake idonta,ita dai Hanan tana tsaye tarasa ma wanne irin tunani zatayi,shikuma Khalil haka rayuwarshi take daga acutar dashi sai acutar da danshi to duk suwaye keyi masa wadannan abubuwan? “Makiya mana” zuciyarta tabata amsa,wuri ta samu ta rafka tagumi tanata tunane tunanen da bata san dalilinsu ba,

Zuwa yamma aka kawo sakon tsumin da za abawa Khalil wanda duk yayi wujiga wujiga dashi babu ci babu sha sai wahalar ciwo,tunda yasha maganin yasamu saukin ciwon cikin domin ba kamar jiya ba yau har yana iya tashi yayi salla kuma ansamu yasha ruwan zafi, Hanan kam koda yaushe cikin hawaye take lallai dan adam ba abakin komai yake ba komai kudinsa komai mulkinsa yanzu shi Khalil ga kudin ga mulkin ga zaratan masu tsaron lafiyarsa amma duk ciki babu wanda ya isa ya dauke masa ciwon dake tare dashi sai sarki Allah.

Cikin kwanaki biyun da suka yi a asibitin za a iya cewa da sauki tunda yana tashi kuma yana iya cin abinci sai dai fa yunkurin aman da yaketa yi kuma yakasa yinsa,yana kwance yanzunma bayan yagama yunkurin aman Hanan na yin salla nasalla yashigo dauke da wata yar batta irin wacce fulani ke zuba ruwa aciki, gaisheshi Hanan tayi sannan tabashi kujera ya zauna yana fuskantar Khalil,

“Moddibo……… Insha Allahu andace kuma anyi nasara domin ansamo makarin cutar dake jikinka shekara da shekaru,amma sai kayi hakuri da abinda zaka ji daga gareni,matarka itace tayi maka sihirin mallaka,sihirin da bazaka taba kusantar wata ‘ya mace ba koma bayan ita,idan har kayi koda yunkurin aikata hakanne to zaka iya rasa rayuwarka…….”

Shiru Khalil yayi yana nazari acikin ransa,yanzu Ramlat itace ta aikata masa wannan mummunan aikin? To saboda me? Awanne dalili? 

“Saboda ta kasance ita daya tilo acikin zuciyarka da rayuwarka mana….” Zuciyarshi tabashi amsa,

“Ba dan Allah yasa hajiya ta kirani ta sanar daniba to da haka zska kare rayuwarka sai dai wani kadari na ubangiji….. Yanzu ga wannan tashi kasha”

Idanuwansa fal da hawaye yatashi zaune ya karbi maganin yakafa kai yafara sha amma ko hadiya uku kwakkwara baiyi ba yaji wani mugun amai yataso masa,karbe maganin nasalla yayi ita kuma hanan ta taso da sauri,

“Samo masa wani abu amai zaiyi…” 

Cikin sauri ta dauko wata silver ta kawo masa riketa yayi bayan ta zauna akusa dashi nan yaci gaba da kakarin aman kamar zai amayar da dukkan abinda ke cikin cikinsa gaba daya,zuwa can yasoma wani irin amai domin gashi ne curi curi yake amayar dasu abun ba kyan gani gwanin ban tsoro,yasha wahala mutuka sannan yasamu nasarar amayar da gashin tas nan nasalla yakarba yafita harabar asibitin yaje ya binne yasake dawowa,

Daga Hanan har Khalil mamakine keta faman dawainiya dasu saboda jin abinda nasalla yace,kai amma gaskiya mata na aikata kuskure,yanzu wannan daukar hakki har ina? Ita gashi wacce ta aikata hakan tariga da tabar duniyar to koma dai tana raye ai da cutarwa,

Shi kuwa Khalil abin yatsaya masa arai haba shiyasa ranar da Ramlat zata rasu ta rinka neman gafararsa tana cewa ya yafe mata to ko dama wannan yafiyar take nema? Gaskiya mata ba abun yarda bane, Ramlat ta cutar dashi da yawa sannan ta cutar da wani ma tunda kila ba dan Allah yakawo karshen abunba da ahaka zai kare rayuwarsa,

Adaren ranar aka sallamesu suka koma gida domin jiki yayi sauki kuma ansamo bakin zaren,wanka yashiga yayi yafito yana zaune bakin gado yana rike da turare Hanan tashigo dauke da tiren abinci ganinshi babu riga yasata niyyar komawa da baya,

“Shigo mana….” Yafada kamar wani marar lafiya koda yake marar lafiyar ne amma dai muryarshi ta sake yin sanyi kalau,

Kanta a kasa ta ajiye masa ta mike zata fita,

“Ina zaki je?”

“Zan koma canne…”

“Can ina?” Ya tambaya bayan yasoma fesa turaren ajikinsa,

“Wurin su hajiya”

Shiru yayi baice komai ba har saida yamike tsaye domin dauko rigar da zai saka sannan taji yace,

“Ki shirya gobe dasafe za akaiki ki gano abbanki”

Cikin fara’a da farin ciki yaga ta dunkule hannayenta wuri daya sannan tace,

“Tom nagode”

Daga haka ta tashi tafita kuma bata kara komawa sashen nasa ba ita dama tun can asali tayiwa Khalil uzuri duk wannan faman shassharetan da yakeyi bai wani dameta sosai ba ashe ashema bai laifinsa bane bawan Allah,

Shima anashi bangaren tunanine kala kala yaketa shiga yana fita cikin kwakwalwarshi,gaskiya Ramlat tayi masa abinda bai taba tunanin zatayi masa ba amma ya yafe mata kuma yana yimata fatan samun rahamar ubangiji. Daren ranar sam bacci baiga idonsa ba sai bayan da yayi sallar asubah sannan ya dan samu baccin,ita kuwa Hanan da wuri tagama shirinta zuwa karfe 8 suka kama hanyar kano saboda aranar zasu dawo,

Lokacin da taje gida ta samu jikin abbansu da sauki babu laifi sai lokacin taji hankalinta ya kwanta domin taganshi kalau dashi nan aka shisshigo da kayayyakin da tazo dashi, agurguje tajewa anty salaha sannan suka juya gombe ita da sabon drivern Khalil mai suna attahir. Tana komawa gombe adaren ranar suka koma Abuja domin acewar Khalil yana da uzururruka da yawa acan,

Karfe 9 da wasu mintuna suka shiga gida cikin murna su umma suka zo suka taryesu ita da Aryan wanda har lokacin baiyi bacci ba,

Ita dai sashenta ta wuce shikuma Aryan yabi abbanshi part dinsa,

Wanka tafara yi sannan ta gabatar da sallolinta tana idarwa ta sauka kasa ta nemawa kanta abinda zata sakawa cikinta,tana kokarin tashi taji shigowar text massage,

_Zo ki dauke Aryan._ 

Ganin abinda Khalil yaturo mata yasata mikewa direct tawuce part dinsa, Aryan na falo kwance kan sofa shi kadai,daukarshi tayi tafita zuwa dakinsa taje ta kwantar dashi,takoma nata har ta kwanta taji shigowar wani text massage din,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button