MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

_Had’o min coffee._

Mikewa zaune tayi tana kunkuni ita kadai,

“Shima Abban Aryan akwai saka aiki wallahi,sam bazai bar mutum ya huta ba”

K’asa ta sauka ta hada masa coffee din sannan ta wuce part dinsa,baya cikin falon dan haka taje gaban kofar bedroom din nasa akaro nafarko dan ba taba shiga tayiba, knocking tayi har zata juya tajiyo muryar shi yana cewa,

“Come in”

Dukan uku uku kirjinta yafara yi sannan wani dan banzan tsoro ya shigeta lokaci guda,kamar wata sakarya haka ta tsaya kafin daga bisani ta kama kofar dakin ta murda tashiga……………………….鉁嶏笍

_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Aisha_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:15 AM – Ummi Tandama: 49

***Yau kam tantagayyar yar kauye Hanan ta koma lokacin da ta shiga bedroom din Khalil, bedroom din ya hadu ya hadu karshen haduwa,komai na ciki farine kama tun daga kan tafkeken gadon baccinshi kirar Turkish bed sai wani dan karamin wurin hutawa mai dauke da kyawawan fararen kujeru zagaye da center table atsakiyarsu,gaba daya idanuwanta sun kasa tsayawa wuri daya sai kaiwa da kawowa suke yi a sassan bedroom din,

Yana kishingide kan wani lilo wanda ke can nesa da gadonshi hannunshi rike da novel na turanci wanda da alama karantawa yake yi,sanye yake da riga armless marar nauyi da kauri sai bakin wando mai santsi,

Cikin sassarfa ta dosheshi hannunta rike da coffee din,jikinta har wani rawa yake yi kadan kadan wanda bata san dalili ba,harga Allah a daidai wannan lokacin da Khalil zaice takoma inda tafito da zata fi yin murna da hakan,kamar wanda zai zaneta ko zai rufeta da duka yau haka take jin bala’in tsoronshi,

Har kasa ta durkusa lokacin da ta karasa gareshi wanda ita kanta bata san dalilin hakanba, hannunta taji ya hada dashi lokacin da ta mika masa coffee din,dagota yayi ya zaunar da ita kan lilon a gefenshi sannan ya ajiye coffee din kan stoll,

Tun shigowar ta kamshin dake manne jikinta yake barazanar tarwatsa kofofin hancinsa dan mutukar sanyi da dadi,tamkar wacce aka zarewa laka ajikinta haka tazama yau dan sam bata cikin nutsuwarta gaba daya,

Wata irin fargaba da tsoro ne keta faman shigarta tun bayan shigowarta cikin dakin,tajima tana burin wannan rana sannan kuma ta dade tana rokon Allah akan yanuna mata ranar nan amma yau sai gashi tana jin inama tana da damar mayarda hannun agogo baya,inama wannan ranar takoma da tayi dunbin farin ciki domin babu komai cikinta inbanda tsoro,damuwa da tarin zulumi,

“Uncle zan koma……. Bacci nake ji…..” Ita kanta bata san lokacin da ta furta hakanba,

Littafin hannunshi taga ya mika mata,

“Babu inda zakije,yau hira zaki tayani and tare zamu kwana……”

Tamkar zakaran da aka tsoma cikin ruwa yayi tsumu tsumu haka tayi jin abinda yace ya sake rikitata da burkitata wannan fa shi ake kira da bazata,ita dai yau tana tsoron wannan rana,jin ya rungumo kafadarta ya karata da jikinsa yasata saurin kallonsa, murmushi yasakar mata cikin rada taji yace,

“Meke tsorataki ne? Dama haka kike da tsoro?”

K’asa tayi da idanuwanta saboda bazata iya cigaba da kallonsa ba,

“Fara karanta min wannan novel din…… Am all ears”

Littafin tabi da kallo kamar wata sokuwa,

“Ke nake jira…..” Taji yafada cikin muryar rada,kasa karanta littafin tayi domin gaba daya tagama tsorata dashi,lallai komai dokinka da wannan ranar dolenka kayi ladab idan tazo,

“Bani littafi na tunda ba zaki karanta minba….”

Karba yayi ya ajiye saman stoll sannan ya dauki coffee dinsa da ke ta faman turiri ya bude yafara kurbarsa da zafinsa wanda hakan har mamaki yaso bata,

Sai da yashanye tass sannan ya ajiye dan karamin flask din saman stoll yajuya ya kalleta,cikin azama tayi kasa da idanuwanta,

“Tunda kin ki karanta min novel to bani labari….”

“Bacci nakeji…… Dare yayi”

Agogo ya kalla sannan ya kalleta,

“Nikuma yanzu dare na yafara, sai 2 ko 3 nake kwanciya bacci…”

Ido ta zaro sannan ta toshe bakinta da hannunta guda daya,

“Uncle dan Allah inje in kwanta?”

Yunkurawa yayi yatashi daga kan lilon yana kallonta,

“Ai nafada miki yau tare zamu kwana,oya tashi muje”

Kasa tashin tayi saboda tsabar fargaba da tashin hankali,har yasoma tafiya ya juyo yaga ta nan zaune bata ko motsa ba,dawowa yayi da baya bata farga ba taga ya tarairayeta gaba dayanta yanufi kan gadonshi da ita nan jikinta ya cigaba da rawa kamar mai rawar sanyi,ajiyeta yayi sannan ahankali taji yace,

“Yi baccinki anan…..”

Daga haka yashige cikin bathroom ita kuma taci gaba da tsittsilla ido tana bin dakin nashi da kallo,wai tayi bacci to tayaya zata iya bacci anan? Ahaka taga yafito ya karasa kan abin sallarshi da alama alwala ya dauro,salla taga yayi raka’a biyu duk yanda akayi shafa’i da wutri zai gabatar,

Anashi bangaren shima yana son yace ta tashi suyi sallar nafila amma ganin irin tsoron da ya bayyana atare da ita yasashi kawai ya rabu da ita sai shi kadai yayi nafilfilinsa bayan ya idar da addu’o’insa yamike ya nufi gadon,tana ganin haka ta mayar da idanuwanta ta kulle cike da fargaba,gaba daya hasken dakin ya kashe sai wata yar blue light marar haske nan Hanan ta sake samun kanta cikin faduwar gaba tare da zulumi,

Abayanta taji kwanciyar shi sannan cikin nutsuwa ya juyo da ita suna fuskantar juna,

“Wannan hijabin zai takura miki…” 

Bai jira cewarta ba yacire hijabin ya ajiye agefe sannan yajata ya sakata cikin jikinsa,

Ji tayi kamar ta saki fitsari awando saboda fargaba da tsoro da suka taru suka kanainayeta shi kansa ya lura da hakan shiyasa saida ya hada da dabaru da wayo, bakinsa taji yana laluben nata wanda ke kamshin splash kamshin kadai ya isa ya sanyawa mutum nutsuwa acikin zuciyarsa,shikuwa tun bayan lokacin da yarabata da hijabin jikinta wani sanyayyen kamshi ke barazanar rusa masa tunani nan duk yabi ya susuce,

Kuka kam ta shashi har ta goda Allah,har komai ya kammala bata daina wannan kukan ba domin jinta take kamar ana kokarin rabata da numfashinta saboda duk ta jijji rauni ayanda yazo mata kamar sabin shiga shima haka ya zama yau,

Rungumeta taji yayi acikin jikinsa cikin muryarshi wacce bata fita sosai yana rarrashinta,

” Kiyi hakuri kinji…… Nine ko? Sorry,ke dince kinada gardama sa’adah,sannu yi shiru bazan kara ba……”

Wadannan sune kalaman da yaketa faman rada mata acikin kunnuwanta ahaka har bacci ya kwasheta,sai da ya tabbatar tayi baccin sannan yatashi yashiga toilet yau kam mararsa sakayau yake jinta sakamakon fitar da abinda yajima yana damunsa da yayi tsawon shekara da shekaru,bazai taba mantawa da wannan ranar ta yauba acikin tarihin rayuwarsa,

Fitowa yayi bayan ya tsaftace jikinsa sannan yabi gefenta ya kwanta bayan ya sauya kayan jikinsa,

“Sarkin tsiwa…” Yafada ahankali yana kokarin sakata ajikinsa,yamutse fuska yaga tayi cikin baccinta sannan ta turo masa dan madaidaicin bakinta, kissing din bakin nata yayi kafin ya lumshe idanuwansa yana rungume da ita tsantsam akirjinsa,

Wani baccin dadi ne yayi awon gaba dashi mai cikeda dunbin ni’ima marar misaltuwa domin rabonsa da yasamu bacci mai dadi irin wannan tun Ramlat tana raye,baccinsa yasha na dan wani lokaci daga bisani yatashi yashiga toilet domin tuni anjima da fitowa daga masallaci, bude ido Hanan tayi tana jin jikinta duk yayi tsami ahankali ta lallaba ta maida sutturarta ta dauki hijabinta ta fice daga dakin tana dingisawa dakyar lokacin da taje corridor kuwa saida ta tsaya ta dan huta sannan ta karasa part dinta,kai tsaye toilet ta shiga ta tara ruwan zafi sannan ta shiga ciki,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button