MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Wanka tayi tai brush sannan tafito har lokacin tana jin zafi da radadi ajikinta ahaka ta canja kaya tayi salla bayan ta idar taje ta rufe kofarta tun daga falo sannan ta dawo tabi lafiyar gado ta lulluba ta kwanta babu jimawa wani bacci mai dan karen dadi ya kwasheta.

Shi kuwa Khalil bayan yafito daga bathroom dinshi sai yaga gadonshi wayam babu Hanan babu alamarta,

“Har ta gudu kenan…..” Yafada acikin ransa,

Salla yayi sannan ya nade bedsheet din da ke kan gadon yawuce dashi toilet wanka yayi yafito yashirya cikin sauri saboda yanada meeting na musamman da mr president sannan da yuyuwar zai iya barin k’asar ayau zuwa k’asar Denmark,

Suit yau yasha yatsuke kuma ba karamin kyau yayi ba,agogonshi ya daura sannan yafita,tun daga corridor yafara jiyo karadin Aryan wanda Attahir sabon driver ke rike da hannunshi cikin shigar kayan makaranta,

“Good morning Papa” Aryan yafada tare da rungumeshi,

“Morning lovely son”

“Uncle yau mommy ba itace ta shiryani ba umma ce,wai mommy ta makara…”

“Ehh Aryan,maza kaje akaika school kada kayi late….”

Part din Hanan ya nufa bayan su Aryan sun koma kasa,kofar tata akulle take gamm nan yayita faman knocking amma shiru domin tana can cikin bedroom dinta tana ta sharar bacci bata ma san yana yi ba,

Gajiya yayi da knocking din yawuce domin har yaso ya dan makara.

Hanan kuwa ba ita ta tashi daga bacci ba sai misalin 12 na rana wannan dinma yunwace ta tada ita,dan mayafi kadai ta yafa sannan ta sauka kasa,umma na babban falon kasa tana sakar tabarma,saida suka gaisa sannan tawuce dining table ta zauna tayi breakfast,bayan ta gama ta sake komawa wurin umma,duk yanda taso da ta boye yanayin da take ciki saida umman ta gane dan har magana tayi mata tace ta daure ta gasa jikinta sosai da ruwan zafi zata ji dadi,cike da kunya ta tashi ta koma sama tana jin dan zazzabi zazzabi ajikinta amma bai sauka sosai ba,shawarar umma tabi ta sake gasa jikinta sosai da ruwan zafi daga nan tasake kwanciya kafin lokacin salla yayi,wani sabon baccinne yasake daukarta cikin baccin zazzabi ya dan rufeta wanda ita kanta tasan na tsananin wahalar da ta shane,har Aryan yadawo daga makaranta tana kwance cikin bargo da zazzabi ajikinta bata samu fitowa ba sai zuwa bayan magriba lokacin ta danji dama dama atare da ita.

Khalil kuwa yau bai samu zama ba duk da yana cikin sabgogi masu tarin yawa amma yana ta gwada kiran layin wayar Hanan amma akashe baya samunta daga karshe lokacin da sukayi waya da Aryan shi ke sanar dashi wai bata da lafiya lokacin da Khalil din ya tambayeshi wai ina mommy,suna gama waya da Aryan yaturawa Dr Al’amin text massage akan yaje yaduba Hanan saboda shi bazai samu damar komawa gidanba dan ta can office zasu wuce airport. 

Hanan bata san cewa Khalil yasan rashin lafiyarta ba,bayan tayi wanka tayi salla ta sauka kasa har lokacin jikinta akwai zazzabi kadan duk kuma tayi sanyi komai tana gudanar dashi cikin rashin kuzari,suna zaune falo Aryan nata wasa akan dokin robarshi Dr Al’amin yazo,gyara mayafinta tayi sannan tace yakaraso,

“Ranki yadade oga ne yaturo ni yace bakida lafiya inzo indubaki….”

Jin abinda Dr yace bayan sun gaisa sai duk kunya ta kamata to shi Abban Aryan din waye yasanar dashi bata jin dadi? Kodai shi da kansa yasan dole hakan tafaru tunda yasan abinda ya aikata? Cike da kunya tayiwa Dr bayanin yanda take ji nan ya hada mata magunguna yabata yatafi,

Abinci ta dan ci sannan tasha maganin tasake komawa sama ta kwanta,haka taci gaba da kwanciyar nan har zuwa dare kuma sai lokacin ta kunna wayarta domin tana son kiran gidansu dan taji ya Abba yakara ji da jiki,

Mamaye ta fara kira bayan sun gaisa sannan ta kira abbaa wanda ke tare da yaya shamsu sun dan jima suna hira daga bisani sukayi sallama,suna gamawa ta ajiye wayar tashiga wanka, lokacin da tafito tana tsaka da shirin bacci kiran Khalil yashigo,rasa yanda zatayi ta dauki wayar tayi domin wata irin matsananciyar kunyarsa take ji har kiran ya katse bata iya dagawa ba,wani kiran ne yasake shigowa akaro nabiyu wanda shi kansa Khalil bai san dalilin zuciyarsa na nacewa lallai lallai sai taji halin da Hanan take cikiba wai yau shine harda kiran ta sau 2 gaskiya taciri tuta domin hakan ba dabi’arsa bace,

Wayar ta d’aga amma ta kasa cewa komai sai shiru da tayi,numfashi ya dan sauke ahankali daga kwancen da yake sannan cikin taushin murya yace,

“Bacci kike yine?”

Jin abinda yace yasata furta, “A’a” Ahankali,

“Me kike yi?”

“Wanka nayi ina shiryawa…..”

“Inzo in tayaki?”

Shiru tayi sakamakon jin abinda yace,gaskiya mutumin nan shima A ne,

“Uhmmm?” Taji yasake bukata,kasa magana tayi amma dai tana rike da wayar a kunnenta,

“Ya jikin naki?”

“Da sauki….” Ta fada muryarta na dan rawa,

“Kinsha maganin?”

“Uhmmmm”

“Allah yakara lafiya….”

Shiru tayi ba amsa,jin har lokacin ta kasa sakewa dashi yasashi yimata sallama ya katse wayar,karasa shiryawa tayi ta kwanta aranta tana sake jinjina rashin kunya irinta da namiji,shikuma Abban Aryan irin nasa salon muguntar kenan yasha coffee mai zafi yakare akanta,lumshe idanuwanta tayi tana murmushi duk da tasha wahala amma moment din yayi mata dadi sannan zata yita ajiyarshi acikin kwakwalwarta har zuwa karshen rayuwarta,da tunanin daren jiya bacci yasamu nasarar yin gaba da ita. Washe gari ras ta tashi sai dai dan abunda ba arasa ba kuma yau dinma wuni tayi akwance wayarta akashe dan har ta kwanta bacci bata bude ba,shi kansa Khalil sai awurin umma yaji lafiyar ta jin umma tace masa lafiya lau yasashi sauke wani gwauron numfashi sannan yayi mata sallama ya katse wayar,

Washe gari tunda ta tashi take shargallenta domin ta wartsake ta warke ras yanzu bata jin ciwon komai kuma sunsha wasansu da Aryan dayake weekend ne,har bayan sallar ishah suna tare afalonta dake sama suna kallo saida yayi bacci sannan tashiga wanka bayan ta kaishi cikin bedroom dinta ta kwantar dashi,rigar bacci ta saka bayan ta shafa humrarta mai sanyin kamshi, wayarta ta landline dake ajiye kan bedside drawer itace tafara ruri nan ta dauka dan jin waye domin dai duk yanda akayi acikin gidanne,

“Meyasa wayarki akashe? Hado min coffee ki kawo min yanzu…..” Jin muryar khalil yasata jin cikinta ya tsure to yaushe yadawo? Gashi kuma wai takai masa coffee,ita fa bata manta da kaiwa coffee din ranar nan ba,anan cikin bedroom dinta tabar Aryan ta saka hijab har k’asa sannan tafita zuwa kitchen, mintuna kalilan tagama hada masa ta dauka tafita,yauma baya cikin falo yana can cikin bedroom dinshi hakan yasake tsinkar mata da gaba,cikin fargaba da tsoro tashiga bedroom din nashi nan dinma baya ciki,ajiye masa coffee din tayi tana kokarin juyawa takoma taji motsin fitowarsa daga toilet,tunda tajuya sau daya ta kalleshi bata sake marmarin kallonsa ba,

“Ina zakije kuma?

Taji ya tambayeta idanuwanshi akanta,

“Uhmmm…… Dama…. Dama Aryan zanje inkai dakinshi”

“To je ki kaishi ki dawo”

Kai ta daga sannan ta fita amma bata da niyyar dawowa dan harga Allah ita yanzu tsoron Khalil take yi,shiyasa lokacin da ta koma bata dauke Aryan din ba tabarshi adakinta zasu kwana tare,

Shiru shiru Khalil yaga bata dawoba har yagama komai nasa, k’arfe 1 na dare agogon kan bedside drawer dinshi yanuna turaren midnight mai tsadar yasake fesawa sannan yafita yanufi part din Hanan,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button