MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Ganinsu kwance tare da Aryan yasashi yin dan murmushi, Aryan din ya dauka yafita dashi yakaishi dakinsa ya kwantar sannan yadawo bedroom dinta,bacci take yi sama sama taji kamar andauketa,jinta tayi kamar acikin mafarki shiyasa tasake kankameshi tana shakar kamshin jikinsa bayan ta lafar da kanta cikin kirjinsa. Yana rike da ita akirjinsa har part dinshi cikin bedroom dinshi,akan gadonshi ya kwantar da ita nan ta wartsake daga baccin da take yi jin ya ajiyeta,dan bude idonta tayi kadan nan ta hangoshi yana kurbar coffee daga tsayen da yake rike da kugunshi da hannunshi guda daya cigaba tayi da kallonsa har ya shanye,sai da taga ya ajiye yana kokarin juyowa sannan tayi gaggawar rufe idanuwanta, murmushi yayi yarage hasken dakin sannan ya nufi kan gadon,

Kamar yadda ta tsammata yauma bai saurara mata ba ko kadan dan gaba daya gajiyarshi akanta ya sauketa,tasha kuka har muryarta ta dashe,kamar yadda take zargin da biyu yake shan coffee din nan da alama zarginta yazama gaskiya dan da asubah ma sai da yafita da kansa yaje kitchen ya hado yazo yasha tana kallonsa,rage mata yayi itama yamika mata wai tasha, girgiza kai tayi idanuwanta har sun tara kwalla,

“Kisha zakiji dama dama….”

Tana kokarin sake yin musu yaje yakai cup din bakinta nan ta tashi tasha duk da bawai so take yiba. Dana sanin shan coffee din ta tsinci kanta tanayi domin wahalar yanzu har tafi ta daren jiya sai dai shi uban gayyar taga kamar yanzun yafi zakewa fiye da jiyan, jikinta duk yayi tsami ahaka bacci ya dauketa tana rungume ajikinsa yana dan jijjigata alamun lallabawa.

Misalin karfe 9 nasafe ta samu nasarar tashi daga daddadan baccin da ya dauketa mai cikeda hutu domin ko babu komai jikinta da ruhinta sun dan huta,idanuwanta ne suka sauka akan Khalil wanda ke tsaye gaban mirror yayi crossing legs dinsa yaharde hannuwanshi a kirjinsa sanye cikin farar t shirt da farin wando,yanda take kallonshi haka shima yake kallonta kamar zai hadiyeta,

“Good morning” Taji yafada ahankali cikin muryarshi mai sanyi da taushi gamida zaki haka kuma mai cikeda dadin saurare,kai kawai ta daga masa tasoma yunkurin sauka daga kan gadon nashi ma’abocin girma da laushi,

“Hey….. Where are you going?” 

“Bedroom dina zan tafi”

“No,kwanta ki huta anan”

Matsawa kusa da ita yayi ya tarairayeta ya sake kwantar da ita sannan yaja duvet ya rufeta, abayanta tajishi shima ya kwanta sannu ahankali ya rungume ta bayan yakai fuskarshi saman tata,irin yanda ya kanannadeta ya kanainayeta ko kwakkwaran motsi ta gagara yi,jin dumin jikinshi da sanyin kamshinsa da ya cika mata hanci bata san lokacin da bacci ya sake d’aukarta ba,shima baccin yayi cikin farin ciki da nutsuwa har zuwa 12 na rana,itace tafara farkawa har lokacin tana kanannade cikin jikinsa sai faman sharar baccinsa yake yi,dan murmushi tayi wanda ita kadai tasan dalilin yinsa sannan ahankali ta daga ido ta kalleshi domin yanzu suna kallon junane,idonshi taga shima yabude wad’anda ke cike da bacci da ido yake tambayar ta menene? Kai ta girgiza masa hakan yabashi damar sake matseta ajikinsa yana shirin komawa wani baccin,

“Uncle yunwa…..”

Bude idonshi yayi ya kalleta babu shiri ta dauke nata idon,

Dan sakinta yayi daga rikon da yayi mata hakan yabata damar tashi duk kunya ta cikata dan dakyar take iya kallonshi, ahankali ta sauka daga kan gadon tafita ta nufi sashenta,ada babu abinda take buri kamar zuwan wannan lokaci sai gashi yazo yanzu kuma tana fatan samun rangwame,wanka tashiga tafara yi sannan bayan tafito batare da ta ko shirya ba ta nufi kitchen taje ta hada tea tafara sha sannan takoma bedroom dinta ta shirya sama sama saboda yunwar da takeji,riga da skirt ta saka na atamfa coffee colour sannan ta shafe jikinta da turare tafita duk jikinta babu karfi sosai,

K’asa ta sauka taje ta zuba abinci sannan ta shiga wurin umma suka gaisa nan umman ke bata labarin mutumin nata Aryan wanda saida yagama casa rigamarsa sannan ya tafi makaranta,dariya Hanan keyi har tagama karyawa sannan tafita ta nufi dining table, Khalil ta shiryawa nasa breakfast din kan wani babban faranti dan tasan shima da wahala idan ya karya,kinkima tayi ta nufi sama, lokacin da ta shiga baya cikin dakin da alama wanka yashiga,ajiye masa tayi akan center table tana kokarin fita yafito,

“Ina zaki? Zo…”

Ahankali tajuyo bayan tayi kasa da kanta ta nufeshi,zama yayi gefen gado sannan yakamo hannunta da nashi,

“Dauko min cream din can na shafa….”

Asanyaye ta karasa gaban mirror ta dauko ta dawo batare da tasake kallonsa ba saboda iya farin wandone ajikinsa iya rabin cinyarsa, hannunta yasake kamawa sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa,

“Yaufa muna da baki amma kinsa na manta….” Ya karasa maganar yana kallon agogon dake ajiye kan bedside drawer, dan kallonsa tayi jin abinda yace wai itace tasa yamanta shi dai yasa,jin ana kiran sallar azahar yasashi tashi domin shiryawa dama ita kam tajima tana neman hanyar guduwa hakan yabata damar tserewa,

Cikin kwanaki biyu kacal har Hanan ta sauya,duk da ta rame amma hakan bai hana fatarta yin fresh ba dan har wani sulbi take yi tana sheki gefe daya kuma ga fargaba da ladama dake sake tsurar da ita tana faman karewa kamar kudin guzuri kana ganinta kaga amarya domin tayi wani irin kyau na musamman,

Yau dai takama ranar juma’a kuma yau Khalil yace mata su abbanta zasu zo shiyasa tun bayan fitar Khalil din ta shiga kitchen ta dorawa su abba girki,misalin karfe 1 na rana suka karaso shida yaya shamsu,murna wurin Hanan ba a magana nan ta shiga gabatar musu da kayan motsa baki da abinci,

Tana tare dasu suna gaisawa Abba nasanar da ita dalilin zuwansu Khalil yakaraso wannan dalilinne ma yasa bata gama jin abinda Abba keson sanar da itaba. Ita dai ta lura tsakanin Khalil da abbanta akwai aminci mai karfi domin yau dinma sai hira suke yi cikin raha da farin ciki kuma hatta abinci ma tare suka ci,

Bayan sallar la’asar Khalil yace ta fito suyi sallama dasu abba zasu wuce,wasu hawaye ne suka fara kokarin zubo mata tun kafin ta karasa,

“Uwar masu gida…. Mijinki yadage akan lallai lallai sai naje k’asar chairo anduba ni saboda wannan ciwon nawa duk da nace masa yabar kudinsa amma yadage….. Kici gaba da yiwa mijinki biyayya, Allah yayi muku albarka,tare da shamsuddini zamu tafi”

“To Abba Allah yasa aje asa’a, Allah yabaka lafiya…”

Hawaye ne suka cigaba da wanke mata fuska har su Abba suka tafi tare da Attahir drivern Khalil wanda yadauki Aryan suka tafi,duk abinda take yi Khalil na ganinta,ganin ta zauna kan kujera tana kuka yasashi karasowa hannunta yakamo ya hadata da jikinsa ahaka yanufi sashensa da ita…………………………….鉁嶐煆?

_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/15/20, 3:50 PM – Ummi Tandama: 50

***Tana rungume ajikinsa har cikin falonshi wanda ya wadatu da sansanyan kamshi mai dadi,

Zama yayi kan kujera ya zaunar da ita ajikinsa yana kallonta,

“Wannan kukan na menene…..? Meyasa wai bakya girma da kuka ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button