MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Jin abinda yace yasata sake bare baki taci gaba da kukanta,kukan ne ya tsaya cak sakamakon harshensa da taji kan fuskarta yana kokarin lashe hawayen dake gudana kan fuskarta, cigaba yayi da lashe mata hawayen daga karshe ya tsaya akan dan kyakkyawan bakinta dake karawa fuskarta kyau da annuri,
Sun jima kadan aduniyar masoya mai cike da tsantsar so,kulawa da kuma farin ciki marar yankewa,dago lumsassun idanuwanshi yayi ya kalli nata idanuwan dake lumshe tayi luff tana amsar sakonnin da yake kokarin bata, hannunshi cikin rigarta yafurta,
“Tashi kije ki hado min coffee…..”
Bubu shiri ta bude idonta,hada ido sukayi ta mayar da nata ta rufe tana makale masa kafada alamun A’a, murmushi yayi yashafi kanta,
“Yaushe kika fara kiwa?”
Shiru tayi bata ce komai ba,saida ya tabbatar ta saki zuciyarta kukan yatafi sannan yafita,ita kam cigaba da kwanciyar ta tayi har tsawon wani lokaci,saima da su Aryan suka dawo ne sannan ta samu ta tashi tabishi zuwa dakin kayan wasanshi wanda har aka kira magriba suna ciki bata saniba lokacin Khalil har yadawo yaje ya dauro alwala yashiga part dinta bai gansu ba,da yaje wurin umma shine take sanar dashi wai watakila suna garden ko kuma yaduba su dakin kayan wasan Aryan,
Yana bude kofar dakin kuwa ya hango Aryan akan dokin wasanshi mai taya ita kuma tana zaune kan kekensa,ta bayanta ya lallaba yaje ya rufe mata ido,wani gwauron numfashi taja sannan cikin faduwar gaba tace,
“Uncle….” Sakamakon kamshin turaren jikinsa da taji,
“Baku san lokacin salla yayi bane? Wasan ya isa haka sai kuma gobe, Aryan zo mutafi salla…”
Mikewa tayi daga kan keken babu zato taji ya hadata da jikinshi ta baya bayan yakamo waist dinta,kwacewa tayi ta gudu tafice daga cikin dakin,
Alwala taje itama tayi tai salla duk mamakinsa yacika ruhinta lallai ashe shima Khalil dan yine amma shine take yimasa kallon salihi,miskili ma’abocin girman kai da dagawa koda yake duk wanda bai fahimceshi ba kallon da zaiyi masa kenan saboda shi ko magana bai fiya sakin baki yayita yinta ba komai atakaice yake fadarshi,wurin umma ta sauka wanda can ta iske Aryan umma nabashi tuwo,
Bayan sallar ishah sashen Khalil suka shiga ita da Aryan,zaune suka sameshi da laptop akan cinyarshi ga kuma waya makale a kunnenshi yanayi,
“Agogo sarkin aiki…..” Ta fada acikin ranta,samun wuri tayi ta zauna idanuwanta akan TV amma jikinta na bata idanuwan Khalil akanta suke domin duk tajita atakure takasa sakewa,dan satar wurin da yake tayi nan taga yayi mata kyarr da ido ko kiftawa bayayi,amma koda suka hada ido sai ya basar,tun safe ya lura da ita bata sakin jikinta yanda yakamata sai wani dingishi dingishi take yi tana tafiya kamar wacce ke taka kaya,
Sai bayan da yagama wayar sannan yamayar da hankalinsa kan Aryan wanda ke kokarin yimasa ta’adi ajikin laptop dinshi,tana jinsu bata tanka ba har tsawon wani lokaci ahaka bacci ya dauke Aryan yana kan cinyar Khalil,
“Zo….” Taji yace idanuwanshi na kan system dinshi,kamar bata so haka ta tashi ta nufeshi tanata faman harararshi ta gefen ido saboda ita kadai tasan irin wahalar da yabata duk yabi ya raunatata,
“Gani….”
Daga kanshi yayi ya kalleta sannan ahankali yace,
“Wai meke damunki ne naga kina yin komai sanyi sanyi…. Baki jin dadi ne?”
Saida ta dan turo baki sannan tace,
“Ni lafiyata kalau…”
Murmushi yayi acikin zuciyarsa yace, “to za ayi min halin ne na rashin kunya?”
Amma afili kuma sai yace,
“To shikenan tunda lafiyar ki kalau”
Aryan ta dauka ta fita,saida ta kaishi dakinsa ta kwantar dashi sannan ta wuce nata part din ta yi wanka da ruwan zafi sannan tazo ta shasshafa turare da humra masu kamshi sosai wadanda ke sanyawa zuciya nutsuwa,wata farar rigar bacci ta saka marar nauyi sannan ta dora dogon hijabi pink ta fita bayan ta dauki wayarta,ita kanta bata san dalilinta na zuwa sashensa ba amma dai haka kawai ta tsinci kanta da nufar sashen,
Lokacin da ta shiga bedroom din nasa yana gefen gado kwance yana waya da sabon PA dinsa,katse wayar yayi sannan ya mika mata hannu,cike da kunya ta kama nasa nan yajata jikinsa,
“Tashi ki kawo min coffee….”
Makale kafada tayi kamar dazu,
“Jikinane babu karfi,bacci kuma nake son inyi”
Duk da taji abinda yace kin tashi tayi domin atsorace take dashi,
“Ok ni bari naje da kaina…”
Tun kafin ya karasa ta rikeshi gam gam ta yadda bazai iya tashi ba,
“Nidinma banida ikon zuwa da kan nawa?”
“Uhmm” tafada tana mai daga masa kai,
“To shikenan kwanta kiyi bacci….”
Kin kwanciyar tayi har saida ta tabbatar cewa dagaske shima baccin zaiyi, ajikinsa ya rungume ta tsantsan yana shakar kamshinta.
Hakace taci gaba da faruwa duk Hanan tabi ta sakawa ranta tsoro da fargaba wannan dalilinne yasa har gobe bata dan murmure ba gaba daya ma ji take yi kamar ta tafi gidansu ta huta amma abun haushi ranar da Khalil yasa aka kaita kanon ma wuni guda tayi ta dawo yaki yabarta ta kwana haka ta kwana tanata yimasa buntsire buntsiren baki tunda tafi kowa sanin dalilin nashi na hanata ta kwana,
Bayan zuwanta kano da kwana biyu suka tafi gombe gaba dayansu saboda bikin saukar alqur’ani da zasu halarta na su Sarah,tunda sukaje hajiya ta sake jan Hanan ajikinta domin ta sake karewa amma kuma tayi kyau ba laifi,ranar walimar kuwa har anty maamy Hanan tagani amma ko gaisawa basuyi ba saboda suna zazzaune su uku da Lubnah da Muneerat da anty maamy tazo sai kawai ta tsallake Hanan ta gaggaisa da sauran tabe baki Hanan tayi aranta taje aje dai tunda ba aurar mata miji ba,
Washe gari khalil yace su shirya zasu koma nan hajiya tace A’a yaje shi kadai su Hanan yabarsu su dan huta tunda ba zuwa suke yiba sai ta kama,badan yasoba haka yasa Aryan agaba suka tafi saboda shi yana zuwa makaranta, Hanan kam murna tarinka yi har acikin zuciyarta dan ko babu komai zata huta da fitinar Khalil,
Tun bayan tafiyar su hajiya ta maida hankali wurin kulawa da Hanan tana sake gyara ta ta hanyar sawa ahado mata tukudi na musamman domin wannan ramar tata bata yiwa hajiya dadi, kullum suna waya da Khalil da Aryan wanda gidan sam baya yimusu dadi saboda rashinta,
Satinta biyu Khalil yazo daurin aure kuma yasamu ya karaso gidan lokacin da yaga Hanan sai yaga ta dan murmure ba kamar daba, murmushi yayi ya shafi kumatunta yana fadin,
“Yar gidan hajiya me hajiyan take baki ne kike cika haka?”
“Bacci”
Wani murmushin yasake yi,
“Bacci take barinki kiyi? Wato nan kuma dani akeyi kenan ana nuna min nine ke hanaki bacci ko? Zaki dawone”
Makale kafada tayi tana cewa saita fadawa hajiya,ranar ma duk yanda yaso sutafi tare da ita sukoma Abuja hajiya cewa tayi yabarta ta kara kwana biyu,bai damuba saboda shi kadai yasan shirin da yakeyi.
Bayan tafiyar shi da kwana uku yaturo driver yazo ya tafi da ita wai akwai inda zata rakashi,aranar da ta koma aka gama dukkan shirye shirye bayan sallar magriba driver yakaita airport wanda wannan shine karo nafarko da zata hau jirgin sama atarihin rayuwarta,gabanta sai dar dar yake,tana shiga taganshi tsaye yana jiranta sanye da kananan kaya jeans da t shirt,tare suka zauna ga kujerarshi ga tata yana rike da hannunta,
“Yau kuma gudu ya kare ko? Zamuje inda babu hajiya ai sai muga ta karyar gudu”