MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

“Dan Allah kayi hakuri…..” Tafada idanuwanta na cikowa da kwalla,
“Ban hakura…”
Kuka tafara yi hakan yabashi damar dan rungume ta kadan yana shafar bayanta babu bata lokaci bacci ya dauketa ba ita ta tashi ba saida jirginsu ya sauka,
Yana rike da ita har cikin motar da zata sadasu da lafiyayyen hotel din da zasu sauka,ita kam yar kauye ta zama domin bata taba ganin hadadden birni makamancin wannan ba ko acikin mafarki kasa boye kauyancinta tayi har saida takaita ga tambayar shi lokacin motarsu na tsakiyar titi suna lilawa,
“Uncle nan inane?”
“Rome…… K’asar Italy”
Lumshe idanuwanta tayi ta kwantar da kanta akafadarshi bayan ta makaleshi kamar tana jin tsoron kada wani ya kwace mata shi,basuyi wata doguwar tafiya ba suka isa hotel din da zasu sauka. Ayanda ta dan lura kamar yana mutukar son k’asar Italy domin yana yawan zuwa akai akai,
Lokacin da suka shiga masaukinsu amutukar gajiye suke duk da cewa dai ba wani aiki suka yiba inbanda zama to amma zaman ma wani lokacin sai ahankali,
Itace tafara shiga bathroom domin yin wanka shikuma yana zaune yana duba wayarshi wacce take akashe tun bayan shigarshi jirgi sai yanzu ya kunna,sak’onni ne rututu suketa kokawar shigowa har har Hanan tafito kasancewar ba wani jimawa tayi ba kawai ta dan watsa ruwane ajikinta gashi tana fashin salla,
Yana zaune inda ta tafi tabarshi ta bude trolley bag dinta ta ciro pad da pant,dan daga kai yayi ya kalleta ganin pad din dake hannunta yasashi dan tsuke fuska,dan karamin tsaki yaja sannan ya ajiye wayoyinshi yawuce bathroom yana wani ciccin magani,
Kafin yafito ta samu ta shirya agaugauce tana kokarin saka night gown yafito saida ya harareta sannan taji yace,
“Karki saka wannan rigar baccin bana bukata….”
Daga haka yawuce gaban kayansa yabarta tsaye rike da riga ahannu, kayan baccinsa ya dauka zai saka hakan yasata juyawa tafita zuwa falo ta nemi wuri ta zauna ita bata saka rigarba sannan kuma ita bata ajiye ba,
Shi kam bayan ya gama shiryawa cikin fararen kayan baccinsa sallolin dake kansa yasoma gabatarwa,yana cikin sallar Hanan tashigo cikin dakin fuskarta awani rakwarkwabe kamar zata fashe da kuka,gefen gado tasamu ta zauna har lokacin tana rike da rigarta ahannu,tana nan zaune tana dan gyangyadi ya idar da sallar baiyi mata magana ba yatashi yafita mintuna kadan yadawo dauke da abinci,
“Sauko kici abinci….”
Batare da tayi musu ba ta sauka ta zauna suka fara cin abincin sai wani shasshan kamshi yake yi domin shi duk zatonshi Allah ya amshi addu’ar shi tasamu juna biyu tun a first night ashe da sauranshi,
Shine yafara tashi sannan yahaye gado ya bararraje yana latsa wayar shi ahaka itama tagama ta zauna saman gadon adan darare kamar mai jin tsoron wani abu, hannu yamika mata kamar koda yaushe takama sannan yajata jikinsa ya rungume cikin sanyin murya taji yana cemata,
“Tunda ga duvet yau bana bukatar wannan rigar baccin taki mai takura mutum…….”
Ita kam ji tayi kamar ta nutse saboda tsananin kunyarshi,wai meyasa shi baya jin nauyinta ne? Har yagama rashin kunyarsa ita dai bata motsa ba haka idanuwanta ma bata budesu ba gashi inbanda bacci babu abinda take bukata amma koda tayi korafi sai cewa yayi ai yanzu lokacinsa ne ba lokacin bacci ba.
***
Kimanin watanni bakwai kenan da bikin mujahid da sumayya wacce yanzu haka take dauke da cikinta dan kimanin watanni bakwai din kuma tuni har ya bayyana tunda jimawa,
Zaune take afalo tana gogewa mujahid k’ananan kayanshi gefe daya kuma tana kallon tashar dake haska finanan turanci inda take kallon wani kayataccen Nigerian film mai suna the perfect couples,ahankali taga yabude kofa yashigo,musayar murmushi suka yiwa junansu sannan yazo ya dan rungumeta kadan ta bayanta,
“Matar alkhairi sannu da kokari…..”
“Sannu da zuwa mijin arziki”
Dariya yayi yashafi cikinta,
“Ya babynmu?”
“Baby na lafiya dazun nan tagama motsi”
Murmushi yayi yai zaman dirsham shima kamar yadda yaga tayi sannan ya karbi gugar yaci gaba dayi,
“Kin san wani abu? Har yanzu inata nazarin sunan da yadace musakawa babynmu…..”
“Wanne kake ganin zamu saka mata”
Kashe iron din yayi ya zuba mata ido,
“Akwai sunan da najima inada burin sakawa ‘yata (Sa’adatu Hanan)”
Murmushi tayi ta gyara zamanta sannan ta kalleshi tana murmushi,
“To yanzun me zai hana ka cika wannan burin naka kayi mata takwara?”
“A’a ni tsorona kar kice da biyu nasaka sunan Hanan”
“Kaji yaya mujahid da wani magana,to ni ina ruwana dan kasawa yarka duk sunan da kayi niyya? Ni ai nadaina kishi da Hanan”
Murmushi yayi yasake rungumeta yana saka mata albarka tare da addu’ar sauka lafiya.
***
Washe gari Hanan bata tashi daga bacci da wuriba kasancewar ga uwar gajiyar da take addabarta sannan ga rashin bacci akan lokaci wannan dalilinne yasa har k’arfe 9 nasafe takai tana bacci batare da Khalil ya tasheta ba sanin ba salla zatayi ba, ahankali take bude idonta kamar bata so ko mai tsoron ganin wani abu tayi luff cikin bargo,bata ga Khalil ba hakan yabata damar cigaba da kalle kallenta acikin d’akin ahaka har idanuwanta suka sauka akan tamfatsetsen mirror din dake cikin dakin,
_Good morning beautiful!_
Abinda taga anrubuta kenan baro baro ajikin mirror din da red din janbaki, murmushi tayi ta tashi zaune tashiga wanka tana sake yaba kyau da haduwar hotel din wanda Allah ne kadai yasan adadin kudin da Khalil din yabiya,cikin farin ciki da annashuwa tayi wanka tafito tazo ta shirya cikin wata bakar riga iya gwiwa,tana kokarin fesa turare yashigo dauke da breakfast a hannunshi,tsayawa yayi kawai yana kallonta saboda ba karamin kyau tayiba,
Kayan hannunshi ta karba sannan ta danyi dage ta yiwa kumatunsa kiss,
“Good morning Uncle”
Rungumeta yayi yana shafar kumatunta,
“Morning mai period,how was your night?”
Murmushi tayi ta lumshe idanuwanta saboda ta lura period dinnan nata ya tsaya masa arai kuma yana jin haushinsa dan tun jiya yaketa faman yin tsaki da yaga pad,zaunar da ita yayi kan cinyarsa sukayi breakfast daga nan kwanciya suka sake yi har lokacin sallar azahar,zuwa yamma taci gayunta cikin jar doguwar gown mai stones tayi rolling suka fita,shi kansa Khalil din shima kananan kaya yasaka da black face ya sakaye fuskarshi,yana rike da hannunta suka rinka zuwa wurare daban daban na shakatawa da debe kewa sunata yin video call da Aryan,gaskiya k’asar tayi mata kyau sannan ta burgeta domin birnine na can kololuwar karshe basu suka koma gida ba sai karfe dayan dare amutukar gajiye. Ai ita kam kasa tabuka abun arziki tayi duk da taga shi lamarin nasa ba sauki,hannayenta ya kama gaba daya yakai jikinsa cikin rada yake cemata,
“Ke yar kauye ce……, Kamar kina tsoron tabani,ko har yanzu kunyar ce bata gama sakinki ba? Kin barni inata wahala ni kadai bayan ba wani abu zan samuba…… Kema kiyi wani abu”
Ahankali hudubar su anty badi’a tafara dawo mata cikin kwakwalwarta tiryan tiryan wacce suka yimata a gombe lokacin da za akawo ta,ji tayi kamar yanzu ne suke yimata amma kuma bata san ta yadda zata tunkareshi da wannan babban lamari ba saboda wallahi tana bala’in jin kunya ga tsoro wanda bata san ko na menene ba,
“Wai ke waya fada miki idan akazo wannan bangaren ana jin kunya? Idan haka zaki rinka barina babu kulawa,babu tarairaya sai dai kisaka ni gaba da kuka muna komawa gida zanyi aure……”