MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Ai tana jin haka bata san lokacin da ta bude idanuwanta ta kalleshi ba,
“Aure uncle……?” Ta tambayeshi bakinta har yana rawa,juyawa yayi yai rigingine batare da ya kalleta ba yace,
“Yes aure…… Kuma bazawara zan aura wacce tasan aure tasan yanda zata kula dani”
Shiru tayi tana kallonsa nan zuciyarta tasoma bugawa da wani irin karfi wanda tafi kyautata zaton na tsantsar kishine,gaskiya tana da zafin kishi na ajin karshe akansa,shima sanin tana da zafin kishin ne yasashi fadin haka ko wai zata nutsu ta gyara tunda yaga abin nata kamar harda sakarci,
Nutsuwa tayi tana saurarar fadan da zuciyarta keyi mata “kema hanan kina abu kamar wawiya, tunda har yafito ya nuna miki ga abinda yake so meyasa bazaki daure ki cije kiyi masa ba? Gashi nan ai kuna komawa gida yace zaiyi aure waya sanima ko mijin anty maamy ya mutu ya aureta shikenan kin zama yar kallo….” Wata kwalla taji ta zubo mata nan ta share kwallar sannan cikin sanyin murya tace,
“Uncle….. Kayi hakuri bazan sakeba”
Shiru taji yayi mata cikin dar dar taja jikinta zuwa gareshi ta rungumeshi tare da yimasa wani lafiyayyen kiss a kumatunsa irin yanda yake yimata, rungume ta taji yayi sannan cikin farin ciki taji yace,
“Yawwa to ko kefa,amma da kamar ba yar makaranta ba….. Ai ko a school ana practical ko?”
Kai ta daga masa,
“To kema lokacin da zaki fara practicing abubuwan da na koya miki yayi…. Don’t be shy”
“Kai Abban Aryan akwai rashin ta ido….” Ta fada acikin zuciyarta,kamar mai shirin taba wutar lantarki haka take tabashi awani d’arare,haka dai da taimakon sa da komai ta dan tabuka abun arziki, rungume ta yayi yana cemata har yanzu batayi wani abun azo ayaba mata ba,yana shafar kanta har bacci ya dauketa shi kam tashi yayi ya tsaftace jikinsa ya dan gabatar da sallolin nafilfili zuwa karfe 3 na dare yaje ya kwanta abayanta tare shiga cikin jikinta sosai. Tsabar gajiyar da tayi ai har gari yawaye bata ko juya ba,shima Khalil din yau saida yamakara sallar asubah.
Ta rigashi tashi,bayan tafito daga wanka tana shiryawa shima yafarka,wankan yashiga shima yayi yafito rike da dan karamin towel daga shi sai gajeren wando,
Zaune yaganta tana kokarin daure gashinta ta saka wata yeluwar riga mai budadden kirji amma dan kauyanci sai ta saka mayafi karami ta rufe kirjin nata, zama yayi gefen gado yace,
“Zo kibani wannan jakar…..”
Tana zuwa ya yaye mayafin yana fadin,
“Ba kiji abinda nafada miki jiya ba ko? Kina son nakara auren dai kenan…..”
Girgiza kai tayi tana bata fuska,kan cinyarsa yadorata sannan cikin taushin murya yace,
“Zan auro yar birni tunda ke yar kauye ce,zan auro wacce ta iya soyayya,wacce zata rinka barmin surarta abude koda yaushe ina gani ba irinki da kike rufewa ba….”
“Nadaina…..” Ta fada tana turo baki,shiru yayi mata yamaida kallonsa kan kirjinta wanda ya bayyana ta saman rigar da ta saka,
“Kaji uncle….” Kunya ce ta kamata lokacin da ta fuskanci abinda yake kallo,babu yanda ta iya haka ta daure ta biyeshi kafin daga bisani sukayi breakfast bayan yayi sallar azahar suka fita. Yauma kamar jiya sunsha yawace yawace dan basu suka dawo ba sai karfe 1:30 nadare, kuma yau dinma bai barta tasamu bacci ba sai wurin karfe 3 saura kwata shiyasa washe gari babu inda suka je a masauki suka wuni suna shan baccinsu sai da daddare ne suka samu dan fita gaban harabar hotel din suka mike kafa suka dawo, Hanan dai tana jin dadin kasar saboda ko ina ya hadu ashe shiyasa Khalil idan yazo yakoma suke ganin ya canja yayi kyau kamar wanda aka canjawa halitta ko fata.
Yau kam tun asubah suka fita tana sanye cikin purple din Dubai gown ta dan yafa mayafi karami akanta kafarta tasaka takalmi toms shima purple sai yar karamar side bag wacce ta rataya hannunta cikin na Khalil wanda yake sanye da fararen jeans da t shirt fuskarsa boye cikin bakin gilashin ido mai dan girma,kai masha Allah dan kasa boye farin cikinta tayi sai daukarsu selfie take ta faman yi har suka shiga cikin wani kyakkyawan jirgin ruwa mai daukar akalla mutane goma,tana zaune gefenshi ga kugunta ga nasa ya rike waist dinta da hannayensa kanta bisa kafadarshi. Sunyi doguwar tafiya har gari ya waye rana ta dan fito duk da bawai ranar mai kwal dinnan bace,awani hamshakin katafaren bakin ruwa suka sauka gaba daya ruwan kalarsa blue ce mai sheki da daukar ido sai ambaliya yake yi ga mutane tsilla tsilla suna hada hadarsu,kamata Khalil yayi yafito da ita yana rike da hannunta,
“Wai uncle ta ina duk kasan wadannan wuraren…..?”
“Tun ina yaro nake mafarkin zuwa wadannan manyan biranen na duniya tare da wata cute baby…..”
Wani kyakkyawan masauki wanda aka gina akan tsauni atsakiyar ruwan suka je can Hanan tayita baje idanuwa tana kallo gaba daya takasa bambance tsakanin can Rome inda suka sauka da nan Florence ina ne yafi wani haduwa,
Gaskiya Khalil yayi kuma ya hadu domin ya zagaya da ita taga wurare ta karkashe kwarkwatar idonta sosai kuma ayanda ta lura shima dan harka ne wato dan soyayya ma’abocin son ashana da iyali,basu suka koma Rome ba sai dab da asubah,ko ba afada mata ba tasan gogan nata mutum ne mai son yawace yawace da harkar bude ido saboda ko agida Nigeria ba zama yake ba bare nan da yakeda yancin zuwa duk inda yake so. Kwanansu biyu adaki babu inda suke zuwa tun bayan dawowarsu daga Florence sai dai suci abinci susha soyayya suyi waya da yan gida,
Yammacin yau yagama shirya musu kayansu tsaf suka kara gaba zuwa birnin Venice dake nan k’asar ta Italy, Hanan duk da tana cikin murna da farin cikin zuwa wuraren da bata taba mafarkin zuwa ba amma adarare take da Khalil saboda yau zata samu tsarki duk da kwana biyu tasake dashi tunda suna zaune daki daya zasu kwana tare zasu tashi tare su wuni tare,
Yanzunma awani dan karamin hadadden hotel suka sauka,bayan sunci abinci sunyi salla Khalil yafita shi kadai yace ita ta kwanta tayi bacci,baccinta kuwa tasha kamar yadda yace,zuwa magriba yadawo hannunshi rike da wayarshi suna yin video call da Aryan,karbar wayar tayi suna yiwa juna dariya itada Aryan ko dariyar ta mecece oho,har Khalil yayi wanka yafito yayi salla basu gama wayar ba da zasu ci abincine yakarbe wayarshi ya kashe.
Shiru tayi tai jugum tana jimamin wannan lamari Khalil yace tare zasu yi wanka saboda ya kyalla ido yaganta tana yin salla, tunaninta ne yatsaya daidai lokacin da yashigo cikin dakin kasa tayi da idonta lokacin da taga yana kokarin rage kayan jikinsa,
“Oya muje….”
Tashi tayi kamar kazar da kwai ya fashewa aciki tawuce gaba yana biye da ita abaya har cikin bathroom din wanda ya hadu karshen haduwa,janta yayi cikin ruwa bayan ya warware towel din jikinta,tun tana jin kunya har ta warware ta saki jiki,daman yau kam ita kanta tasan babu daga kafa domin kamar Khalil baida hakuri da kawaici a wannan bangaren,duk da yau taji lamarin da sauki sai dai amma akwai tarin gajiya da tarin bacci wadanda suka hadu suka yimata rubdugu shiyasa ta wuni tana bacci washe garin ranar. Zamansu a Venice yafi na ko ina tsaya mata arai domin acan ne suka fi kulawa da juna da tattala juna tunda yanzu tafi sakewa dashi wannan kunyar tata da Khalil ke kira da kauyanci ta dan rageta,kayan shan iska take sakawa na wulakanci suyi ta shanawarsu da daddare kuwa sallama take yi da kowacce irin suttura komai kankantarta domin saukakawa gwarzon nata,