MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Tunda Khalil yafada mata saura kwana biyu su koma gida duk take jin babu dadi kamar kar su tafi saboda yanzu tayi sabo dashi ta shaku dashi yanzu suna komawa gida zai fara yimata wahalar gani sai dare yau yana kano gobe yana bauchi,zama yayi kusa da ita yana murmushi shigowar shi kenan,
“Hey…… Meyake damunki ne?”
Shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka,
“Nasan idan muka koma gida zan daina ganinka koda yaushe……”
Murmushi yayi yakama hannunta yana matsawa ahankali,
“Kekuma kina son ganina koda yaushe ko?”
Kai ta daga masa kwalla na shirin sauko mata,hadata yayi da jikinsa yana bubbuga bayanta alamar kulawa da rarrashi, ahankali ya zaro wani dan karamin akwati daga cikin aljihunsa ya bude yaciro dan karamin zoben gold mai mutukar kyau ya kama yatsanta,saida yafara zira zoben cikin yatsanta na tsakiya sannan ta dago tana kallonsa cikin farin ciki tasake rungume shi tana cewa,
“Thank you uncle….”
“I love…..you…..” Yafada kamar mai koyon magana ai duk sai taji ta rude jin abinda yafito daga bakinsa kamar cikin mafarki,fuskarshi yasake mika mata taci gaba da yimasa ruwan kiss tako ina.
Ranar alhamis da yamma suka sauka a Nigeria,tsayawa kawai Khalil yayi yana kallon Hanan da Aryan lokacin da suka rukunkume juna suna murna,kamar yadda Hanan ta tsammata washe gari Khalil yasoma tafiye tafiyen nasa da yasaba kullum baya dawowa gidan sai dare wani lokacin ma sai tayi bacci. Wannan watanma da yaga tana period sai duk yabi ya bata rai ya tsuke fuska daga karshe sai cewa yayi umarah zai tura hajiya da umma barira da Aryan suje su tayashi da addu’a tasamu ciki tunda har yanzu yaji shiru,zaro ido Hanan tayi sannan cikin mamaki tace,
“Kai uncle dan rashin kunya hajiyan zaka fadawa haka?”
“Ni ai babu maganar da bamayi da hajiya,barima kiga…”
Ganin zai dauki wayarshi yasata rigashi dauka ta gudu,silifas dinshi yasaka yabi bayanta har zuwa sashenta,tsaye ya sameta a corridor tana yimasa bincike awayar,
“Duk abinda kika gani babu ruwana bincikenki ne yaja miki dan nayi budurwa jiya”
Murmushi tayi tai tsalle ta dale bayansa tana tambayar shi wai ina nura PA saboda kwana biyu bata ganinsa,riketa yayi Sosai abayanshi sannan yabata amsa,
“Na koreshi tun tuni……”
“Saboda me?”
“Saboda naga yana kokarin shiga gonata…….”
“To Uncle kuma basai kabarshi ba iyakaci fa idan yagama nomanshi ya…..”
Bata karasa ba taji ya birkitota tadawo gaba, makalkale shi tayi da kafafuwanta idonta cikin nashi yake kallonta,
“Kin kuwa san abinda kike fada? Shine fa wannan da yarinka yimiki text massage dinnan,harda sake sabon layi saboda yazaci bazan ganeshi ba…..”
Shiru tayi aranta tana cewa lallai kam biri yayi kama da mutum ashe shiyasa idan yashigo cikin gidan koda yaushe idonshi akanta. Kamar yadda Khalil yace saida yatura hajiya da umma barira umarah amma banda Aryan saboda shi lokacin suna yin exams a school shiyasa Khalil yajira sai bayan yagama,suna yin hutu kuwa suka tafi tasu umarar shida Aryan da Hanan,bayan sun gama suka nufi k’asar Scotland daga can kuma suka wuce Australia, Hanan kam taga manya manyan biranen duniya kuma tasha tarairaya wurin Khalil,tun daga can take jin jikinta yana wani canja mata bata jinsa daidai amma dai bata fadawa Khalil ba har suka dawo gida Nigeria nan abu yaci gaba da karuwa kasala da ciwon jiki ga kuma yawan bacci dake damunta ganin duk kuzarinta ya ragu yasa Khalil kiran Dr Al’amin,test din farko da Dr yayi mata ya fahimci tana da juna biyu, Khalil ji yayi kamar ya goyata har Aryan yarinka fadawa wai yakusa yasamu sister ko brother,ita kam kyautar wata dambasheshiyar sarkar diamond yabata kuma tun daga ranar kulawar da yake bata ta karu lallaba ta yake yi kamar kwai. Koda cikin yagirma kuwa ai Hanan daina fita tayi wai ita kunya take ji kaza da kaza dariya Khalil yarinka yimata shikam yawonsa bashi nan bashi can yau yana wannan kasa gobe yana waccan……………………………..鉁嶐煆?
_Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/17/20, 9:07 PM – Ummi Tandama: *Littafina na kudine ga duk wacce keda bukatar karantawa saita turo naira 200 ta account dina 3112877210 Aishatu Ibrahim first bank,sai aturo shaidar biya ta wannan number din 07044644433 ko kuma recharge card na MTN ko atuntubi marubuciyar kai tsaye ta wannan number din 07044644433*
*51*
***Fad’ar irin kulawar da Khalil ke baiwa Hanan bata bakine ko kuma kauyanci domin yanzu ne tagane ainihin irin soyayyar da yake ikirarin yana yimata kuma hatta hotunan Ramlat da ada yake ajiye dasu akan drawer gefen gadon baccinsa ayanzu duk ya kwashesu ya adana a inda yadace,
Hanan haihuwa ko yau ko gobe domin cikinta yagama tsufa kuma ya isa haihuwa,tunda ta tashi yau dai haka haka take jin jikinta amma da yake bata san takan abunba shiyasa bata kawo cewa haihuwa bace kuma dama jiya a sashen Khalil ta kwana shikuma sai shegen rashin hakuri duk da ga halin da take ciki lallabata yake yasha sha’aninsa, asubanci yayi yau yafita zaije kasar Ghana,
Abinci ta zubo soyayyen dankali da farfesun hanta ta zauna kenan agefen kujera taji wani abu ya tsurkuneta haka dai ta daure ta cuccusa dankalin tasha ruwa nanfa taji ciwo kamar karuwa yakeyi kafin wani lokaci har ciwon ya tsananta,umma ta kira awaya babu bata lokaci suka tafi asibitin da take zuwa awo wato alkhairi clinic and maternity,
Tun safe take nakuda amma har dare bata haihu ba, khalil yana can amma hankalinsa yana gida musamman ma da yakira hanan bai sameta ba wayar umma da Aryan kuma duk ba adauka idan yakira, daren ranar Hanan bata yi bacci ba saboda da ciwon nakudar ta kwana zuwa asuba ta haifo katon jaririnta sambalele,dakyar ta iya bacci saboda azabar da take ji atare da ita karshe ma saida aka hada da yimata allurar bacci,sai lokacin umma tasamu zarafin kiran yan uwa da abokan arziki ta sanar musu da haihuwar Hanan, ai tun aranar yan uwa suka yiwa garin Abuja cincirindo dan asibitin cika yayi taf da yan uwan Khalil da na Hanan shima Khalil adaren ranar yadawo, lokacin da yashiga d’akin tana kwance angama yimata karin ruwa tana bacci,goshinta yayi kissing ya shafi kumatunta sannan yafita cikeda farin ciki marar misaltuwa,ita Hanan bata san yanayi ba saboda baccine take yinsa kamar wata yar kwaya ga uban ciwon dake damunta wanda bai saketa ba har yanzu. Washe gari tunda sassafe Khalil yadawo asibitin shida Aryan,zuba musu Ido kawai tayi tana kallonsu saboda yadda suketa murna suna kwakwume da jaririn wanda Khalil yayiwa huduba da Muhammad Ayaan,
Kwananta uku suka koma gida kuma aranar kaf yan gidansu suka zo kafatanin ilahirinsu dan harda mamaye,ganin girman jaririn yasa anty salaha cewa ai dole tasha wahala ji jariri kamar dan kwana arba’in? Ita dai bata ma magana dan ko zama saida dabara sakamakon irin uban dinkin da tasha,tafiya ma wannan ba son yinta take yiba sai ta zama dole,
Lura da yanda take ciccije lips idan tana zaune ko tana tafiya Khalil yayi nan yasata agaba da tambayar menene matsalar? Turo baki tayi cikin shagwaba tace,