MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

“Nida aka dinkeni kamar bayan kwarya……”
“Insha Allah anyi nafarko kuma anyi na karshe ai hakan bazata sake faruwa ba…”
Jin abinda yace yasata yin watsi ma da maganar saboda duk tunaninta bazai iya yin abinda yafada ba bata san shi abinda yake nufi ba shine bazai sake barinta ta haihu a k’asar nan ba gara yafitar da ita k’asashen ketare koda kuwa tattalin arzikinsa zai kare. Haka dai akayi suna aka gama mai jego babu cikakkiyar lafiya,anty salaha da umma barira sune ke tare da ita suna kula da ita,bayan suna da kwana biyu taji kamar akwai matsala nan ta fadawa anty salaha babu shiri suka koma asibiti wani dinkin aka sake yimata domin wancan ya warware,da kuka suka dawo gida tana ta kuka ahaka Khalil yazo ya sameta. Zama yayi kusa da ita ya rungumota jikinsa yana rarrashinta,
“Uncle zafi mutum kamar zai suma ko zai mutu ni wallahi bazan kara haihuwa ba ma……”
“A’a sa’adah,wahala ai mai wucewa ce insha Allah bazaki sake shan wahala kamar wannan ba wurin haihuwa….. ” Dakyar yasamu ya rarrasheta ta yi shiru ta daina kukan nan aka cigaba da lallaba ta su umma na kulawa da ita,shi kuwa jariri dayake yana samun abincinsa yana koshi nan da nan yasake zama kato dan ko Aryan baya iya daukarsa sai dai idan yana zaune abashi shi,itama mai jegon ba abarta abaya ba wurin murmurewa da sake kara samun kumari domin itama ta cika tayi kiba kamar ba itaba sai yanzu ta yarda da batun mutane da suke cewa kudi na gyara mutum haka duk muninka yana kara maka kyau,kafin arba’in tasamu ta warke tayi fess da ita amma duk da haka bata sakin jiki da khalil kuma shima baya takurawa saboda yana son ta huta sosai,kullum da daddare dai yana kasancewa dasu itada Aryan da Ayaan su raba dare a sashensa suna hira,anty salaha kuwa ganin Hanan ta warke yasata tattarawa ta tafi saboda tabar yara agida duk hankalinta yana garesu,
Tunda anty salaha ta tafi kuma Hanan ta koma sashen Khalil da kwana itada jararinsu can suke tafiya suyi baccinsu cikin nutsuwa da kulawa domin ko tashin dare Ayaan yayi zaiyi rigima khalil ke daukarsa ya rarrasheshi. Watan Ayaan biyu Hanan ta shirya ta tafi gida kuma itace har gombe domin ziyara tayi ba kadanba saida tayi sati biyu taje nan taje can duk wasu danginta da na Khalil lungu da sako babu inda bata je ba takai Ayaan anganshi wanda kamarsu daya da Aryan saboda duk Khalil suka debo,
Kafin ta baro gombe saida aka yimata kunshi da kitso sannan Zaid ya mayar da ita, lokacin da ta koma bata samu Khalil ba domin yatafi k’asar chairo wanda bata san dalili ba,gyara jikinta taci gaba dayi har izuwa ranar da zai dawo,bayan dawowarta da kwana biyu shima ya sauka amma office yawuce bai karaso gida ba sai dare,
Kwalliya taci sosai cikin doguwar riga ta material tasha turare mai sanyin kamshi,yana dauke da Ayaan a kafadarsa wanda ya karbeshi hannun umma Aryan na biye dashi,
A sashensa ya sameta tana shirya masa table ganin irin adon da ta caba yasashi yin murmushi ya nemi wuri ya zauna,
“Sannu da zuwa uncle….”
“Yawwa…. Irin wannan kwalliya haka? Ko anshirya karbata ne yau?”
Murmushi tayi ta karasa kusa dasu,
“Kai uncle…..”
“Ai tambaya nayi,kuma shiyasa nayi miki da yaren da Aryan bazai ganeba, anshirya karbata yau?”
Kafada ta makale tace “A’a”
“Karya kike yau dai dole akarbeni tunda ai anhuta kuma zafin haihuwar yatafi….”
Dariya tayi ta mika hannu ta karbi Ayaan tana fadin,
“Zo nan mubar uncle yaje ya shirya yazo yaci abinci…”
Tare suka rankaya zuwa dakin nasa banda Aryan wanda yakoma wurin umma,ita ta taimaka masa yayi wanka sannan ya shirya cikin kayan shan iska saboda shi mutumne mai jin zafi gashi baida wata kiba ta azo agani amma sai jin zafi,falo suka koma ta bashi abinci yaci daga nan tatafi sashenta domin yin shirin bacci. Yau kam tayi shirin da Khalil bazai kirata da yar kauye ba itama yar birni ta zama domin rigar baccin da ta saka kadai ta isa tabbatar masa da haka kuma kalar da yafi murada ce wato fari,
Yana zaune rike da wani littafi a hannunsa kishingide saman sofa acikin bedroom dinsa ta shiga,bayan ta kwantar da Ayaan ta nufeshi,acikin jikinsa ta zauna tana cire hijabin dake jikinta,
“Wow……. Kinyi kyau” yafada yana shafa kitson kanta,tun anan labari yasoma canjawa har suka dangana ga gadon barcinshi amma kuma yau sam ta lura kamar baida kuzari kai kamar ma dan ita yake jagorantar tafiyar bawai dan kanshi ba,
“Uncle ko inkawo maka coffee din ne?”
“No”
Ita dai yau ganinsa take yi kamar wani marar lafiya kuma duk zumudinsa yau kam jikinsa asanyaye yake,
Bayan wani dogon lokaci tayi bacci ta farka ta ganshi zaune ya tallafe kumatunsa da hannunshi abin yayi mutukar bata mamaki, cike da bacci ta tashi zaune,
“Uncle wai lafiya kuwa? Meke damunka ne?”
Kamata yayi suka kwanta ya kwantar da kanshi a kirjinta bayan ya rungume ta,
“Babu abinda ke damuna,muyi bacci…”
“A’a uncle wallahi da akwai abinda ke damunka…”
“Babu”
Jin yaki fada mata yasata tureshi ta mike zata bar dakin tana masifa,
“Tunda baka daukeni abokiyar shawararka ba,kuma baka kallona a abokiyar tayaka farin ciki ko sabanin haka….”
Tashi yayi ya rikota dakyar ya kwantar da ita tana ta zizzillewa,binta yayi ya saka mata nauyinsa ta yadda bazata iya tashiba,
“Nifa bazan kwana adakin nanba….”
Dariya yayi sannan ya shafi kumatunta,
“Kwana kuma na nawa sa’adah? Jiya kam ai kin kwana saura yau kuma…”
“To ba ka ki ka fada min damuwarka ba”
“Sa’adah banda lafiya……… Insha Allah zan koma chairo next month zasuyi min surgery…..”
Tashi zaune tayi yunkurin yi ya hanata babu bata lokaci tafara hawaye tana ta tambayar rashin lafiyar dake damunsa amma yaki fada kawai dai yace mata wai wani abune shima bai san menene ba zasu yimasa aiki,dakyar ya lallaba ta suka koma bacci,tun daga ranar hankalinta yaki kwanciya duk tabi ta damu dan gani takeyi kamar mutuwa zaiyi yabarta,shima kuma komai nashi cikin sanyin jiki yake gudanar dashi dan daga karshe ma cewa yayi zaiyi resigning yabar aiki hajiya ta hanashi,haka dai yaci gaba da fita aiki kusan kullum yana fama da zazzabi mai zafi,
Lokacin da zai koma chairo din tare da Hanan suka tafi kuma aranar da suka je aranar aka yimasa aikin,yasha wahala ba kadan ba amma kuma anyi cikin nasara nan tayita zaman jinyarsa har yafara samun lafiya,kullum cikin amsa wayar yan uwa daga gida Nigeria take,satinsu uku acan ya warke garau kuma yaji sauki sai lokacin yake sanar da ita wai cancer ce ta kamashi amma bata girmama ba ita aka cire masa,
Gida suka koma yaci gaba da al’amuransa gefe daya kuma yana kulawa da iyalinsa, itama dagewa tayi tana kulawa dashi domin bata son wata ta kwace mata shi bugu da kari kuma mijin matacciya take aure idan batayi da gaske ba zaiyita kewar matarsa da tunaninta, abinda bata saniba shi yanzu baida lokacin kara aure ko kula mace awaje saboda atsarinshi mace guda daya ta isheshi rayuwa.
Ganin wanda takeyi dominsa baya ta kowacce mace sai iya ita kadai yasata sakin jikinta nan tafara kasuwancinta tabude restaurant da boutique mai hadeda wurin saloon da gyaran jiki da kwalliya duk na manyan mata,idan Khalil ya tsareta da tambayar wai me zatayi da kudi sai tayi dariya tace abunda akeyi dasu nan kuwa iyayenta take taimakawa wanda bata da kamarsu kuma duk da Khalil na iya bakin kokarinsa amma itama gara tayi nata haka kuma sauran yan uwa da abokan arziki ai basai tazo tana cemasa bani bani ba lokuta da dama da nata take yin amfani.