MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Ai rasa abinda zatace tayi,ta ma rasa wanne irin farin ciki zatayi gaba daya, kwalla ce ta ji ta ciko mata idanuwanta saboda tsabar farin ciki,dama tajima tana mafarkin jin wadannan kalaman daga bakinsa amma bata tsammaci jinsu kwana kusa ba,bata zaci zata jisu a daidai wannan lokacin ba,rufe bakinta tayi da dukkanin hannayenta guda biyu.

***

  Ta jima akwance tana kuka tun bayan fitowarta daga part din Khalil ta kwanta tana kuka,haba wannan cin fuska da tozarci har ina? Dan kawai anty maamy tana matsayin kanwarsa sai yarinka fifitata akanta? Duk yanda akayi ba a iya yan uwantaka al’amarin nasu ya tsaya ba sai dai idan akwai wata akasa,ita tana nan tanata wahalar dawainiya da soyayyar shi bai tsaya ya kulata ba a matsayinta na matar aurenshi amma yaje yana kula da wata mace dan kawai yana takamar jininshi ce,

Sam Hanan bata iya samun abu ba shiyasa wuni tayi tana kuka kuma har lokacin bata jin zuciyarta ta huce daga bacin ran dake makale dankare acikinta, Aryan tunda yadawo daga makaranta yake son ta tashi suje garden su hau lilo kuma ta koya masa karatun hisnul ad’fal amma taki tana nan dai kwance kamar ruwa kan gadonta duk idanuwanta akode,

Duk da bawai azumi take yiba amma wuni tayi bata ci komai ba bata saniba yaturo andauki anty maamy din ko bai turoba oho musu,bayan tayi sallar magriba wanka tayi ta saka riga da wando na English wears jeans da t shirt ta dan yafa mayafi ta fita ai karuwancin kowama ya iya kunya ce da kara ke sawa ake nuna kamar ba a iya ba,azo har gidanta anemi takura mata? Wallahi bazai yuyu ba ai tunda anty maamy tasata kuka wallahi itama sai ta sakata kukan kuma shima Khalil din zai gane shayi ruwane dan sai yagane kurensa,umma kadai ta samu a falon kasa sai Aryan dake kan kekenshi yana ta faman zagaye harabar falon,zama tayi suka gaisa da umma anan umman ke tambayar ta wai ko lafiya kuwa kodai jikinne? Murmushi kawai tayi aranta tana tunanin wai har sai yaushe su umma zasu farga su gane cewa babu juna biyu a tattare da ita? Tashi tayi zuwa dining area ta hado golden moon cup biyu ita da Aryan domin shima gwaninshi ne yana son golden moon haka zata yita hada musu suna sha kamar wasu yan boarding,suna nan falon suna taya Aryan kallon cartoon anty maamy ta shigo tabe baki Hanan tayi ta kawar da kanta gefe acikin zuciyarta tana cewa ashe ma bata nan ko ina taje kuma oho? Itama Anty maamyn umma kadai ta kula sai Aryan tawuce bedroom daga nan bata sake fitowa ba,har 10 suna falon kasa da umma suna hira ganin karfe 10 ya dan gota kuma batayi sallar ishah ba yasata hawa sama dan tayi,tana tashi Khalil na shigowa,ai tun ahanya Aryan yasoma tsegunta masa wai mommy tanata kuka tun da yadawo daga school yau ko karatu bata koya masa ba blah blah,

Bayan sun shiga falonshi text massage ya tura mata wai tazo, shareshi tayi ta sake gyara zamanta saman kujerar da take zaune tana kallon tashar zee world,har yayi wanka yafito bata zo ba ga Aryan nan yayi bacci kasa kan rug acikin falonsa,da kanshi yafita ya nufi sashenta, knocking yafara yi sannan yabude yashiga duk zatonta Aryan ne shiyasa bata ma ko dago ba daga kwancen da take da pillow akirjinta ta rungume,

Kamshin turaren sa tafara ji sai kuma tajiyo muryar shi,

“Baki ga kiran da nayi miki bane nace kizo?”

Bata rai tayi sannan ta tashi zaune tana sake babbata fuska,

“Zo….”

Daga haka yajuya yafita ta tashi tabi bayansa tana gwada tafiyarsa harda wani dan sakin doro take yi,shi dai baima san tanayi ba,suna shiga part dinsa bedroom yawuce zai dauko system dinshi ita kuma ko zama batayi ba ta hango anty maamy rikeda karamin flask tana tahowa tashi tayi taje ta sakawa kofar lock,ta dawo ta zauna, knocking anty maamy tafara yi amma Hanan taki budewa zuwa can dai ta tashi taje ta bude amma tayi bake bake akofar ta yadda mammy bazata iya wucewa ba,

“Lafiya?” Hanan ta fada tana kallon gefe,

“Matsa inwuce…”

“Ki wuce ina? Haba anty dare ne fa,ai wannan lokacin na ma’aurata ne,muna cikin tsaka da raya sunna kinzo kin katse mana jin dadi…….”

Daga haka ta mayar da kofar ta rufe ta sake danna lock ta wuce ciki tabar anty maamy tsaye baki abude…………………….鉁嶐煆?

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:14 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

43***Tana iya hango anty maamy daga zaunen da take wacce takaici ya hanata ko motsi daga inda take tsaye kawai mamakin maganganun da yarinyar nan ta fada mata take yi,ta dan jima atsaye sannan taja kafafunta wadanda suka yimata nauyi ta kara gaba zuciyarta cike famm da takaicin furucin da hanan tayi mata,

Hanan sake gyara zamanta tayi tana hango lokacin da maamy ta juya ta koma inda tafito dama allah allah takeyi ta tafi kafin Khalil yafito yaganta yaje da kansa yabude mata kofar,ai kuwa tana tafiya sai gashi yafito yana yin waya da alama ma wayarce ta tsayar dashi cikin dakin dan har yanzu bai gama ba,zama yayi a kujerar da yafi zama wacce ke kallon kofa,jin ya ambaci barrister muhsin yasata fahimtar cewa da lawyer dinsa yake yin waya,

Aryan ta dauka ta fita zata kaishi dakinshi ta kwantar dashi kafin Khalil yagama wayar da yake yi,saida ta zauna tayi zaman canjawa Aryan kaya sannan ta fita,part din Khalil ta sake komawa sai kunkumbura baki take yi ita kadai,

Ayanda ta tafi ta barshi haka ta dawo ta sameshi sai dai yanzu ba waya yake yiba laptop dinshi yake dubawa,a kasa ta zauna tana wani turo baki,

“D’anki yace yau ma kinyi kuka,meya faru?” Yafada idanuwanshi na kan system dinshi kyarr,

Jin abinda yace yasata sake turo baki amma batayi magana ba,ai yafi dan dako sanin tasha,yafi kowa sanin abinda yasata kuka tunda shine sila,

“Uhmmmm….?” Ya sake fada batare da ya kalleta ba,

“Da safe ne na tambayi zuwa saloon aka hanani…..”

Murmushi yayi jin abinda tace, lallai yarinyar nan yar yice,

“Shine kika zauna kina kuka?”

“Uhmm”

Shiru yayi yaci gaba da abinda yake yi tsawon mintuna biyu taji yace,

“Jeki ki hado min coffee ki kawo min”

Tashi tayi tafita aranta tana mitar dama dan dai yasata aikine kawai yaje ya tasota, kitchen dinta ta shiga,tana cikin hadawa taga diff an dauke wuta akaro nafarko tun bayan zuwanta gidan bata taba ganin an dauke wutaba sai yau, wayarta ta kunna da ita tayi amfani ta karasa ta dauka ta fita wato da ita maamy kawo mishi tayi kenan to sai dai taje tasha kayanta yau bazai sha ba. 

Daga shi sai gajeren wando ta sameshi lokacin da ta koma amma jin motsinta yasa shi lulluba t shirt dinsa a kirjinsa,sai tsaki yake yana kiran wani awaya wanda bata san ko waye ba,shi kwata kwata baya shiri da zafi duk da ba wani jikin azo agani gareshi ba amma jin zafine dashi to sai Allah yarufa masa asiri ya iyoshi agidan hutu kullum yana cikin AC,

“Wai meke faruwa da Gen dinne?…….. Ok tom”

Daga haka taga ya katse wayar yamike daga kan kujera yashiga bedroom dinsa,ruwa yaje ya watsa ya fito yana fitowa wuta tazo dama wai Gen din aka yiwa juye, jallabiya yasa yafita har lokacin tana zaune tana jiransa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button