MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Rana tsaka kuma Khalil ya daukesu ya mayar dasu k’asar Paris saboda karatun yaransa itama ba abarta abaya ba ta fada tata makarantar inda taci gaba da karatu kuma su basu cika zuwa bama sai shine ke zuwa,amma wannan karon saida yayi 3 months bai jeba,kuka Hanan tasaka masa awaya washe garin ranar sai gashi yazo lokacin dama har ta yaye Ayaan,
A bedroom dinta ya sauka tunda dama 2 bedrooms ne daya nata daya nasu Aryan,
“Wai sai yaushe za abawa su Aryan kani ne…”
“Hum um babu rana,garinsa da nisa….”
“Garinsa akusa yake ai kuwa saboda saida nataro gajiya ta gaba daya sannan nataho”
Turo baki tayi tana harararshi,
“Muda ka manta ma damu kaje kayi zamanka….”
“No,ni na isa mantawa da zuciyata……… Zo kiji wani abu”
Janyota yayi ya rungume ta yana fada mata irin girman matsayinta cikin zuciyarshi daga karshe kuma yashiga nuna mata a bayyane da bakinsa da hannayensa da dukkan gangar jikinsa gaba daya yana kara jaddada mata shi nata ne ita daya haka kuma ta daina kiransa da mijin matacciya shi mijin rayayyiya ne domin tuni ya maye gurbin Ramlat da Hanan tsakaninsa da Ramlat addu’a ce amma Hanan itace abokiyar rayuwarsa har gaban abada zai cigaba da kulawa da ita da nuna mata kauna da soyayya har tsufansu, wannan karon akasar Paris tasamu ciki kuma acan ta haihu cikin kulawar doctors da Khalil wanda ya tayata nakuda ta haifo yaronta santalele wanda gaba daya su Aryan suka tare masa kyau domin tamkar balarabe haka yake nan Khalil yayi masa huduba da Abubakar saddiq yana tsokanar Hanan wai wannan karon babu kukan dinki to sai muce Allah yaraya yakaro kazantar daki.
ALHAMDULILLAH
Godiya ta tabbata ga ubangiji Allah madaukakin sarki wanda yabani ikon kammala wannan littafi mai suna mijin matacciya, Allah ya yafe mana kuskuren dake ciki ya hadamu acikin ladan gaba daya tare daku masu karatu,kamar yadda nafada book dina na kudine duk wadda ta karanta batare da ta biya ba to yar uwa kisani Allah yana kallonki,bawai book dina kadai ba duk book din da akace na kudine yakamata mu kiyaye daukar hakkin wani domin Allah yana gafarta abinda ke tsakaninka dakai bawa amma baya yafe hakkin wani murinka tunawa da wannan,ina mutukar godiya ga masoyana wadanda ke nuna min kauna kuma suke tare dani koda yaushe Allah yabarmu tare,sai mun hadu acikin labari nagaba,taku ahar kullum kuma akoda yaushe Ummi A’isha nagode.
_*Ummi Shatu*_馃憣馃徎
Share this
[ad_2]