MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

“Gobe za akaiki saloon din….”
Kamar tace ta fasa sai ta amsa masa,cewa yayi ta tashi taje ta kwanta,tashi tayi ta fita sai faman cika take tana batsewa kamar zata fashe, bai san har lokacin akule take dashi ba shiyasa ma ai yau ko girkin bata yimasa ba ita maamy din da ta fita awurinsa ba sai tayi masa ba.
Juyi ta fara yi lokacin da ta kwanta domin yin bacci sai dai sam baccin yaki zuwa maimakon ma taji alamunsa sai tunanine taji yana bijiro mata adaidai wannan lokaci,bata taba ganin namijin dake burgeta yana jan hankalin ta ba kamar Khalil tsawon rayuwarta, musamman ma yau da ta ganshi cikin yanayin da bata taba ganinsa ba koda yake bama shiba bata taba ganin babban namiji baligi ahaka ba dan ko yaya shamsu zata iya bugar kirji tace bata ganinsa yana zama haka,
Wani irin bege da shaukine ke fusgarta agame dashi,jin zuciyarta takeyi tana wani irin harbawa da karfi, runtse idanuwanta tayi tana fatan bacci ya dauketa ko wai zata samu ta huta da wannan tunane tunanen amma hakan bai samuba har wurin k’arfe 1:30 dakyar da addu’a tasamu tayi bacci a wannan dare,
Washe gari bayan ta shirya Aryan yatafi makaranta itama shiryawa tayi cikin wata jar atamfa mai zanen camera ajiki,sashen Khalil ta wuce dauke da kayan breakfast a hannunta,tana shiga ta wuce kan dining ta soma shirya masa tana gamawa ta koma ta rufe kofa b’am ta dawo ta zauna tasan yanzu haka anty maamy tana kan hanyar zuwa sai kace wata matarsa kullum tana manne dashi,wani dogon tsaki taja saboda kishin da ke ciciyar zuciyarta wanda ita bata ma gane ba kawai dai tasan tana masifar jin haushin anty maamy sannan tana jin haushin yanda take shisshigewa Khalil duk da yar uwarsa ce,
“Keda wa?”
Juyawa tayi sakamakon jin muryarshi da tayi abayanta yana tsaye ya dafa kujerar da take kai shirye yake tsaf cikin shirin fita office yau kam yafi koda yaushe yimata kyau saboda abaturensa yafito sak domin suit yasaka bakake amma farar t shirt mai dogon hannu wacce keda kwala yasa aciki,
“Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakkyawar halitta…. Masha Allah” Ta furta can kasan makoshinta,kasa dauke idanuwanta tayi daga kansa ahaka suka gaisa ya nufi dining tabishi,dan wake da yaji da man gyada da vegetables ta zuba masa harda dafaffen kwai sai kunun farar shinkafa mai dauke da gyada da madara,kai masha Allah shima hakan yaketa nanatawa cikin ranshi saboda tsabar dadin da abincin yayi masa,yana masifar son irin girke girken nan amma baya samu sai idan yaje gombe,
Kiran Khalid ne yashigo cikin wayarshi saboda tun daren jiya yatura Khalid din text massage yana yimasa maganar daidaita kansu da sukayi da maamy yanzu wani abu kadai yake jira sai yasanar da gida,yasan Khalid zaiyi farin ciki saboda dama maamy kanwarsa ce shikuma amininsa ne,
“Kai baban yan uku ya akayi?” Khalil yafada cikin raha,
“Lafiya lau babban mutum,ya aiki? Ya Aryan?”
“Yatafi school…… Kaga sakona ko?”
“Ehh naga abin farin ciki,wai ya akayi hakan ta kasance? Kodai kun tuna tsohuwar soyayya ne?”
Kamar tv haka Hanan ta sakashi gaba tana kallonsa, Kai wannan mutum da kyau yake,ga nutsuwa ga kuma aji,shagala tayi da kallonsa shiyasa ma bata samu damar ganin tahowar anty maamy ba kawai sai knocking dinta taji,da hannu Khalil yayi mata alama wai taje ta bude,mikewa tayi cike da bacin rai ta nufi kofar tana harare harare ita daya,tana zuwa ta tsaya bakin kofar kamar yadda tayi jiya,anty maamy tasha kwalliya cikin doguwar riga ta shadda hadaddiya peach,
“Anty maamy gaskiya bazan boye miki ba kina shiga hakkinmu….. Wai meye tsakaninki da mijina da har zaki rinka shigowa part dinsa kullum? Nidai agaskiya kina takura min sannan kuma nagaji….”
Murmushin takaici anty maamy tayi,
“Bani wuri inwuce ni ba gunki nazo ba gurin mijinki nazo”
“Toh ai duk daya….. Koba wurina kika zoba tunda kika zo wurin mijina ai baki nemi zaman lafiya ba,nifa kina shigar min hakkina kuma bazan lamunta ba….. Nayi kara nayi kara har nagaji”
“To yanzu zaki bani hanya inwuce ne ko yaya?”
“Gaskiya sai dai ki koma inda kika fito dan wallahi bazaki shiga ba,haba ya wai nida gidana nida mijina amma ahanani sakewa?”
Turata anty maamy tayi zata wuce nan kuwa ta dage karfinta ta dawo da ita baya tana kokarin mayar da ita waje abu sai yakoma fada fada kokawa kokawa,wayar da yake yi ya katse yamike domin kamar hayaniyar su yake jiyowa,mamakine karara ya bayyana akan fuskarshi lokacin da ya iskesu suna kai ruwa rana ita Hanan ta daddage tayi bake bake abakin kofa tana hana maamy shiga ita kuma maamyn itama ta dage tana kokarin ita alallai dolen dole sai ta shiga,
“Maamy….. Menene haka?” Yafada idanuwanshi akansu su duka biyun,
“Wai daga nazo inaso zan shiga wurinka shikenan yarinyar nan ta daddage ta hana wai bazan shiga ba….”
“Meya faru?” Ya maida kallonsa kan Hanan gaba daya wacce ta bata fuska ta hade rai tana ta faman gurmude gurmuden baki sai karkada jiki takeyi alamar masifa da bala’i karara,jin tambayar da yayi mata yasata kallonshi sannan ta kawar da kanta gefe tana hararar anty maamy,
“Abinda ta fada maka shi akayi,ba ita kafara tambaya ba….?”
Bashiba ita kanta maamy saida kalaman Hanan suka bata mutukar mamaki kuma suka daure mata kai mutuka gaya,yanzu yarinyar nan ce ke fadawa Khalil haka agabansa bawai abayan idonsa ba? Shi kuwa dama yasan hali yasaba da rashin kunyarta sai dai ma yabawa wani labari shiyasa abin bai wani dameshi ba sannan shi mutum ne mai hakurin gaske sau tari sai dai mutum ya cuceshi amma shi yakan jima kafin ya nunawa mutum rashin hakurinsa,
“Ehh ai ta fada min kuma naji nata yanzu naki nake son ji shiyasa na tambayeki…..”
“Takura min take yi duk lokacin da ta shigo min b’angaren mijina,jiya cikin dare tazo nace bazata shiga ba yauma ta sake dawowa to menene ma’anar hakan? Wannan safa da marwa din ya isa haka….”
“To yanzu me kikeso ayi? Yar uwata ce fa”
“Duk da yar uwarka ce ai bai kamata ta rinka shigo mana ba anyhow,ya za ayi ace ni banda sirri? Shikenan kuma har turakar mijina sai wata mace tagani? Ni karta kara shigowa sashenka idan gaisawa ne tajira duk lokacin da ka sauka k’asa sai ku gaisa….”
Shi gaba daya ma mamaki Hanan take bashi saboda yanda ta fututtuke ta hakikice tana tada jijiyar wuya wai harda cewa maamy karta kara shigar mata turakar miji,
“Yanzu ke idan akayi hakan kin kyauta kenan? Fada da bakuwa? Kwana nawane zata taf….”
“A’a wannan yanzu ba bakuwa bace ai tajima da zama yar gida….yau kwananta nawa agidan?”
“To yanzu dai kar na kara ganin kinyi mata irin wannan babu ruwanki da ita,ba wurinki take zuwa ba wurina take zuwa….”
“To wallahi ni bazan zauna da ita ba agidan nan,zanje intafi gidanmu inyaso ita taci gaba da zama tare daku…….”
Fuuuuhhh tayi waje tabarsu awurin tawuce sashenta hawaye na karakainar zubowa daga cikin idanuwanta,tana zuwa ta janyo babban akwati daga cikin na lefenta tasoma kwaso kayanta na sawa tana zubawa aciki wanda kawai cakuda su take tana hautsinawa aciki babu wani jerawa ko shiryawa,
Jiki asanyaye maamy tajuya tabar Khalil tsaye ta sauka kasa zuciyarta duk babu dadi, Kai tashin hankali baiyi ba arayuwa me za ayi da bacin rai,
Shi kuwa Khalil ciki yakoma ya dauko wayoyinsa yasaka bakin takalmi sau ciki yafito yasauka kasa,a babban falon kasa yasamu Hanan da umma barira wacce keta faman riketa tana bata hakuri akan ta janye maganar tafiya gidan da ta dage sai tayi amma taki sai jan uban akwati take yi,