MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

“Wai meya faru ne? Mu’azzam meke faruwa?” Umma barira ta tambaya tana kai dubanta gareshi,
“Umma ni bazan zauna tare da anty maamy ba,sai dai azabi daya ya zauna tsakanin nida ita acikin gidan nan…. Wallahi tafiya zanyi”
Lamarin Hanan gaba daya mamaki yake bashi wai yarinya duk tabi ta burkice tace ita lallai lallai sai maamy tabar gidan,to wai menene azuciyar yarinyar nan? Kafin yayi magana fuuhhh yaga taja akwati ta nufi kofa ita kuma umma ta tsaya cak tana kallonsu tama rasa me zata tsara balle tasamu ta cewa,bin bayanta yayi tana ta kokarin yafa jan mayafin dake hannunta cak numfashinta yanemi daukewa sakamakon rikon da taji yayi mata wanda har saida yayi sanadiyyar haduwar jikinsu wuri daya………………………….鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*44*
***Fuskarta ya tallafe da dukkan hannayensa guda biyu masu tsananin taushi hakan yasa ta lumshe idanuwanta wanda yayi sanadiyyar zubowar wasu tagwayen hawaye ajere,
“Meyasa bakya jin magana ne? Kina musu dani ko? Ga gardamar tsiya kamar sabon angon jaki…… Kina son infadawa abbanki?”
Girgiza kai tayi tana cigaba da b’arin hawaye afuskarta,
“To yanzu da kika debi wadannan uba uban kayan cikin akwati ina zakije? Kin gaji da zama da mune?”
Kai ta sake girgiza masa har lokacin idanuwanta a rufe suke sai hawaye dake ta faman malala,
“Kar ki tafi ki daure ki zauna ko dan d’anki Aryan…. Yanzu idan yazo ya iske bakya nan wanne irin hali kike tsammanin zai shiga? Kar ki tafi kibar d’anki idan kuma kin dage sai kin tafi to kibari yadawo sai ki hada masa nasa kayan kutafi duk inda zakije tunda ni kin gaji da zama tare dani….”
Sai lokacin ta bude idonta ta kalleshi shima ita yake kallo ko kiftawa bayayi ita dai tasan kawai yafada ne amma ya za ayi yabata Aryan yace wai sutafi duk inda zataje ai ko giyar wake yakesha bata jin zata yi masa tasiri anan,
Kai ya jijjiga mata alamar tabbacin abinda yafada,daga haka ya saketa daga rikon da yayi mata yawuce yafita yana kokarin gyara necktie dinshi,
Tafi minti biyar tsaye wurin ta kasa koda kwakkwaran motsi har umma barira ta karaso tazo tana mai sake bata hakuri akan karta tafi tunda bada mijinta sukayi fada ba to babu amfanin tabar gidan wai da sunan yaji,
Juyawa tayi ta ja akwatinta ta nufi ciki dakyar ma take jan akwatin saboda kayan da ta loda ba kadan bane sai kace wacce idan ta tafi zatayi shekara agidan,har bedroom dinta umma ta rakata tana sake bata baki tana cemata kowa kagani agidansa hakuri yake yi amma akwai matsalar da take tare dashi,
Bayan fitar umma Data ta kunna awayarta ta hau online saboda tana son ta dan debewa kanta kewa amma acan kasan ranta ta kuduri aniyar itafa bazata cigaba da zama da anty maamy ba sai dai ayi wacce za ayi.
Har Khalil yaje office bai daina mamakin abinda Hanan tayi ba,to wai me zai kira wannan lamarin nata dashi? Kishi ko kuruciya? Gaba daya yarinya ta dage sai ta kori maamy daga gidan,yana shiga office kiran maamy yashigo masa, dauka yayi muryarshi asanyaye kamar kullum,
“Ibrahim ni nagama shirya kayana zan wuce gombe……”
Dan jimm yayi sannan yace,
“Ban gane zaki wuce gombe ba…”
“Ehh zan koma gidan ubana mana,inbanda matarka ta samu dama wai har ni zata yiwa gorin gida? Taje ta tambaya waye ubana,kai kanka kasan ubana yanada gidajen da bazasu lissafu ba,ni kaina inada gidaje sunfi goma mallakina amma wai ni ake yiwa gori akan gida nida gidan mijina akasar turai yake amma wai yau saboda nazo gidanka karamar yarinyar da bata fi sa’ar autar gidanmu ba take kokarin wulakanta ni….. Nagode”
Kitt ta katse wayar,rabuwa yayi da ita bai kara kiranta ba saboda yasan yanzu ranta abace yake ko daga kalaman da take yi yasan akule take maamy kuma badai zuciya ba,rabuwa yayi da ita har zuwa yamma lokacin da zai tashi daga office inyaso sai yabita can gomben ya wanke kansa.
Misalin karfe 6 yatashi daga office kuma direct hanyar gombe suka kama wanda basu suka isa ba sai bayan sallar magriba,salla yafara yi sannan ya karasa gidan Alhaji Idris kanwa mahaifin maamy,bai samu abban agida ba kasancewar baya gari, Jawad yatura yace yayi masa sallama da momyn su nan Jawad din ya ruga da gudu ya nufi can cikin gida,
Maamy tana gaban mirror tana tsala kwalliya tamkar wata budurwa dan ko da wasa bata daukar kanta a matsayin wata babba ta azo agani duk da tana da samarin yaya da budurwar ‘ya,
“Mommy kizo inji uncle Khalil….”
“Yana ina?”
“Yana falon abba na kasa”
“Ina zuwa to”
Fita jawad yayi ita kuma ta tashi ta karasa shiryawa cikin doguwar riga ja tasha turare sannan ta dauki dan siririn mayafinta ta fita tana takunta mai cike da nutsuwa da daukar hankali,
Zaune ta sameshi ya dora kafarshi daya akan daya yana duba wayarshi,zama tayi gefenshi bayan tayi masa sallama,
“Haba amarya irin wannan fushi haka kuma? Sai kace dani akayi fadan…..”
Wani kallo tayi masa kafin ta rausayar da kanta gefe,
“Ai wannan matar taka sai Kai….. Kasan wani abu? Wallahi bazan zauna gida daya da ita ba, tun wuri ma ni ka sama min gida amma banda wannan….. Ban son rashin kunya”
Murmushi Khalil yayi ya shafi sajensa,
“Kinji tsoro kenan?”
“Ba maganar tsoro anan fa Ibrahim gaskiya ce”
“To Allah dai yabaki hakuri,dan Allah ki dauki abinda yafaru yau amatsayin ba komai ba saboda kinga ita yarinya ce,yanzu ne ma take sanin yaya rayuwar take……”
“Nifa banda case da ita,kawai nidai bukatata awurinka shine karka hadamu gida daya dan bazamu zauna lafiya ba….”
“Baki da matsala a wannan bangaren Maryam,insha Allah zanyi yanda kike so……., Yanzu ina son zan karasa wurin hajiya mu gaisa sai inkoma Abuja,dan nan nafara zuwa”
“Ayya babu matsala,ka gaida min da ita”
“Zata ji insha Allah, shikenan intafi an sallameni?”
Murmushi tayi ta dan fara idanuwanta alamun shagwaba,
“Da ance maka kai mai laifine?”
“Ehh mana ranki yadade….. Za dai muyi waya insha Allah”
“To babu matsala yallabai,muje in taka maka”
Har inda motocinsa ke ajiye ta rakashi aka bude masa yashiga sannan tajuya tawuce cikin gida,shikuma suka nufi gidan hajiya can dinma bai wani zauna ba dan ana kiran sallar ishah yafito bayan sun gabatar da salla suka juya abuja zai koma ya tarar da yar rigama Hanan,karo na farko da yayi tunanin abinda ya shafeta har yayi dariya shi daya,gaskiya yarinyar nan case ce,wai,wayarshi ya ciro ya soma kiran layin Aryan.
Ita kuwa Hanan bayan tafasa tafiya ta mayar da kayanta ciki sai da ta zauna ta sha kukanta sannan tayi shiru wannan dinma zuwan umma ne wacce ta tisata agaba tana ta faman bata hakuri tana cemata shi dama zaman aure gaba dayansa hakurine yafi yawa acikinsa kai bama iya zaman aure ba ita kanta rayuwar gaba dayanta hakuri ce dan haka ta dauki wannan abun da yafaru amatsayin ba komai ba kuma taci gaba da yiwa mijinta biyayya,
Tsamm tayi ta tsaida hankalinta da tunaninta wuri guda tana mai cigaba da jujjuya maganganun umma acikin ranta duk da cewa umman adunkule ta bata maganar bawai zama tayi tai mata ita dalla dalla ba amma akwai alamar tana bukatar tayi wa dukka maganganun duba na tsanaki domin umma cemata tayi taci gaba da kyautatawa mijinta saboda zuciya ahar kullum tana son mai kyautata mata sannan ta guji fushi da bacin ransa,to tayaya zata guji wadannan abubuwan? Dole tana bukatar daura damarar kulla abota da hakuri da gujewa duk wani abu da ka iya bata ransa sannan umma tace duk runtsi duk tsanani karta karaya daga fafutukar yakin neman cikar burinta taci gaba da fadawa Allah dukkan bukatunta haka kuma ta jajurce ta tsaya tsayin daka har sai hakarta ta cimma ruwa,