MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Murmushi tayi aranta tana tambayar kanta to kodai umma ta fahimce cewa tana son Khalil? Ko umma ta gano sirrin da taketa boyeshi acikin zuciyarta ita kadai wanda bata fatan wani mahaluki ya fahimta baya gashi wanda take yi dominsa? Cigaba tayi da aikinta acikin tamfatsetsen kitchen dinta mai dauke da komai da komai na bukata wurin girke girke,dama tasan bazai dawo da wuriba shiyasa itama bata tarki aikin da wuriba har sai da tabari la’asar tayi liss sannan tafara,tuwon semovita ta dora saboda Aryan yanata damunta da tambayar wai “mommy tuwo zaki dafa mana?” Wannan dalilinne yasata dora tuwon semovita miyar shuwaka, farfesun zabbi da kuma kunun shinkafa. A kitchen magriba tayi mata,agurguje ta karasa aikace aikacenta sannan ta kwashi na umma ta kai mata can ta isketa tana ta drama da mutumin nata Aryan ita dai da yake bata yi salla ba komawa sama tayi taje tayi wanka sannan tayi salla bayan ta idar ta koma k’asa dauke da tuwon da zata bawa Aryan,

Anan umma ke sanar da ita tafiyar anty maamy wadda sam ita Hanan bama tasan cewa ta tafi ba sai yanzu da umma ke bata labari,

“Allah yaraka taki gona……” Shine abinda Hanan ta fada acikin zuciyarta,afili kuwa sai kawai tayi murmushi tana sauraren umma,

Yau sun jima sosai da umma wacce keta yiwa Aryan tatsoniya har saida yayi bacci,daukarshi Hanan tayi a kafadarta ta nufi dakinsa dashi ta kaishi ta kwantar,daga can kuma part dinta ta wuce tana kallon agogon dake kan wayarta karfe 11 na dare harda wasu mintuna,shirin bacci tafara yi itama bayan tagama ta saka dogon hijab ta fita,kanta tsaye sashen oga ta nufa wanda dawowarsa kenan dan ko minti biyar baiyi ba da shigowa cikin gidan,wani abun mamaki kuma wai sai yanzu ne taji tana jin kunyar abunda yafaru da safe sai yanzu take jin kunyar rufe idanuwanta da tayi ta zazzaga masa rashin ta ido,

Tana shiga falon yana fitowa jikinsa sanye da rigar wanka fara, hannunshi rike da charger da alama wayar shi zai saka ajikin chaji, sunkuyar da kanta kasa tayi tana yimasa sannu da zuwa daga bisani ta mike tafita domin kawo masa abinci kamar kuwa tasan dama yunwa yake ji saboda rabonsa da abinci tun wanda yaci da safe. Yana zaune yayi nisa kadan aduniyar tunanin da ya tafi tabbas yana son maamy bawai so irin can mai zurfin nanba amma kuma wani lokacin sai yaji kamar yafasa auren nan domin shi yanzu gaba daya mace bata gabansa bawai dan baya bukatarta ba a’a saboda kawai ruhinsa da tunaninsa gaba daya kacokan suna ga Ramlat,iya gangar jikinsa ce kadai anan ita kanta wannan yarinyar Hanan kawai yana zaune da itane saboda Aryan,amma har gobe Ramlat ce abirnin zuciyarsa, shigowar Hanan bayan tayi masa magana shine yayi sanadiyyar dawowarshi daga tunanin da ya zurfafa acikinsa,

Cikin sanyin jiki da na murya yace ta zubo masa tuwon guda daya,zubo masa tayi sannan ta zuba masa kunu cikin cup da farfesun da tayi agefe takai masa gabansa,samun wuri tayi ta zauna duk da ta dan fara jin bacci sama sama domin 12 ta kusa,lura da gyangyadin da yaga tana yi yasashi fadin,

“Je ki kwanta sai da safe,nagode……”

Tashi tayi tana lullumshe ido ta fita,tana zuwa daki ta fada kan gado tana zare hijabin dake jikinta babu jimawa bacci ya dauketa,

Shi kuwa Khalil yana can yana sakawa da kwancewa yarasa meyasa aduk lokacin da maganar aure ta fara shiga tsakaninsa da wata mace sai yasamu kansa cikin mugun hali sai yaji gaba daya kunci da damuwa sun rufeshi koda yake yasan hakan bai rasa nasaba da tsananin kaunar da yake yiwa Ramlat,lumshe idanuwansa yayi yana mai barwa Allah zabi,idan har aurensa da yar uwarsa maamy alkhairi ne to Allah ya tabbatar idan kuma babu alkhairi Allah ya canja musu da mafi alkhairi.

3:30 AM

  Daidai wannan lokaci Hanan ta farka daga nannauyan baccin da take yi,yanda taga yanayin d’akin nata sai ta dan tsorata domin kamar anshigo mata dan ga kofar dakin nan abude alhalin kuma ita ta rufe sai dai bata saka mukulli ba,wuta ta kunna ta sad’ad’a taje ta rufe da key sannan ta wuce bathroom tayi abinda zatayi ta gama tazo ta sake kwanciya tana dauko wayarta daga karkashin pillow dan ganin time, text massage taga anturo mata da kamar ba zata budeba sai kuma ta bude nan taga abunda yayi nutukar razanata kuma yasata cikin tunani sakamakon ba sanin wanda yaturo sakon tayi ba……………………………..鉁嶐煆?

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:14 AM – Ummi Tandama: 45

***Gabanta ne yasoma faduwa saboda sako aka turo mata mai cike da kalaman soyayya tsantsa wanda kuma ba sanin number din tayi ba,kasa komawa bacci tayi tanata faman sak’awa da warwarewa,to ko waye wannan kuma? Innalillahi,shine abinda take ta faman nanatawa acikin zuciyarta,shiru tayi tana tunanin abinda yadace tayi daga karshe dai ta tattara sakon da mai turo sakon ta watsar da tunaninsu tayi kwanciyarta tana fatan sake komawa wani baccin,

Daidai wannan lokacin shikuma Khalil ya idar da sallolinsa na dare kamar yanda yasaba yahaye saman gado ya kwanta yana son ya huta, tunani kwaya daya shine keta faman kaiwa da kawowa cikin kwakwalwarshi wato tunanin auren maamy,yanzu shikenan ta tabbata yaci amanar Ramlat? Yanzu shikenan ya saba alkawarin da yajima yana yiwa Ramlat akan bazai taba auren wata ‘ya mace ba bayan ita? Shi yanzu abinda yafi damunsa kenan dama ita Hanan ba a ta ita domin yanada hujja da dalilin aurenta,har yayi bacci tunanin dake cikin ransa kenan.

Washe gari karar shigowar text massage ne ya tada Hanan daga bacci,bata budeba tawuce toilet kai tsaye domin ta so ta makara,cikin sauri sauri ta ke gabatar da komai har ta kammala sannan ta shirya Aryan,sai da yahau sama yaje wurin abbanshi sannan yazo yawuce makaranta,ita kuma daki ta koma tayi wanka tafito sai lokacin ta bude sakon da aka turo mata tun dazu, number din jiyace kuma yanzun ma sakone na barka da safiya mai dauke da kalaman soyayya,lumshe idanuwanta tayi aranta tana fatan inama inama…. Inama ace wanda zuciyarta take bege take mutukar kauna shine ke turo mata wadannan kalaman ai da tayi tsalle akan kaya saboda tsabar farin ciki.

***

 Rayuwa haka taci gaba da tafiyarwa Hanan cikin gidan Khalil duk da babu wani sauyi a zamansu amma idan tace bata jin dadin zaman gidan tayi karya,har ila yau Anty hasinah naci gaba da bata shawarwari da kwarin gwiwar hanyoyin da yakamata tabi domin mallaka da siye zuciyar mijinta wanda amafi yawan lokuta tafi kwatanta shi da bahago,miskili kuma murdadde domin kamar bai san wadannan abubuwan da take yimasa ba shiyasa duk tabi ta kare ta sake bushewa saboda tsananin damuwa domin ita tana sonshi kullum ta Allah da sabuwar soyayyar shi take wayar gari amma kamar shi baya ganewa, sannan wani abun karin takaicin shine wasu zafafan massages da ake turo mata kullum safe da rana da dare wanda takasa gane ko waye sai dai tanata addu’ar Allah yasa muradin ranta ne.

Abinda Hanan bata saniba shine shikam Khalil tuni shirye shiryen bikinsa da anty maamy yayi nisa domin har sun kai maganar gaban iyaye bayan sun gama shirya yanda suke son abunsu ya kasance,duk da wani lokacin idan ya kadaice kansa ya zauna sai yayita tambayar kansa Wai meyasa zaiyi auren nan ne? Wani bangare na zuciyarsa na son yayi auren yayinda wani bangaren kuma ke adawa da hakan,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button