MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

Daurewa dai kawai yakeyi akan maganar auren nan tunda har anyanke lokaci bayan babbar salla da sati uku kamar yadda ita amarya maamy ta bukata,shima uban gayyar hakan yayi masa shiyasa ya sanar da Abban London wanda shine zai nema masa auren kuma gaba daya family kowa yayi farin ciki da murnar wannan al’amari dake shirin kulluwa nan wasu cikin dangi ke fadin ai dama tun suna yara budurwar shi ce ashe da rabon aure,ita Hanan koda wasa bata san abinda ke faruwa ba saboda dama can shi zuwa gombe bata yimasa wahala shiyasa yanzun ma idan yace yatafi gombe bata jin komai aranta,
Yau kam tun kafin ta kwanta bacci ta gama shirya kayanta saboda Khalil yace mata ta shirya gobe zasu tafi gombe saboda acan zasuyi salla shi dama agida yake salla karama da babba,
Washe gari tare da Aryan suka je school dinsu ta rakashi saboda ranar za abasu hutu,taji dadin zuwan da tayi sosai domin daliban makarantar sun shirya wasanni kala kala dan nishadantar da iyayen yara wadanda suka samu damar halattar bikin rufe makarantar,
K’arfe 2 saura suka dawo gida nan suka fara zaman jiran Khalil saboda sai yataso daga office zasu tafi ai kuwa kamar yadda Hanan ta tsammata sai dab da magriba yazo nan suka tattara suka tafi,umma barira da Aryan motarsu daya shikuma oga da Hanan suma mota daya suka shiga dukkansu sun kame agidan baya,zaman kurame yau dinma sukeyi kamar koda yaushe,ajiyar zuciya Hanan ta dan ajiye sannan ta saci kallon sa tace,
“Abban Aryan nidai da son samune inyi salla a kano…..”
Idonshi na kan jaridar daily trust dake hannunsa yabata amsa da,
“Saboda wanne dalili?”
“Nafa jima rabona da gida…..” Ta fada cikin shagwaba,
“Shine kadai dalilin?”
“Dan Allah…..”
Shiru taji yayi hakan ya tilastata itama yin shirun tana zunburo baki duk da tasan ba ganinta yake yiba. Bayan sallar ishah suka shiga cikin gombe kai tsaye cikin gida suka wuce tun daga lokacin basu kara ganin Khalil ba dan ko shiga gidanma baiyi ba lokacin, wannan karonma sun samu tarba ta girma da karamtawa daga daukacin jama’ar dake rayuwa agidan lokacin salla saura kwana biyu kacal,
Tun bayan zuwansu rabonta da Khalil dan ko da safe lokacin da takai masa breakfast baya nan har yafita sai ajiye masa tayi afalo tadawo,suna tare dasu Sarah da Rufaida hajiya ta dauko musu mai k’unshi tana ta yalyala musu text massage din Khalil yashigo wayarta gashi lokacin kunshin kafarta bai busheba bakin amma jan yayi dan harma ancire,
_Zo ina part dina._
Abinda taga yarubuto kenan,babu yanda zatayi haka dole ta tashi da kwayayyen zani tabi ta baya saboda mutane ta nufi sashen nasa,yana baje falo yana cin kilishi cikin wata babbar takarda da waya a kunnenshi,wuri ta samu ta zauna tana kallonsa kallo na kurulla aranta tana gulmarsa ita daya wai har yanzu bai fara furfura ba domin babu ko kwaya agashin kansa,
“Idan kin gama gulmar ga kayanku nan keda Aryan…..”
Jin abinda yafada yasata saurin dauke idonta daga kan sumarshi,
“Gulma kuma uncle?”
Bai bata amsa ba maimakon haka ma sai taji yace,
“Wannan menene aka mammanna miki?”
“Lalle ne fa….”
Jijjiga mata kai yayi, nannade kilishin da yake ci yayi yasaka mata cikin leda sannan ya mika mata,karba tayi ta tattara kayan da yakira da nasu ita da Aryan tafita.
Bata kara sakashi a idonta ba sai ranar salla yasha manyan kaya farare tas andawo daga masallaci dama ita bataje ba saboda ta tashi tana fashin salla,gidan gaba daya cike yake da baki daga wurare daban daban sai rabon kudi da danyen nama yake yi domin ya yanka shanu da raguna sun kai talatin duk wanda yazo maroka da mabukata sai ancika masa leda Viva da nama,sai bayan da yayi sallar la’asar sannan yafita. Wannan karonma kamar karamar salla sun yi ziyarce ziyarcen gidajen dangi da yan uwa,washe garin salla suka tafi katsina gidan yayarshi saudat wannan shine karon Hanan nafarko da taje gidan anty saudat kuma ta karbeta hannu bibbiyu basu wani jima sosai ba suka tafi nan kuma kano suka wuce direct gidansu Hanan ai tun acikin mota hanan ke murna kamar zatayi tsalle,
Ta samu gidansu cikin wadata da walwala domin suma saniya suka yanka da raguna guda biyu kuma duk Khalil ne yakawo banda kayan salla da ya aiko dasu wadanda za arabawa dangi,wuni guda yabarta tayi agida dan har gidan anty salaha suka je a tsattsaye daga nan suka juya gombe,yauma Hanan harda kukanta wanda bai san ko kukan me zai kirashi ba shin kukan shagwaba zai kirashi ko kukan sakarci?
“Ke Wai bakya girma da kuka?” Taji yace da ita lokacin da take share hawaye da gefen mayafinta,dole yafadi haka mana tunda shi yana zuwa gida yana ganin kowa nashi aduk lokacin da yaso ta ayyana hakan acikin ranta.
Washe garin salla da kwana uku suka koma Abuja inda akaje aka cigaba da zama irin na da,gashi kullum mai turo mata sakon nan bai daina ba yi yake ita kuma bata ko bi takai dan bata san waye ba,
Bikin maamy da Khalil kam kullum kara karatowa yake yi domin saura sati daya da yan wasu kwanaki angama komai sadakine kadai yarage Khalil bai bada ba amma har gidan da maamy zata zauna da komai da komai yagama shiryashi.
K’arfe 11 saura minti shida agogon bangon dake cikin falonsa yanuna,zaune yake akan sofa yana sanye da farar t shirt mai tambarin Nike ajiki da farin dogon wando mai santsi yana tura wasu bayanai ta laptop dinshi, Hanan yake ta jira ta kawo masa coffee din da yaturata ta hado masa amma shiru kamar wacce aka aiki bawa garinsu,
Bai kai ga gama tunaninsa ba ta turo kofa tashigo,sanye take cikin kayan bacci riga da wando marassa nauyi shiyasa ta dora dogon farin hijabi akai,gabansa takai ta ajiye kan center table sannan ta nemi wuri ta zauna,
“Gashi….”
Kai ya daga mata sannan cikin taushin murya yace,
“Thank you”
Shiru tayi kawai ta dan yi murmushi tana mai cigaba da satar kallonsa,zuwa can ta mike saboda bacci take ji,
“Saida safe….”
“Ok Allah yakaimu”
Ya furta yana binta da manyan idanuwansa masu haske, yarinyar tana dan bashi tausayi kadan saboda yanda take dawainiya da Aryan da kuma shi kansa wani lokacin domin kullum cikin fama take da girkin abincin da zai ci da gyaran sashensa kamar wata house girl,watsar da tunanin yayi yaci gaba da aikinsa yanayi yana kurbar coffee din da ta ajiye masa wanda bashi yagama ba sai misalin karfe 1 na dare,
Tattare komai yayi zai wuce bedroom dinshi nan yaji k’arar wayar Hanan wacce ta manta,idonsa ne yakai kai bayan tagama kara alamar shigowar sako,komawa yayi ya dauki wayar zuciyarshi na tambayar shi to waye yaturowa yarinyar nan sako adaidai wannan lokaci? Tambayar da yaketa yiwa kansa kenan saboda ko babu komai ai a karkashin ikonsa da kulawarsa take dan haka wajibine yasan dukkan motsinta da kuma mu’amularta da kowa, ajiye wayar yayi tare da sauran wayoyinsa akan gado yawuce bathroom yaje ya dauro alwala yafito,fitowarsa tayi daidai da shigowar wani sakon cikin wayar Hanan,zama yayi gefen gadon ya dauki wayar tata luckily babu wani lock ajiki nan yabude sakonnin yasoma karantawa idanuwanshi aware bakinsa abude alamar mamaki…………………………鉁嶐煆?
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._