MIJIN MATACCIYA 1-END

MIJIN MATACCIYA Page 51 to 60

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:14 AM – Ummi Tandama: 46

***Idanuwansa aware bakinsa abude alamun mamaki yasoma bude sakonnin yana karantawa daya bayan daya wadanda ke dauke da kalamai na soyayya,

Kasancewar abun yayi mutukar bashi mamaki shiyasa bai tsaya wuri daya ba dan koda yagama karanta wanda aka turo yanzu cigaba yayi da bude sauran sakonnin dake cikin inbox din nata yana dubawa,shi kansa bai san dalili ba amma dai bai ji dadin wannan al’amari ba sam baiji dadin ganin sakonnin da yagani ba saboda har da na mujahid duk yagani,to Hanan wacce irin yarinya ce? Koda yake dama yajima da fahimtar cewa akwai wanda take so wanda ta mallakawa zuciyarta shikuma yazo yayi musu karfa karfa ya aureta,

Gaba daya ji yayi kansa ya kulle yarasa ma wanne irin mataki yadace ya dauka akanta,ya za ayi tana gidansa karkashin ikonsa a matsayin matarsa amma wani gardin banza acan waje yana turo mata sakonni makamantan wadannan?

Raba dare yayi yana binciken dashi kansa baiga alfanunsa ba acikin wayar tata ko ina saida yaduba hatta nata sakonnin da ta tuttura saida yabude yagani bayan ya gama ya kashe wayar ya ajiye cikin bedside drawer sannan ya kwanta zuciyarshi cunkushe da fushin da bai san hujjarsa ba.

Hanan bata da masaniyar abinda ke faruwa shiyasa bayan tayi sallar asubah ta wuce kitchen kamar yadda ta saba ta dorawa oga breakfast,tana ta tunanin to a ina ta ajiye wayarta saboda ta duba bata ganta ba babu inda bata duba ba daga karshe ta tuno cewa ai a sashen Khalil ta barta jiya da daddare,cike da kwarin gwiwa ta kammala komai kamar yadda ta saba taje ta shirya Aryan yatafi makaranta sannan itama ta shirya ta nufi bangaren Khalil. Ta jima zaune kadan a falon nashi tana dakon jiran fitowarshi,misalin karfe 8 taji alamun fitowarshi,duk da dama can shi ba ma’abocin dariya satataa bane amma yau kam kallo daya tayiwa fuskarshi ta gane akwai matsala saboda irin yanda yatsare gida ya hade bangon gabas da yamma ya daure fuskarshi tamau,

Cikin sanyin jiki da tsoro bayyananne ta gaidashi,

“Uncle ina kwana?”

Sai da ya dan ja lokaci kafin ya amsa mata da, “lafiya”

Daga haka yawuce yayi waje yana kara waya a kunnenshi ko kallon inda ta ajiye masa abincinsa baiyi ba saboda amugun kule yake da ita,ita mahaukaciyar inace da bata san darajar aure ba har zata rinka musayar kalamai da wani katon banza awaje? Shiyasa ya zama dole agareshi ya dauki matakin da yadace,

Hanan abun duniya ne taji yataru yayi mata yawa domin sam bata da masaniyar abinda ke wakana,ita dai kawai abunda ta sani shine yanzu Khalil ya canja completely yana yin wasu abubuwa fushi fushi,zafi zafi dan ko abincinta yadaina ci tsawon kwana uku kenan sannan ko gaisheshi tayi asama yake amsawa kamar zai mareta to wai me yake faruwa? Ita ba abinda yafi tayar mata da hankalima kamar yajin cin abincinta da yayi domin haka zata zage ta bata lokacinta ta shiga kitchen ta shirya masa abincin da ta san zaiyi farin ciki dashi amma yanda ta ajiye masa haka zata samu abinta ta dauko bai ko taba ba, gashi wayarta tana son tambayarsa amma tana tsoro domin wani irin kwarjini gareshi na innanaha. Khalil kuwa ya zabi ya hanata wayar ne har zuwa lokacin da zai gama fahimtar komai saboda bazai yuyu ya zuba ido tayita aikata son ranta ba,

Maganar aurenshi da maamy kuwa ankammala komai sai daurin aure kawai da yarage sadakinta ma yayi order dinsa dubai tun kwanaki biyu da suka wuce aka kawo masa dan haka yau bayan yatashi daga office yawuce gombe domin kaiwa maamy zoben,

Bayan sallar magrib yashiga gidansu maamy din yana shiga ya isketa zaune tare da abbansu jawad wato tsohon mijinta, kamar zasu mari juna suka gaisa abban su jawad yatashi yafita,da alamar tuhuma akan fuskarshi yake kallon maamy kafin ya furta,

“Wannan fa?”

“Ibrahim kenan…. Abbansu jawad ne fa….,Yazo ganin yaranshi”

“Ehh nasani,but da nashigo ban ganshi tare da yaranshi ba da ke naganshi”

“Su dinma da suna tare damu basu jima da fita ba saboda zamu tattauna akan makomarsu wato inda yadace su zauna a hannunsa ko a hannuna…..”

“To yanzun a ina kuka yanke hukunci zasu zauna?”

“Nidai idan son samuna ne shine su zauna anan wurin iyayena shikuma yaki yarda wai ala dole lallai lallai sai nabashi yaranshi ya kaiwa mom dinshi wacce nasan gallaza musu kawai zatayi”

“To ke meyasa ba zaki rikesu ba?”

Dan Damm tayi sannan ta saki murmushi,

“Ibrahim kenan,taya zan rikesu alhali ubansu na raye? Da dai ace baya raye ne shine zan iya daukarsu intafi dasu gidan aure na”

“Kar ki damu indai dan tani ne,maamy nima fa mai rike yaranki ne koda kuwa babu aure tsakaninmu……. Babu matsala kina iya rikesu”

“Allah sarki Khalil….. Can’t wait lokacin da zamu zama ma’aurata”

Murmushi yayi ya kalleta,

“Wanne albishir za ayi min?”

“Farin ciki kawai….”

Murmushi yayi baice komai ba,har suka gama hirar yatafi bai nuna mata zoben ba ko yamanta ne ko kuma meyasa oho shi dai yasan dalili.

Karfe 11 yashiga gidansa a abuja, Hanan na zaune taji shigowar shi yau kam ta daura damarar sai taji daga gareshi, mintuna 30 tabashi yagama kintsawa sannan sai taje gareshi taji abinda ke faruwa da har yadauki fushi da ita,

Tana ganin mintuna 30 sun cika ta tashi ta fita tana sanye cikin kayan bacci ta dora hijab akai,falon nashi ta shiga wanda ya wadatu da kamshinsa mai sanyaya zuciya da tsayawa arai,bata fi mintuna biyu da zama ba taji fitowarsa yana magana awaya cikin sanyin murya,

“Khalid maganar aure na da maamy ne…… Dazu naje na sameta tare da baban yaran nan nata,ni banda problem akan yara zan rike mata amma inda problem din yake shine…..”

Ai bata jira taji karshen bayanin nasa ba ta tashi jiri na d’aukarta kamar zata fadi tafita daga sashen nasa gaba daya. Wani irin kuka ne yaci karfinta kuma tun kafin ta shiga bedroom dinta ya subuce mata,haba ashe da walakin,ashe dama can akwai wata akasa shiyasa anty maamy tazo gidanta ta tare tun kafin adaura musu aure da Khalil,ashe sun jima suna cin amanarta bata saniba,

Kukan rashin sanin mafita tayita faman yi gashi babu waya a hannunta bare ta bukaci shawarwarin yan uwa da abokan arziki,kusan kwana tayi tana kuka sai da asubah ta iya samun bacci. Haka ta wayi gari kamar wata marar lafiya gashi sam babu farin ciki atare da ita danma dai kafin ta tashi umma tuni ta shirya Aryan yatafi makaranta,kasa cin abinci tayi sai ruwan tea kadai da ta iya kurba,tsawon kwanaki biyu tana fama da rashin cin abinci da kuma rashin bacci wanda yayi sanadiyyar haddasa mata ciwon kirji da zazzabi,

Da farko zazzabin baiyi zafiba amma magriba nayi sai ya tsananta jikinta kamar ana kada mata mazari saboda tsananin rawar sanyin da take yi,waya umma tayiwa Khalil ta sanar masa akan ya turo musu Dr,babu jimawa sai ga Dr Al’amin din yazo nan ya dubata yayi duk abunda yadace yatafi,

Wani bacci ne mai dadi ya kwasheta bayan tafiyar Dr nan umma taja hannun Aryan suka fita suka barta dan ta samu bacci,shi kuwa Khalil lokacin da umma ta kirashi awaya tana fada masa rashin lafiyar Hanan yana can gombe tare da maamy wacce gyaran jikin da aka fara yimata na dilke da halawa yasa ta sake fitowa dauu kamar wata balarabiya ga wani azababben kamshi da ke tashi daga jikinta kamar masana’antar sarrafa turare,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button